Malamar Islamiyya: Sufeton 'Yan Sanda Ya Dauki Mataki kan DPO a Kaduna

Malamar Islamiyya: Sufeton 'Yan Sanda Ya Dauki Mataki kan DPO a Kaduna

  • Sufeto janar na 'yan sandan Najeriya, Disu Tunji ya bukaci a gudanar da bincike na musamman a kan malamar Islamiyya da aka kashe a Kaduna
  • Matakin binciken ya biyo bayan korafi da aka mika game da zargin cewa dan sanda ne ya mika matar ga mutane suka kashe ta a Maraban Jos
  • Mutanen gari ne suka taru suka kashe Malama Ummulkhairi kuma suka kona ta bisa zargin cewa satar yara ta ke yi a Maraban Jos a Kaduna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Ana cigaba da daukar mataki game da malamar Islamiyyar da wasu mutane suka kashe a karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

Bayan korafin da aka shigar, rundunar 'yan sandan Najeriya ta bukaci a binciki jami'in ta da ake zargi ya yi sakaci game da lamarin.

Kara karanta wannan

Yadda aka nemi ceto malamar Islamiyya amma mutane suka taru suka kashe ta

Sufeton 'yan sanda malamar Islamiyya
IGP Tunji Disu a hagu da malamar Islamiyya a dama. Hoto: Nigeria Police Force|Hassan Muhammad
Source: Facebook

Barista Hamza Nuhu Dantani ya wallafa a Facebook cewa ya gana da sufeton 'yan sanda game da zargin da aka yi wa DPO da ke lura da wajen da abin ya faru.

Malamar Islamiyya: Za a binciki DPO na Marabar Jos

Lauya mai kare hakkin dan Adam, Barista Hamza Nuhu Dantani ya bayyana cewa sufeton 'yan sanda ya bayar da umarni a binciki dan sandan da ake zargin ya yi sakaci.

Sakon da lauyan ta wallafa ya nuna cewa:

"Sufeton 'yan sanda, IGP Disu Tunji, ya bada umurni cikin gaggawa da a binciki hakikanin abin da ya saka DPO ya mika matar ga jama'a har ya kai ga mutuwarta.

Baya ga DPO da ake zargi, umarnin ya shafi dukkan wadanda aka ce suna da hannu a lamarin, inda lauyan ya ce binciken zai hada da

"Duk waɗanda ake zarginsu wajen kisan wannann matar."
Malamar Islamiyya da mijinta
Malama Ummulkhairi a hagu da mijinta a gefen dama. Hoto: Hassan Muhammad
Source: Facebook

Wanda zai binciki DPO a Kaduna

Kara karanta wannan

Bello Turji ya ba Najeriya zabin yaki ko zaman lafiya a sabon bidiyo

Barista Dantani ya bayyana cewa Tunji Disu ya ce mataimakin sufeton yan sanda da mai kula da sashen CID ne za su jagoranci binciken.

Lauyan ya ce:

"Dazu na gana da IGP kuma ya umurci mataimakin sufeton 'yan sanda (DIG) da babban sashen bincike dake Abuja da su tabbatar da an yi binciken gaskiya,"

Ya kara da cewa shugaban 'yan sandan ya bukaci a mika masa rahoton da zarar an kammala bincike, inda ya ce ya bukaci:

"A aika masa da rohoto idan sun kammala."
Takardar bincike kan DPO
Takardar da IGP Tunji Disu ya fitar kan binciken DPO a Kaduna. Hoto: Hamza Nuhu Dantani
Source: Facebook

Ran sufeton 'yan sanda ya ɓaci

Bugu da kari, lauyan ya bayyana cewa ran sufeton 'yan sanda ya ɓaci sosai da ya ji labarin abin da ya faru da malamar Islamiyyar.

Ya ce:

"A Gaskiya ran IGP ya yi matukar ɓaci irin yadda ya kalli bidiyon matar nan yake ci da wuta, da kuma zargin cewa an mika wannan matar har aka kashe ta ta hanyar banka mata wuta a bainar jama'a a kan zargin laifin da ba ta aikata ba."

Maganar mijin matar da aka kashe

Kara karanta wannan

Mutane sun kama malamar Islamiyya da karfi sun kona ta, 'yan sanda sun magantu

A wani labarin, mun kawo muku cewa mijin malamar Islamiyyar da aka kashe a Maraban Jos a Kaduna ya ce yana cikin matukar damuwa.

Rahoto ya nuna cewa mijin malamar ya ce tana kokarin tafiya zuwa wajen wa'azi ne aka yi mata sharrin cewa tana satar yara aka kashe ta.

Ya kuma bayyana cewa a yanzu haka wasu daga cikin kananan 'ya'yan malama Ummulkhairi na tambayar yaushe mamar su za ta dawo.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng