DSS da Yan Sanda Sun Yi Bincike, An Ji Gaskiya kan Bullar Sabuwar Ƙungiyar Ta'addanci a Najeriya
- Gwamnatin Kebbi ta musanta rahoton ɓullar wata kungiyar ta'addanci mai suna Sai Malam a wasu yankunan jihar
- Kwamishinan yada labarai na Kebbi, Alhaki Yakubu Ahmed ne ya bayyana hakan, yana mai cewa wadanda ake zargi matasa ne yan damfarar intanet
- Gwamnatin ta kuma musanta rahoton mutuwar yara 130 a kullum, tana zargin 'yan adawa da yada bayanan karya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kebbi, Nigeria - Kwamishinan Yada Labarai da Al'adu na Kebbi, Alhaji Yakubu Ahmed, ya musanta rahotannin da ke cewa wata sabuwar kungiyar ta'addanci mai suna Sai Malam ta bullo a jihar.
Ahmed ya bayyana hakan ne yayin da ya jagoranci tawagar kafafen yada labarai domin kai ziyarar ban girma ga Shugaban Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN), Malam Ali M. Ali, a Abuja.

Source: Facebook
A rahoton Vanguard, ya bayyana rahoton a matsayin karya tsagwaronta da kuma wani yunkuri na yaɗa bayanan da ba su dace ba domin cimma muradun siyasa gabanin babban zaben 2027.
Abin da bincike ya gano kan kungiyar
Kwamishinan ya ce binciken da Hukumar Tsaro ta DSS da Rundunar 'Yan Sanda suka gudanar ya nuna cewa ba wata kungiyar ta'addanci ba ce, illa wasu matasa da ake zargi da aikata damfarar intanet.
A cewarsa, matasan na amfani da fasahar kwamfuta wajen tuntubar jami'an gwamnati da sauran mutanen da suke zaton suna da kudi domin damfararsu.
Ya ce:
"Lokacin da aka fara yaɗa wannan labari, ya jefa mutane cikin fargaba. Mun samu kira daga sassa daban-daban na Najeriya da ma kasashen waje suna neman sanin gaskiyar lamarin.
"Sai DSS da 'yan sanda suka gudanar da cikakken bincike, inda suka gano cewa ba kungiyar ta'addanci ba ce, wasu matasa ne masu aikata damfarar intanet."

Kara karanta wannan
Allah Ya ceci wani mutumi da matarsa ta lallaba za ta yanka masa wuya yana barci a Katsina
Ahmed ya kara da cewa an kama wasu daga cikin wadanda ake zargi, kuma su ne ake kira Yan Vocal, wadanda yanzu wasu ke alakanta su da sunan Sai Malam.
Gwamnatin Kebbi ta zargi 'yan adawa
Kwamishinan ya ce binciken ya nuna cewa wasu 'yan adawa ne suka kirkiri wadannan rahotanni domin cimma manufar siyasa, kamar yadda Leadership ta rahoto.
Ya ce gwamnatin jihar na fuskantar kalubalen yada bayanan karya da rabin gaskiya daga wasu masu adawa da gwamnati domin bata mata suna.
"Suna kara gishiri a kan duk wani lamari saboda suna tunanin hakan zai ba su wata riba ta siyasa," in ji shi.

Source: Original
Ahmed ya kuma musanta rahoton da ya ce yara fiye da 130 na mutuwa a kullum a Jihar Kebbi sakamakon yawan mace-macen yara.
Ya bayyana rahoton a matsayin kirkirarren labari da aka yi domin bata sunan gwamnatin Gwamna Nasir Idris kafin babban zaben 2027.
Matakin da gwamnatin Kebbi ta dauka
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Kebbi ta ayyana gagarumin yaƙi da wata sabuwar kungiyar masu aikata laifuffukan yanar gizo da aka sani da “Yan Vocal".

Kara karanta wannan
Kungiyar Obidient ta bada tabbaci kan takarar Obi da Kwankwaso a 2027 duk da hukuncin kotu
Gwamnatin ta yi alƙawarin tarwatsa hanyoyin sadarwar su da kuma.gurfanar da waɗanda ke da alhakin karuwar damfara ta yanar gizo a gaban kotu.
A wata sanarwa da ta fitar, gwamnatin ta bayyana ayyukan ƙungiyar a matsayin wata barazana ga al'umma da kuma tsaron ƙasa.
Asali: Legit.ng
