Davido: Yan Sanda Sun Bayyana Wanda Yan Daba Suka Kai wa Hari
- ’Yan sanda sun ce maharan da suka kai hari kan ayarin gwamnan Osun sun yi hakan ne domin kai wa fitaccen mawaki Davido hari
- Rundunar ’yan sanda ta ce wani tsohon mai laifi da ake zargi da kasancewa ɗan ƙungiyar asiri ta Eye Confraternity ya yi ƙoƙarin isa wurin Davido.
- An harbe wani mutum mai shekaru 60, Tajudeen Yusuf, har lahira yayin da ake musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da waɗanda ake zargi da kai hari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Osun – Rundunar ’yan sanda ta ce wani tsohon mai laifi da ake zargin ɗan ƙungiyar asiri ta Eye Confraternity ya yi ƙoƙarin isa wurin Davido, amma jami’an tsaronsa suka hana shi.
An harbe wani mutum mai shekaru 60, Tajudeen Yusuf, har lahira yayin da ake musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da waɗanda ake zargi da ’yan daba.

Kara karanta wannan
Nasara: An kama wanda ya shirya harin da aka shiga gida gida ana yanka mutane a Najeriya

Source: Instagram
Daily Trust ta wallafa cewa fitaccen mawakin Najeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, shi ne wanda ake zargin aka yi niyyar kai wa hari yayin da aka kai farmaki kan ayarin motocin Gwamnan Jihar Osun, a cewar rundunar ’yan sandan jihar.
Yan sanda sun yi magana kan harin Osun
Blueprint ta ruwaito cewa jami’an tsaron gwamnan sun yi musayar wuta da wasu mutane da ba a san ko su waye ba a lokacin da gwamnan ya kai ziyara fadar Ataoja na Osogbo a ranar Laraba 19 ga watan Agusta, 2026.
Gwamnan ya ziyarci sarkin ne jim kaɗan bayan ya karɓi takardar shaidar nasara daga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC.
Davido, wanda ɗan’uwan gwamnan ne kuma ya taka muhimmiyar rawa a zaɓen, ya raka gwamnan zuwa ofishin INEC da kuma fadar sarkin tare da ’ya’yansa.
Yadda aka kai wa su Davido harin

Kara karanta wannan
Duk da shan wahala a zaɓen Osun, Davido ya faɗi yadda Tinubu zai yi nasara a 2027
Wasu mazauna yankin Oja Oba da ke Osogbo sun ce karar harbe-harbe ta jefa mutane cikin firgici na tsawon sama da mintuna 15, yayin da mutanen ke ci gaba da yin harbe-harbe lokaci-lokaci, jami’an tsaron gwamnan kuma suna mayar da martani.
Da yake magana kan lamarin, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sanda ta Osun, Abiodun Ojelabi, ya ce binciken farko ya nuna cewa wasu ’yan ƙungiyar asiri ta Eye Confraternity ne suka yi yunƙurin kai wa Davido hari.

Source: Instagram
Ya ce:
“Rikicin da ya biyo baya ya jawo hankalin wasu da ake zargi ’yan ƙungiyar ne da ke yankin, waɗanda suka toshe ƙofar shiga fadar na wani lokaci tare da hana ayarin motocin gwamnan wucewa."
Ya ce jim kaɗan bayan haka, mutanen da ake zargin ’yan ƙungiyar ne sun bar wurin, amma yayin da suke kan hanyarsu, sun harbi wani mutum mai suna Tajudeen Yusuf a yankin Itaolokan da ke Osogbo.
Mahaifin Davido ya magantu kan zaben Osun
A wani labarin kun ji cewa Dr Adedeji Adeleke ya yi murna cewa nasarar da dan uwansa ya samu amsa ce ta addu'o'in da suka rika yi na neman lashe zaben da aka gudanar a ranar Asabar 15 ga watan Agusta, 2026.
Attajirin ya zargi Oyetola da kokarin hana dan uwansa, Gwamna Ademola Adeleke, yin nasara a zaben Osun, amma daga baya suka samu nasarar doke dukkanin abokan hamayya a zaben jihar.
Yayan gwamnan ya ce sun fuskanci mummunar kiyayya da siyasa saboda minista yana so APC ta koma mulki idonsu a rufe ba tare da la'akari da an kashe bayin Allah ko an bar su da rai ba.
Asali: Legit.ng
