Tinubu Ya Dauki Sabon Mataki kan Tsaro, Ya Ba da Wa'adin Kwanaki 90

Tinubu Ya Dauki Sabon Mataki kan Tsaro, Ya Ba da Wa'adin Kwanaki 90

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin game da matsalar rashin tsaro da ta saka Najeriya a gaba domin nemo bakin zaren
  • Tinubu ya dora wannan sabon aiki a kan kwamitin mutum 11 karkashin mai ba Shugaban Kasa shawara kan tsaron cikin gida, Manjo Janar Adeyinka A. Famadewa
  • Shugaban ya bai wa kwamitin wa’adin kwanaki 90 domin kammala shirye-shiryen tare da gabatar masa da aikin da ya ba su domin a sake fasalin tsaron

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da fara shirya cikakken binciken tsaron kasa da kuma shirin dabarun ayyukan tsaro na shekaru biyar.

Gwamnatin tarayya ta ce an dauki sabon matakin ne domin karfafa hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, leken asiri da sojojin Najeriya.

Kara karanta wannan

'Ina N4tr suka shiga"? Atiku ya kalubalanci Tinubu kan farfado da matatun mai

Shugaban kasa ya ba da umarni kan tsaro
Shugaban Najeriya Bola Amed Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Tinubu ya bayar da umarnin ne a ranar Laraba 19 ga wata Agusta, 2026 yayin taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya da aka gudanar a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja kamar yadda Bayo Onanuga ya wallafa a X.

Tinubu ya ba da umarni kan tsaro

Mai ba Shugaban Kasa shawara kan tsaron cikin gida, Manjo Janar Adeyinka A. Famadewa, ne zai jagoranci ayyukan sakatariyar kwamitin mutum 11 da aka kafa domin tsara shirin.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da mai bai wa Shugaban Kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu; Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa da Karamin Ministan Tsaro, Alhaji Bello Muhammad Matawalle.

Shugaba Tinubu ya ce ana son inganta tsaro
Sugaban kasa Tinubu yayin wani taro a kasar waje Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Olufemi Oluyede; Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu; Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke; da Babban Hafsan Sojin Ruwa, Vice Admiral Idi Abbas.

Haka kuma, Darakta-Janar na Hukumar DSS, Tosin Ajayi, da Darakta-Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa, Ambasada Muhammed Muhammed, na cikin kwamitin.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: 'Babu mai iya girgiza tikitin mu da Peter Obi a 2027'

Abin da Tinubu ke so a yi

Shugaban Kasa ya ce bukatar samar da tsarin ta samo asali ne daga sauye-sauyen barazanar tsaro da ke fuskantar Najeriya, inda ya jaddada muhimmancin samun tsari guda da zai bai wa hukumomin tsaro damar aiki tare yadda ya kamata.

Ya ce sabon tsarin zai samar da fahimta guda kan barazanar da kasar ke fuskanta, manufofin ayyukan da ake son cimmawa da kuma irin karfin da ake bukata domin tunkarar wadannan barazana.

Tinubu ya yi nuni da cewa nasarorin baya-bayan nan da jami'an tsaro suka samu, ciki har da kubutar da dalibai da malamansu da aka sace a Karamar Hukumar Oriire ta Jihar Oyo, sun nuna muhimmancin inganta hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da na leken asiri.

Kwamitin zai kuma iya gayyatar wakilan wasu ma'aikatu, hukumomi da sassan gwamnati domin su bayar da gudunmawarsu idan bukatar hakan ta taso.

Ya umarci kwamitin da ya fara aiki nan take tare da kammala Binciken Barazanar Tsaron Kasa da Shirin Dabarun Ayyukan Tsaro cikin kwanaki 90, sannan ya gabatar masa da su domin nazari da amincewa.

Kara karanta wannan

Magana ta fito: An ji yadda ta kaya tsakanin wakilan Najeriya da na Amurka a Washington DC

Tinubu ya ba EFCC umarni

A wani labarin, mun wallafa cewa Shugaba Bola Tinubu ya umarci EFCC ta tura kudaden da aka kwace, ribar hannun jari da ba a karba ba zuwa shirin bayar da lamunin ilimi na NELFUND.

Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya ce matakin zai taimaka wajen tabbatar da wadatar NELFUND domin biyan bukatun dalibai da ke karuwa a fadin Najeriya da tabbatar da cewa an samu ilimi ya wadata.

Gwamnati ta ce kudaden da ke fuskantar shari’a ba za a tura su ba, yayin da za a mayar da wadanda ba su da takaddama ga NELFUND domin daliban Nariya su amfana kai tsaye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng