‘Jahilci ke Damunsu’: Matashi Ya Kare Kalaman Jingir kan Tinubu, Muslim Muslim

‘Jahilci ke Damunsu’: Matashi Ya Kare Kalaman Jingir kan Tinubu, Muslim Muslim

  • Matashin ɗan siyasa Khamis Musa Darazo ya soki masu zagin Sheikh Sani Yahaya Jingir, yana mai cewa irin wannan hali rashin tarbiyya ne
  • Darazo ya ce bai kare Sheikh Jingir ba saboda goyon bayan gwamnatin Tinubu kawai, sai dai ya yi Allah wadai da cin mutuncinsa
  • Ya bayyana cewa malamin na da ’yancin bayyana ra’ayinsa, tare da yi masa addu’ar Allah Ya ƙara masa lafiya, daraja da tsawon rai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Darzo, Bauchi - Wani matashin dan siyasa a jihar Bauchi ya yi magana game da yadda ake sukar Sheikh Sani Yahaya Jingir a kwanakin nan.

Khamis Musa Darazo wanda aka fi sani da goyon bayan gwamnatin Bola Tinubu ya nuna goyon bayansa game da kalaman malamin.

Matashi ya kare Jingir da ya goyi bayan Tinubu
Sheikh Sani Yahaya Jingir, Khamis Musa Darazo da Bola Tinubu. Hoto: Khamis Musa Darazo, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Darazo ya bayyana haka ne yayin zantawa da wakilin Legit Hausa a yau Laraba 19 ga watan Agustan shekarar 2026 da muke ciki.

Kara karanta wannan

Duk da shan wahala a zaɓen Osun, Davido ya faɗi yadda Tinubu zai yi nasara a 2027

Darazo ya kare kalaman Jingir game da Tinubu

Matashin dan siyasar ya ce ko kadan bai goyon bayan malamin kawai domin sun hada layi daya a siyasa na goyon bayan gwamnatin Bola Tinubu.

Sai dai ya ce abin da mutane ke yi wa malamin da yadda suke zaginsa musamman a kafofin sadarwa kwata-kwata bai dace ba.

Ya kara da cewa babu mai zagin Malam Ssani Yahaya Jingir sai wanda bai da tarbiyya ko kuma jahili da bai san darajar mahaifansa ba.

A cewarsa:

"Babu mai zagin malam sai dan tasha, jahili koh kuma wanda bai da tarbiyya da rashin ganin darajar mahaifansa.
"Zan yi magana ne ba wai don malam yana bayan abin da nake kai a siyasa ba sai dai domin rashin tarbiya da jahilici da ke damun wasu daga cikinmu.
"Wallahi ko da malam ba masanin addini ba ne a shekurunsa inda wasu daga cikinmu suna da tarbiyya bai kamata a ce suna kafe hoton malam suna bakaken maganganu akan sa ba."

Kara karanta wannan

'Ba su yi mana ta'aziyya ba': Hadimim marigayi ɗan majalisar tarayya ya soki ADC

Yabon gwamnatin Tinubu da Jingir ya yi ya jawo magana
Sheikh Sani Yahaya Jingir da Bola Tinubu. Hoto: JIBWIS Gombe state, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Masoyin Tinubu ya yi ruwan addu'o'i ga Jingir

Darazo ya kara da cewa Sheikh Sani Yahaya Jingir yana da damar bayyana abin da yake ransa kuma yana da yancin haka a matsayinsa na ɗan ƙasar Najeriya.

Daga karshe, ya yi addu'ar Ubangiji ya kara wa Malam lafiya da daraja ta kuma azurta shi nisan kwana mai albarka.

"Domin yana da dama da iko da kuma yancin da zai bayyana abin da yake so kuma ya nusar da mutane abin da ya kamata a fahimtarsa.
" Allah Ubangiji ya kara wa malam lafiya da daraja da nisan kwana mai Albarka, Allahumma Ameen."

Jingir ya yi karin haske kan kalamansa

Mun ba ku labarin cewa Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi karin bayani kan kalaman da ya yi game da takarar musulmi da musulmi a wurin daura auren gata a Kano.

Shugaban Majalisar malamai ya ce kiransa na goyon bayan tikitin Musulmi da Musulmi a 2027 ra’ayinsa ne na kansa.

Ya ce ba matsayar kungiyar JIBWIS ba ce kuma bai kamata a dauke shi a matsayin umarnin kungiyar ba sai dai kawai radin kansa.

Wanda ya tantance Abdullahi Abubakar, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.