Rahoto: Muhimman Ayyukan Alheri 7 da Za a Tuna Marigayi Aminu Dantata da Su

Rahoto: Muhimman Ayyukan Alheri 7 da Za a Tuna Marigayi Aminu Dantata da Su

Kano - Alhaji Aminu Alhassan Dantata, fitaccen ɗan kasuwa kuma mashahurin mai bada tallafi daga Arewacin Najeriya, ya rasu yana da shekaru 94 a Abu Dhabi.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Daga kasuwanci zuwa aikin jin ƙai, Dantata ya bar gagarumin gurbi da zai yi wahalar cikewa a tarihin Najeriya, musamman ga Arewacin kasar.

Alhaji Aminu Dantata ya rasu ya bar babban gurbin da zai yi wahalar cikewa a Arewa da Najeriya baki daya
Alhaji Aminu Dantata ya rasu a Abu Dhabi yana da shekaru 94 a duniya. Hoto: @SasDantata
Asali: Twitter

Ayyukan da za a rika tunawa da Dantata

An haife shi a cikin babbar zuriyar nan ta Dantata, wadda ta daɗe tana gudanar da kasuwanci a fadin Afirka ta Yamma, inji rahoton WikiPedia.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma fiye da gadon alhalinsa, Aminu Dantata ya kafa nasa suna ta hanyar ayyukan jin ƙai da sadaka, musamman a Arewacin Najeriya.

Yayin da ya gina masallatai, makarantu da asibitoci, bai taɓa neman suna ko jiran yabon mutane ba, yana gudanar da sadakarsa cikin sirri da tawali’u.

Wannan rahoto na Legit Hausa zai duba muhimman gudunmawar da za a ci gaba da tunawa da su a game da Dantata — daga ilimi da lafiya zuwa taimakon gaggawa, addini da ci gaban al’umma.

1. Ayyukan taimako da jin-kan al'umma

Ayyukan alherin Aminu Dantata sun samo asali ne daga kyawawan halayen zuriyarsa da kuma addininsa na Musulunci wanda ke jaddada muhimmancin yin taimako.

A matsayinsa na ɗan Alhassan Dantata, ɗaya daga cikin attajiran Afirka ta Yamma a karni na 20, Aminu ya gaji babbar harkar kasuwanci da taimakon jama’a.

Mahaifinsa ya yi fice wajen daukar nauyin mutane su je aikin Hajji da tallafa wa marasa ƙarfi a lokacin karama da babbar Sallah, al’adar da Aminu ya ci gaba da riko da ita tare da faɗaɗa ta.

Ya shafe shekaru 94 yana cika alkawurran taimako bisa imani da cewa: “gwargwadon farin cikin da ka sanya wasu, gwargwadon farin cikin da za ka karawa kanka."

Dantata bai so a bayyanar da taimakonsa ba, kuma bai nemi yabo ko ɗaukaka ba, sai dai ya yi amfani da dukiyar da Allah ya ba shi wajen gyara rayuwar jama’a.

Kodayake yawancin ayyukansa ba a san su ba, girman tasirinsu ya haifar da yabo daga shugabanni da talakawan kasar nan.

2. Gina ilimi ta hanyar gidauniyar jihar Kano

Ɗaya daga cikin fitattun gudunmawar Aminu Dantata shi ne kasancewarsa cikin waɗanda suka kafa gidauniyar jihar Kano, inji rahoton Business Day.

Wannan gidauniyar tana ba da tallafin karatu ga dalibai da ba da gudunmawar jari ga masu ƙananan sana’o’i.

Baya ga haka, Legit Hausa ta rahoto cewa Dantata da kansa ya ɗauki nauyin karatun ɗalibai da dama a fadin Najeriya.

Haka nan, ya ci gaba da tallafa wa Makarantar Dantata da mahaifinsa ya kafa a shekarar 1955 — wacce ta kasance cikin farkon makarantu masu zaman kansu a Arewacin Najeriya.

Yayansa, Dr. Munzali Dantata, ya bayyana cewa jajircewarsa wajen habaka ilimi alama ce ta yadda yake ganin ilimi a matsayin matakin cigaban mutum da al’umma gaba ɗaya.

