INEC Ta Lissafo Abubuwan da Ke Barazana ga Zaben 2027

INEC Ta Lissafo Abubuwan da Ke Barazana ga Zaben 2027

  • Hukumar INEC ta gano manyan abubuwan da za suniya yin barazana ga sahihin zabe a shekarar 2027
  • Shugaban hukumar, Joash Amupitan, ya ce kalaman kiyayya, yaɗa bayanan ƙarya da tsoma bakin ƙasashen waje na iya rage amincewar masu kaɗa kuri’a
  • INEC ta ce tana shirin tura ma’aikatan wucin gadi kusan miliyan 1.4 zuwa sama da rumfunan zaɓe 176,000 a faɗin ƙasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta gano abubuwan da za su iya kawo cikas ga babban zaben 2027.

INEC ta gano barazanar tsaro, tashe-tashen hankulan zaɓe a wasu yankuna, sayen kuri’u, kalaman kiyayya, yaɗa bayanan ƙarya da kuma Tsoma Bakin Ƙasashen Waje da Sarrafa Bayanai (FIMI) a matsayin manyan barazana ga sahihancin babban zaben 2027.

INEC ta yi magana kan zaben 2027
Shugaban hukumar zabe ta INEC, Farfesa Joash Amupitan Hoto: @inecnigeria
Source: Facebook

Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan (SAN), ne ya bayyana hakan ranar Talata a Abuja lokacin da ya karɓi tawagar International Republican Institute (IRI) mai gudanar da Binciken Shirye-shiryen Zaɓe (PEAM), cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Yadda aka dukufa da addu'a har aka kifar da APC a zaben gwamnan Osun

Abubuwan da ke barazana ga zaben 2027

Amupitan ya ce barazanar da aka gano na iya rage amincewar masu kaɗa kuri’a tare da haifar da manyan ƙalubale ga tsarin zaɓe idan ba a magance su yadda ya kamata ba.

"Barazanar tsaro, tashe-tashen hankulan zaɓe a wasu yankuna, sayen kuri’u, da saurin yaɗuwar kalaman kiyayya, bayanan ƙarya da tsoma bakin kasashen waje da sarrafa bayanai (FIMI), na barazana kai tsaye ga amincewar masu kaɗa kuri’a.”

Ziyarar ta zo ne kwanaki uku bayan zaɓen gwamnan jihar Osun da aka gudanar ba tare da haɗa shi da sauran zaɓubbuka ba, sannan kwana ɗaya kafin fara kamfen da gangamin siyasa bisa doka gabanin babban zaben 2027, wanda zai fara ranar Laraba, 19 ga Agusta.

INEC ta fara shirye-shiryen zaben 2027

Shugaban INEC ya ce binciken na PEAM ya samar da wani ra’ayi mai zaman kansa a daidai lokacin da hukumar ke shiga cikakken shiri domin gudanar da zaben 2027.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya fadi abin da ya sa gwamnoni da dama za su sha kunya a zaben 2027

Ya bayyana cewa hukumar tana ƙara ƙarfin gudanar da ayyukanta domin tura ma’aikatan wucin gadi kusan miliyan 1.4 zuwa rumfunan zaɓe sama da 176,000 a faɗin ƙasar yayin zaben 2027..

A cewarsa, zaɓubbukan gwamnonin da aka gudanar ba tare da haɗa su da sauran zaɓuka ba da kuma zaɓukan cike guraben majalisu na baya-bayan nan sun zama gwaje-gwajen yadda hukumar ke gudanar da jigilar kayayyaki a filin aiki, haɗin gwiwa da hukumomin tsaro da kuma tsarin fasahar zamani.

Ya ce amfani da fasaha ya rage ƙalubalen da ke da alaƙa da yadda ake gudanar da zaɓubbuka a Najeriya a baya, Tribune ta kawo labarin.

INEC ta tabo batun zaben 2027
Farfesa Joash Amupitan na jawabi a wajen taro Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Hanyar da za a iya magudi a zaben 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ministan sufurin jiragen sama, Osita Chidoka, ya bayyana hanyar da za a iya yin magudi a zaben 2027.

Chidoka, wanda shi ne shugaba na cibiyar Athena Centre mai zaman kanta da ba ta da alaka da wata jam’iyyar siyasa, ya ce hanya daya tilo da za a iya yin magudi a zaben 2027 ita ce rashin gudanar da zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng