Uba Sani: 'Yan Sanda Sun Kama akalla Mutum 100 kan Kisan Ummulkhairi a Kaduna'

Uba Sani: 'Yan Sanda Sun Kama akalla Mutum 100 kan Kisan Ummulkhairi a Kaduna'

  • Gwamna Uba Sani ya nanata matsayar da gwamantin jihar Kaduna ta dauka game da kisan wata baiw ar Allah da mazauna Maraban Jos suka yi
  • Makonni da kisan malamar addinin Musulunci, Ummulkhairi Aliyu, a Kaduna, jami'an tsaro sun yi nasarar kama akalla mutane 100 da ake zargi da hannu a lamarin
  • Daga cikin wannan adadai an gurfanar da sama da mutum 40 a gaban kotu domin bibiyar hakkin malamar da aka yi wa kisan gilla ba tare da laifin komai ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya tabbatar da cewa babu wanda zai tsallake hukunci har sai an tabbatar da adalci ga marigayiya Ummulkhairi Aliyu.

Wasu fusatattun mutane da suka take doka sun hallaka malamar addinin Musulunci bayan sun yi mata dukan tsiya a yankin Maraban Jos.

Kara karanta wannan

'Yan kwallo sun rasu bayan hadari a Kebbi, gwamna ya ba su miliyoyin Naira

Gwamnan Kaduna ya sake magana kan UmmulKhairi
Gwamna Uba Sani tare da iyalan marigayiya Ummulkhairi Hoto: Senator Uba Sani
Source: Facebook

A hira da ya yi da Arise News, Gwamnan ya ce gwamnatin jihar tana ci gaba da kama waɗanda ake zargi, ana gudanar da bincike da kuma gurfanar da masu hannu a kisan domin tabbatar da an hukunta masu laifin.

An kama sama da mutum 100 a Kaduna

The Sun Nigeria ta wallafa cewa Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa an kama sama da mutum 100 da ake zargi da hannu a lamarin.

A cewarsa, tuni aka gurfanar da mutum 41 daga cikinsu a gaban kotu kan zargin kisan kai, yayin da wasu 41 ke ci gaba da fuskantar bincike, sannan mutum 30 kuma suna fuskantar tuhuma kan taro ba bisa ka'ida ba.

Ya ce:

"Wannan lamari mai matuƙar takaici ya faru kusan makonni biyu da suka gabata kuma ya shafi wata mata marar laifi, Ummulkhairi, wadda malamar addinin Musulunci ce. An kashe ta ba tare da ta aikata wani laifi ba."

Kara karanta wannan

An kama mutum 10 kan kashe shugaban Miyetti Allah a Benue

Yan sandan Kaduna sun fadada bincike

Uba Sani ya bayyana cewa binciken bai tsaya kan mutanen da ake zargi da hannu a harin ba kaɗai, domin ya tuntuɓi Sufeto Janar na ‘Yan Sanda kan lamarin.

Ya ce an sauya wa jami’in ‘yan sanda mai kula da ofishin Maraban Jos (DPO) wurin aiki kuma yanzu haka yana fuskantar bincike bayan iyalan marigayiyar sun gabatar da wasu zarge-zarge a kansa.

Gwamna Uba Sani ya ce an kai mutum 41 gaban kotu
Marigayi Ummulkhairi da aka yi wa kisan gilla a Kaduna Hoto: Hassan Abubakar
Source: Facebook

A cewarsa:

"Lokacin da na gana da iyalan Ummulkhairi, sun gabatar da wasu zarge-zarge kan DPO na yankin. Saboda haka babu wanda aka wanke daga zargi a wannan lokaci."

Gwamnan ya jaddada cewa duk wanda bincike ya tabbatar yana da hannu a lamarin, daga ciki har da jami’an tsaro idan an same su da laifi, za su fuskanci cikakken hukunci.

Mutane sun hallaka malama a Kaduna

A baya, mun kawo labarin yadda wasu mutane suka kashe wata mata da aka ce malamar Islamiyya ce tare da kona gawarta a Maraban Jos a jihar Kaduna, lamarin da ya tayar da hankalin yan uwa da iyalanta.

Kara karanta wannan

Tuban muzuru: Malami ya gargadi gwamnati game da karban tuban yan bindiga

An bayyana cewa da farko ta shiga ofishin 'yan sanda amma tarin mutane suka mamaye shi, suka fitar da ita, suka kashe ta kan zargi maras tushe ba tare da an tsaya an bar doka ta yi aikinta yadda ya dace ba.

Biyo bayan lamarin, rundunar 'yan sandan Kaduna ta ce ta kama wasu mutane inda ta ce za a hukunta wanda aka samu da laifi ba sani ba sabo, sai dai iyalan malamar sun zargin babban jami'i da mika ta ga jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng