Umarnin da Tinubu Ya ba EFCC game da Kuɗaɗen da Hukumar ke Ƙwacewa
- Shugaba Bola Tinubu ya umarci EFCC ta tura kudaden da aka kwace, ribar hannun jari da ba a karba ba zuwa NELFUND domin ilimi
- Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya ce matakin zai taimaka wajen tabbatar da wadatar NELFUND domin biyan bukatun dalibai da ke karuwa a fadin Najeriya
- Gwamnati ta ce kudaden da ke fuskantar shari’a ba za a tura su ba, yayin da za a mayar da wadanda ba su da takaddama ga NELFUND
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya ba Hukumar yaki da cin hanci ta EFCC umarni game da kudaden da ake kwatowa.
Tinubu ya ba Hukumar EFCC umarni ta tura dukkan kudaden da aka kwace zuwa Asusun Lamunin Ilimi na Najeriya, NELFUND.

Source: Twitter
Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manema labarai na Fadar Shugaban Kasa bayani bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya, cewar Vanguard.
Muhimmancin hukumar NELFUND a Najeriya
NELFUND wata hukuma ce ta gwamnatin tarayya da aka kafa karkashin Dokar Lamunin Dalibai, wadda ta shafi damar samun ilimi mai zurfi, bayan sake tsara dokar a shekarar 2024.
Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu kan dokar a ranar 3 ga Afrilu, 2024, domin samar da tsarin tallafawa dalibai wajen biyan kudaden karatu.
Taron ya gudana ne karkashin jagorancin Shugaba Tinubu a dakin taron Majalisar Zartarwa da ke fadar shugaban kasa, Abuja.
Ministan ya ce Shugaban Kasa ya umarci a tura dukkan kudaden da aka kwato, ribar hannun jari da ba a karba ba da kuma kudaden asusun da ba a taba amfani da su ba zuwa hukumar NELFUND.
Ya ce manufar wannan mataki ita ce tabbatar da cewa NELFUND na da isassun kudade domin iya cika nauyin da ke gabansa wanda ke kara karuwa.
“Shugaban Kasa ya umarci — kuma FEC ta amince — cewa dukkan kudaden da EFCC ta kwace ya kamata a tura su NELFUND domin tallafa wa ilimin ‘ya’yanmu."
- In ji Alausa
Dakta Alausa ya ce ilimin yara ba zai iya jira ba, yana mai cewa wannan batu na da matukar muhimmanci ga Shugaban Kasa.

Source: Twitter
Umarnin Tinubu a taron FEC kan NELFUND
A cewarsa, Shugaban Kasa ya kuma umarci, kuma FEC ta amince, cewa dukkan ribar hannun jari da ba a karba ba daga asusun amana na kasuwar hannun jari a tura ta NELFUND.
Ya kara da cewa kudaden asusun amana na bankunan da ba a gudanar da su ba su ma za a tura su hukumar NELFUND domin tabbatar da cewa asusun yana da karfin kudi.
Ya ce ana gudanar da bitar dokoki domin gano sauye-sauyen da ake bukata, tare da tabbatar da cewa tsarin yana da cikakkiyar fahimta da kuma bin doka.
Ministan ya ce akwai shirin amfani da kudaden da aka kwato wajen bai wa ilimin yara muhimmancin da ya dace.
Gwamnatin Tinubu ta samu kudi na cire tallafi

Kara karanta wannan
Abubuwan da ya dace a sani game da yarjejeniyar da aka yi tsakanin Musulmi da Kiristocin Najeriya
Mun ba ku labarin cewa Ministan Kudi Taiwo Oyedele ya bayyana makudan kudi da gwamnatin Bola Tinubu ta samu dalilin cire tallafin man fetur.
Daga cikin kudin, gwamnatin tarayya ta samu Naira tiriliyan 5.4, yayin da jihohi da ƙananan hukumomi suka raba Naira tiriliyan 10.4.
Oyedele ya ce gwamnati ta kuma samu karin kudaden shiga na Naira tiriliyan 3.1 tare da karbar bashin Naira tiriliyan 11.9.
Asali: Legit.ng

