Gwamnati Ta Gano Matsala, Ta Rufe Asibitocin Kudi Sama da 30 a Jihar Kano
- Gwamnatin jihar Kano ta rufe asibitoci da cibiyoyin lafiya na kudi 37 cikin watanni 18 saboda karya ƙa’idojin gwamnati
- Rahotanni sun nuna cewa gwamnati ta rufe cibiyoyi 16 a 2025 da wasu 21 tsakanin watan Janairu zuwa watan Yuli 2026
- Fiye da cibiyoyin lafiya masu zaman kansu 1,405 ne ke da rajista a jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Hukumar Kula da Cibiyoyin Lafiya Masu Zaman Kansu ta Jihar Kano (PHIMA) ta rufe asibitoci da sauran cibiyoyin lafiya na kudi guda 37 a jihar.
Hukumar ta rufe wadannan asibitocin na kudi ne cikin watanni 18 da suka gabata saboda laifuka daban-daban na karya ƙa’idojin aiki.

Source: Facebook
Tribune Nigeria ta rahoto cewa mukaddashin shugaban PHIMA, Hajiya Khadija Sa’id, ta bayyana cewa an rufe asibitoci 16 a 2025, yayin da aka rufe wasu 21 tsakanin watan Janairu da Yuli 2026.

Kara karanta wannan
Yadda dalibin tsangaya ya tsallake rijiya da baya lokacin da abokansa 4 suka rasu a Kano
A cewarta, a halin yanzu akwai cibiyoyin lafiya masu zaman kansu sama da 1,405 da aka yi wa rajista a hukumar a faɗin jihar Kano.
Ayyukan da suka rataya a wuyan PHIMA
Hajiya Khadija ta ce PHIMA ce ke da alhakin sauƙaƙa, daidaitawa da sa ido kan ayyukan kiwon lafiya da asibitocin kudi da sauran cibiyoyin lafiya masu zaman kansu ke bayarwa.
Ta ƙara da cewa hukumar na da ikon hukunta ko rufe cibiyar da ta karya ƙa’idojin da gwamnati ta gindaya.
Ta ce PHIMA na sanya ido kan cibiyoyin lafiya masu zaman kansu ta hanyar gudanar da sa ido na yau da kullum da kuma sa ido na tallafi.
PHIMA na sa ido kan asibitocin kudi
A cewarta, tawagar da ke gudanar da sa ido na yau da kullum na ƙunshe da ma’aikatan PHIMA da ma’aikatan wucin gadi masu ƙwarewar aikin likita.
Ta ce sauran masu taimakawa hukumar wajen sa ido sun haɗa da masu ruwa da tsaki da suka haɗa da ƙwararrun likitoci, lauyoyi, wakilan Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano, jami’an tsaro da shugabannin al’umma.

Kara karanta wannan
FAAC ta cika aljihun gwamnatin Tinubu da jihohi, an raba abin da ba a taba samu ba
Hajiya Khadija ta ce cibiyoyin da aka yi wa rajista sun haɗa da ƙananan asibitoci, kyamis, asibitoci, ƙwararrun asibitoci, gidajen jinya, cibiyoyin asibiti da haihuwa da kuma asibitocin haihuwa.

Source: Original
Gwamnatin Kano ta gargadi asibitocin kudi
Ta jaddada cewa kowane rukuni na cibiyar lafiya yana da takamaiman ayyukan da aka ba shi izinin gudanarwa.
Ta yi gargaɗin cewa karya doka ne, asibitin da aka ba izinin yin ayyukan karamar cibiyar lafiya ya gudanar da ayyukan da aka ware wa babban asibiti.
“Abin da ya fi damunmu shi ne tabbatar da samar da kyakkyawan aikin kiwon lafiya ga Qa son wani yanayi da lafiyar jama’a za ta kasance cikin haɗari,” in ji ta.
Gwamna Abba ya sauya sunan asibiti
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sauya sunan Babban Asibitin Dawakin Tofa zuwa Dr Mahmoud Baffa Yola General Hospital.
Gwamna Abba ya yi haka ne domin karrama marigayi Mahmoud Baffa Yola, dattijon kasa da ya yi fice wajen hidimtawa al’umma da ci gaban jihar Kano.
Asali: Legit.ng