Ustazai a Najeriya Sun Hada Kudi ga Iyalan Malamar Islamiyyar da aka Kashe

Ustazai a Najeriya Sun Hada Kudi ga Iyalan Malamar Islamiyyar da aka Kashe

  • Ustazai da ke koyarwa a Islamiyya sun yi yunkuri na musamman a kafafen sada zumunta domin tallafawa iyalan malamar da aka yi wa kisan gilla a Kaduna
  • A ranar Alhamis, 25 ga watan Yunin 2026 ustazan suka tura tawaga ta musamman da kudi domin tallafawa 'ya'yan da Malama Ummulkhairi ta bari a duniya
  • Daya daga cikin masu fafutuka game da malaman Islamiyya a kafafen sada zumunta, Abdulkarim Hamisu Assuyudy ne ya jagoranci tattara tallafin da aka hada

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Malaman da ke koyarwa a makarantun Islamiyya a sassan Najeriya sun hada kudi domin tallafawa iyalan malamar Islamiyya da aka kashe bisa zargin satar yara a Kaduna.

A ƙarshen makon da ya wuce mutanen gari suka yi kururuwar cewa malamar tana satan yara a lokacin da ta ke kan hanyar zuwa wajen wa'azi a Maraban Jos da ke jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta jero mutane da kamfanoni 9 masu tallafawa 'yan ta'adda

Ustazai da iyalan malamar Islamiyya
Lokacin da aka kai wa iyalan malamar Islamiyya tallafi. Hoto: Abdulkarim Hamisu Assuyudi
Source: Facebook

Biyo bayan lamarin, Abdulkarim Hamisu Assuyudy da ake yi wa lakabi da Garkuwar Malaman Islamiyya ya fara kira a hada wa iyalan ta tallafi a Facebook.

An ba iyalan Ummulkhairi tallafin kudi

Da yammacin ranar Alhamis, malaman Islamiyya suka nada wakilai a Kaduna domin mika tallafin da suka hada wa iyalan marigayiya Ummulkhairi.

Rahotanni sun nuna cewa malaman Islamiyya sun hada kudi sama da N200,000 domin ba iyalan marigayiyar su rage wasu dawainiyoyyin rayuwa.

Ga sanarwar da suka fitar game da tallafin:

"Ustazai lallai kun faranta ran marayun da Malama Ummulkhairi ta bari!
"Yau mun sallama gaba ɗayan abin da aka samu N270,900 cif-cif, zuwa ga mijin marigayiya da 'ya'yanta."

Sanarwar ta kara da cewa:

"Mun faɗa masa cewa domin ya ƙara kula mana da 'ya'yanmu da malamar Islamiyyah ta bari, kuma sun yi farinciki da murna da godiya sosai.

Wakilan da malaman suka tura

Kasancewar malaman Islamiyyar sun hada tallafin ne a kafafen sada zumunta saboda suna jihohi daban-daban, sun wakilta wasu malamai a Kaduna wajen mika kudin.

Kara karanta wannan

NASFAT ta ja hankalin musulmai, ta nemi su taimaka kan matsalar tsaron Najeriya

Abdulkarim Assuyudy ya sanar da cewa:

"Mun wakilta Sheikh Jamilu Tahir Maraban Jos Kaduna da Shaikh Ukasha Umar da Shaikh Abdullahi Habib domin kai masu tallafin,"

Ya kuma yi addu'a da cewa:

"Ubangiji Allah ya sakawa duk wanda ya taimaka da alkhairi ya karɓi shahadarta ya kyautata ta mu in ta zo."
Malamar Islamiyya da aka kashe a Kaduna
Wasu ustazai da mijin malamar da aka yi wa kisan gilla. Hoto: Abdulkarim Hamisu Assuyudi
Source: Facebook

Martanin Iyalan malamar Islmamiyyar

Hotuna da bidiyo da suka bayyana a lokacin ziyarar sun nuna mijin malamar tare da 'ya'yan ta hudu a lokacin da aka mika masu tallafin kudin.

Mutumin da ya yi magana a madadin iyalan malamar ya bayyana cewa sun yi matukar farin ciki game da tunawa da su da malaman Islamiyyar suka yi.

Cikin bayanin mika godiya da ya yi, ya yi addu'ar Allah ya saka masu da alheri tare da karbar wannan muhimmin aiki da suka yi.

Za a binciki DPO a jihar Kaduna

A wani labarin, mun kawo muku cewa rundunar 'yan sandan Najeriya ta bayar da umarni a binciki DPO da ake zargi ya mika malamar Islamiyya ga jama'a sun kashe ta.

Kara karanta wannan

Malamar Islamiyya: Sufeton 'yan sanda ya dauki mataki kan DPO a Kaduna

Hakan ya biyo bayan korafi da wani lauya, Hamza Nuhu Dantani ya shigar a gaban sufeton 'yan sanda na kasa, IGP Tunji Disu a birnin tarayya Abuja.

Wata mata daga cikin iyalan malamar da aka yi wa kisan gilla ta ce DPO din ne ya mika ta ga jama'a suka kashe ta yayin da ta nemi mafaka a caji ofis a lokacin da aka jefa mata zargin satar yara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng