Mutanen da Yan Bindiga Suka Sace a Wurin Ibada Sun Dawo Gida, Mutum 1 Ya Mutu a Ekiti

Mutanen da Yan Bindiga Suka Sace a Wurin Ibada Sun Dawo Gida, Mutum 1 Ya Mutu a Ekiti

  • Mutanen da aka yi garkuwa da su suna cikin ibada a cocin jihar Ekiti sun shaki iskar 'yanci bayan shafe tsawon lokaci a hannun 'yan bindiga
  • Rundunar 'yan sanda ta bayyana cewa jami'an tsaron hadin gwiwa ne suka yi nasarar ceto mutanen, amma ɗaya daga ciki ya rasu
  • Kwamishinan 'Yan Sandan Ekiti, CP Falade Adegoroye Michael, ya yaba da jajircewa, kwarewa da hadin kan hukumomin tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ekiti, Nigeria - Rundunar 'Yan Sandan Ekiti ta tabbatar da rasuwar daya daga cikin masu ibadar da aka sace yayin harin da aka kai Cocin Christ Apostolic a watan Afrilu, 2026.

Haka kuma rundunar ta sanar da cewa an ceto sauran masu ibadar wadanda aka yi garkuwa da su a cocin da ke Eda-Oniyo, karamar hukumar Ilejemeje ta jihar Ekiti, a ranar 28 ga Afrilu, 2026.

Kara karanta wannan

An rike dan ta'adda da ya nufi fadar sarki da bindiga zai kai hari

Yan sanda.
Wasu jami'an rundunar yan sandan Najeriya a bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Daily Trust ta ruwaito cewa jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan Ekiti, SP Sunday Abutu, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar yau Asabar, 4 ga watan Yulin 2026.

Yadda aka ce masu ibadar coci

Ya bayyana cewa an ceto mutanen ne sakamakon ci gaba da gudanar da ayyukan tattara bayanan sirri da kuma hadin gwiwar hukumomin tsaro daban-daban.

Ya ce aikin ya samu gudummawar, rundunar 'Yan Sandan Najeriya, Sojojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro, rundunar Amotekun, maharba na gargajiya, gwamnatin Jihar Ekiti

Abutu ya ce an garzaya da wadanda aka ceto zuwa asibiti domin a duba lafiyarsu tare da ba su kulawar da ta dace.

Ya kara da cewa Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Ekiti, CP Falade Adegoroye Michael, ya yaba da jajircewa, kwarewa da hadin kan dukkan hukumomin tsaron da suka taka rawa wajen ceto wadanda aka sace.

Ya yabawa gwamnatin Ekiti

Kara karanta wannan

Sufeton ƴan sanda ya ja kunne kan zargin an boye masu laifi a gidan gwamnatin Osun

Kwamishinan ya kuma yabawa gwamnatin Jihar Ekiti karkashin jagorancin Gwamna Biodun Abayomi Oyebanji saboda irin goyon bayan da take bai wa hukumomin tsaro.

A cewarsa, wannan goyon baya ya kasance muhimmin abin da ya taimaka wajen samun nasarar aikin ceton.

Yan sanda sun ja hankalin al'umma

Abutu ya kuma gode wa al'ummar jihar Ekiti saboda ci gaba da ba jami'an tsaro hadin kai, kasancewa cikin shiri da kuma kai rahotannin sahihan bayanai a kan lokaci.

Ya ce ana ci gaba da kokarin cafke wadanda suka aikata wannan ta'asa, domin gurfanar da su a gaban doka.

Oyebanji.
Gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji yana jawabi a taron majalisar zartarwa Hoto: Biodun Oyebanji
Source: Twitter

Ya tabbatar wa mazauna jihar cewa rundunar 'yan sanda za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama'a, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Sannan ya bukaci jama'a su kasance masu lura tare da ci gaba da kai rahoton duk wani mutum ko abu da suke zargin yana da alaka da laifi zuwa ofishin 'yan sanda mafi kusa.

Mutane 11 sun kubuta daga yan bindiga

Kun ji cewa mutum 11 da aka yi garkuwa da su a gonakinsu a jihar Edo sun tsere bayan masu garkuwar da su sun yi barci.

Kara karanta wannan

2027: Malami ya gana da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC a Abuja

Rahotanni sun nuna cewa sun gudu ne bayan masu garkuwar sun yi barci saboda gajiyar tafiyar da suka yi da su cikin daji tsawon dare.

Bugu da kari, rundunar 'yan sandan jihar Edo ta ce ta kama mutane 32 da ake zargi masu garkuwa da mutane ne a Yunin 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262