Akwai Matsala: Ruwan Kogi na Shirin Ballewa Ya Mamaye Kaduna, Jigawa da Wasu Jihohi

Akwai Matsala: Ruwan Kogi na Shirin Ballewa Ya Mamaye Kaduna, Jigawa da Wasu Jihohi

  • Hukumar NiHSA ta yi gargadin cewa akwai babban haɗarin ambaliyar koguna a Kaduna, Neja da wasu jihohi 31 tsakanin 19 zuwa 25 ga Agusta 2026
  • Hukumar ta buƙaci al’ummomin da ke zaune a wuraren da ambaliya ka iya shafa su koma wurare masu tudu da aminci
  • Ta kuma buƙaci gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi su dauki matakin gaggawa don tunkarar ambaliyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Hukumar Kula da Harkokin Ruwa ta Najeriya (NiHSA) ta yi gargadin cewa akwai babban haɗarin ambaliyar koguna a Kaduna, Neja da wasu jihohi 31 tsakanin 19 zuwa 25 ga Agusta 2026.

Hukumar ta buƙaci mutanen da ke zaune a wuraren da ambaliya ke iya shafa su koma wurare masu tudu da aminci.

Ambaliya.
Yadda ruwa ya mamaye gidaje sakamakon ambliyar da aka yi Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ta kuma yi kira ga gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi da su dauki tsarin gargadin gaggawa da matakan tunkarar ambaliyar, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

Abubuwan da ya dace a sani game da yarjejeniyar da aka yi tsakanin Musulmi da Kiristocin Najeriya

Shugaban hukumar NiHSA, Arc Umar Mohammed, ne ya bayyana hakan a sabon rahoton gargadin ambaliya na kwanaki bakwai da hukumar ta fitar.

Jihohin da ambaliya ke barazana

“Lokacin da ake wannan hasashen ambaliyar da ta auku shi ne daga 19 zuwa 25 ga Agusta 2026. Ana hasashen babban haɗarin ambaliyar koguna cikin kwanaki bakwai masu zuwa a Kaduna, Neja da wasu jihohi 31," in ji shi.

Jihohin da aka lissafa cikin hasashen sun haɗa da Taraba, Ondo, Oyo, Rivers, Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bayelsa, Benue, Borno, da kuma Cross River.

Sauran sun hada da Delta, Ebonyi, Edo, Enugu, Gombe, Imo, Jigawa, Kogi, Kwara, Nasarawa, Lagos, Ogun, Osun, Plateau, Kaduna da Neja, da sauran jihohi.

Wuraren da ambaliyar za ta iya barna

NiHSA ta kuma bayyana wasu al’ummomi da muhimman gine-gine da ababen more rayuwa da ke fuskantar barazanar ambaliya a wasu jihohin.

A Jihar Kaduna, hukumar ta ce al’ummomi 2,006, makarantu 453, cibiyoyin kiwon lafiya 69, kasuwanni 12 da gine-ginen addini 213 na cikin wuraren da ke fuskantar haɗarin ambaliya.

Kara karanta wannan

Dalibai 4 na makarantar haddar Kur'ani sun mutu lokaci guda a jihar Kano, an gano dalili

A Jihar Neja kuwa, an gano al’ummomi 898, makarantu 524, cibiyoyin kiwon lafiya 268, kasuwanni 12, gine-ginen addini 318 da hekta 23 na gonaki a matsayin wuraren da ambaliya za ta iya shafa.

A Jihar Delta, wuraren da aka gano sun haɗa da al’ummomi 1,046, makarantu 1,850, cibiyoyin kiwon lafiya 505, kasuwanni 192, gine-ginen addini 492 da hekta 16 na gonaki, cewar rahoton Punch.

Matakan kariya daga ambaliya

Mohammed ya shawarci gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi da su kwashe mutane, dabbobi da kayayyaki daga filayen ambaliya zuwa wuraren da aka riga aka tantance masu tudu.

Ya kuma buƙaci hukumomi su tattara masu aikin sa-kai na gargadin ambaliya, su share magudanan ruwa da wuraren fitar da ruwa da suka toshe, tare da tanadin kayan agaji, kayayyakin tsaftace ruwa tun kafin afkuwar ambaliya.

Ruwan sama.
Ruwan sama yana sauka a wasu sassan Najeriya Hoto: Adamu Shehu
Source: Facebook

Hukumar ta gargadi mazauna yankunan da su guji ketare hanyoyi, gadoji ko ruwa mai gudu idan ambaliya ta mamaye su, ko da a ƙafa ne ko cikin abin hawa.

Ta kuma shawarci al’umma da su guji yin gine-gine ko zama a filayen ambaliya, tare da bibiyar sanarwar NiHSA domin samun sabbin bayanai kan matakan ruwa a koguna.

Kara karanta wannan

Yadda motoci suka nutse, komai ya tsaya cak bayan ambaliya a Abuja

Ruwan sama ya haddasa ambaliya a Abuja

A wani rahoton, an ji cewa ruwan sama mai ƙarfi ya haddasa ambaliyar ruwa a sassa daban-daban na Abuja, inda ya katse zirga-zirgar ababen hawa.

Ambaliyar ta shafi titunan Wuse 2, Gudu da Lokogoma, yayin da gadar da ta haɗa Gaduwa da Durumi ta cika da ruwa, lamarin da ya tilastawa kowa ya tsaya cak.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262