Uba Sani Ya Ziyarci Iyalan Malamar Islamiyya da Aka Kashe, Ya Daukar Masu Alkawura
- Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan malamar Islamiyya da aka kashe a Mararraban Jos
- Sanata Uba Sani ya bayyana cewa an gurfanar da wasu mutanen da ake zargin akwai hannunsu a kisan da aka yi wa marigayiyar
- Gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar Kaduna za ta dauki nauyin karatu da kula da marayun da ta bari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya ziyarci iyalan Ummulkhairi Usman Aliyu, malamar Islamiyha da gungun fusatattun mutane suka kashe.
Gwamna Uba Sani ya tabbatarwa danginta cewa za a gurfanar da waɗanda ke da alhakin kisan a gaban shari'a, yayin da gwamnatin jihar za ta kula da ilimi da jin daɗin yaranta.

Source: Facebook
Gwamnan ya bayyana haka ne a cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook, biyo bayan ziyarar ta'aziyya da ya kai ga iyalai da aka yi wa rashi a Maraban Jos ranar Asabar, 27 ga watan Yunin 2026 da yamma.

Kara karanta wannan
Gwamna Abba ya raba wa hadimai filaye da kudi, ya yi magana kan zaɓen Tinubu a 2027
Uba Sani ya ziyarci iyalan Ummulkhairi
A cewar Gwamna Uba Sani, ziyarar ta kasance ne domin nuna aljini da juyayi da kuma nuna goyon baya ga iyalan a lokacin da ya bayyana da “lokaci na tsananin baƙin ciki.”
“Na kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan marigayiya Ummulkhairi Usman Aliyu a Maraban Jos, Kaduna, domin nuna juyayi na kashin kaina da kuma nuna masu goyon baya a lokaci na tsananin baƙin ciki."
“Na haɗu da mijinta, Malam Aliyu, da sauran mambobin iyalinsa, inda na isar da ta'aziyya ta tare da tabbatar masu cewa, a wannan lokaci na raɗaɗin rashi, muna tare da su."
“Na yi addu'a ga Allah Maɗaukakin Sarki da ya ba wa Ummulkhairi hutun dindindin kuma ya ƙarfafa masoyanta da haƙuri da juriyar jure wannan babban rashi.”
- Gwamna Uba Sani
An gurfanar da wadanda ake zargi
Gwamna Uba Sani ya sake jaddada sadaukarwar gwamnatinsa wajen tabbatar da adalci, inda ya bayyana cewa za a gano duk wanda ke da alaƙa da kisan kuma a gurfanar da shi gaban kotu.
Yayin da yake bayar da sabon bayani kan binciken da ake gudanarwa, gwamnan ya bayyana cewa hukumomin tsaro sun riga sun gurfanar da tarin mutanen da ake zargi yayin da bincike ke ci gaba da gudana.
“Na sanar da iyalan cewa an gurfanar da mutane 41 da ake zargi a kotu kan laifin kisan kai, yayin da mutane 30 da ake zargi aka gurfanar da su kan laifin taro ba bisa ka'ida ba."
"Bugu da ƙari, an saki mutane 17 da ba a samu laifi a tare da su ba, yayin da sauran mutane 41 ke tsaka da kasancewa ƙarƙashin bincike yayin da hukumomin tsaro ke tsananta ƙoƙari domin kama ƙarin mutanen da ake zargi da suka tsere a yanzu."
“Na ƙara tabbatar musu cewa ana nan ana gudanar da bincike kuma duk wani jami'in ɗan sanda da aka gano yana da hannu kai-tsaye ko ta wata hanyar zai fuskanci cikakken hukuncin doka."
- Gwamna Uba Sani

Source: Facebook
Za a dauki nauyin karatun yaranta
Gwamnan ya kuma sanar da cewa gwamnatin jihar Kaduna za ta ɗauki alhakin karatu da jin daɗin yaran da marigayiyar ta bari.

Kara karanta wannan
'Kashi 80 na matsalolin tsaro da suka addabi Sakkwato na da alaka da miyagun kwayoyi'
“Mun kuma yi alƙawari ga Malam Aliyu cewa gwamnatin jihar Kaduna za ta ɗauki alhakin karatu da jin daɗin yaran da Ummulkhairi ta bari."
- Gwamna Uba Sani
An gurfanar da mutane kan kisan Ummulkhairi
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta sanar da kama tare da gurfanar da karin mutum 17 a gaban kotu kan kisan gillar da aka yi wa Malama Ummulkhairi.
Rundunar ta bayyana cewa bincike kan lamarin na ci gaba, tare da alƙawarin gurfanar da duk wanda aka tabbatar yana da hannu a kisan.
Bayan kammala binciken farko, an kuma gurfanar da wasu mutum 33 bisa zargin haɗa baki da kuma shiga taron da ba bisa ƙa'ida ba dangane da lamarin.
Asali: Legit.ng