Har ila yau, ya zama shugaban farko na jami’ar Al-Qalam da ke Katsina, tare da bayar da gudunmawa ga jami’o’i kamar jami'ar Ahmadu Bello, jami'ar Bayero da sauran makarantu.

An ba Alhaji Aminu Dantata digirin girmamawa da kuma lambar yabo a matsayin gwarzo da ke tallafawa ilimi.

Alhaji Aminu Dantata ya gina cibiyar wankin koda ta Dantata a Kano
Alhaji Aminu Dantata ya rasu a Abu Dhabi yana da shekaru 94 a duniya. Hoto: @SasDantata
Asali: Facebook

3. Kiwon Lafiya: Cibiyar Haemodialysis ta Dantata

A fannin lafiya ma, Aminu Dantata ya taka gagarumar rawa. Muhimmiyar gudunmawarsa ita ce gina cibiyar jinyar koda ta Alhassan Dantata a asibitin koyarwa na Aminu Kano.

Wannan katafariyar cibiyar zamani ta ke ba da kulawa ga marasa lafiya masu fama da cutar koda, wacce ta cike gibin da ke akwai a tsarin kiwon lafiyar Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Alhaji Aminu Dantata ne ya ɗauki nauyin dukkanin kayan aiki da gudanarwar cibiyar.

Baya ga haka, ya tallafa wajen gina cibiyoyin lafiya a sassa daban-daban na Arewa, ya sayo kayan aiki, ya gyara asibitoci, da goyon bayan shirye-shiryen kiwon lafiya don rage matsalolin jama’a.

Wadannan ayyuka sun nuna irin yadda ya damu da jin daɗin al’ummarsa, musamman a Kano da kewaye.

4. Taimakon gaggawa: Jin-kai a lokacin musifa

Aminu Dantata ya shahara wajen kai daukin gaggawa a lokacin musifu, musamman lokacin ambaliyar ruwa da ta auku a jihar Borno a shekarar 2024.

A lokacin, ya bayar da tallafi na Naira biliyan 1.5 domin tallafa wa waɗanda ibtila’in ya shafa kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Wannan gudunmawa, wacce aka yi tare da Aliko Dangote, ta jaddada jajircewar dangin Dantata wajen kai dauki ga al’umma a lokacin bukatu.

A shafukan sada zumunta irin su X (Twitter), mutane da dama sun yabawa halin kirki da tausayinsa.

Wannan taimako ba shi ne na farko ba, kasancewar Dantata ya saba tallafa wa marayu, gajiyayyu da mata marasa galihu.

Yadda ya ke iya hanzarta samar da agaji cikin kankankin lokaci ya janyo masa karbuwa a matsayin mai taimakon al’umma na gaske.

5. Goyon bayan addini da al’adun Arewa

A matsayin Musulmi mai tsantseni, Dantata ya haɗa ayyukan jin ƙai da imani. Ya gina masallatai da dama a fadin Najeriya domin bai wa jama’a wurin yin ibada.

Haka kuma, ya tallafa wa makarantun Islamiyya da cibiyoyin karatun addini, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen karfafa tushen al’adun Hausawa da Musulunci.

Ya ci gaba da fadada al’adar mahaifinsa na daukar nauyin mutane su je aikin Hajji, yana bai wa masu ƙaramin ƙarfi damar sauke farali.

Bugu da ƙari, ya tallafa wa malamai da malaman addini domin ƙarfafa tushe na addini da tarbiyya a Arewacin Najeriya.

6, Kula da matasa da haɓaka jama’a

Baya ga tallafi na kudi, Aminu Dantata ya shahara wajen jagoranci da horar da matasa da ‘yan kasuwa, inji rahoton PM News.

Ya taimaka wa dimbin masu neman ci gaba ta hanyar shawarwari da goyon baya, wanda hakan ya taimaka matuka wajen haɓaka sashen kasuwanci na Najeriya.

Ya kasance Life Patron a cibiyar kasuwanci, masana'antu, hakar ma'adanai da noma ta Najeriya (NCCIMA), wanda ya jaddada jajircewarsa wajen bunkasa tattalin arziki.

Dantata ya kuma shahara wajen ba da shawarwari ga shugabanni — daga shugabannin ƙasa zuwa gwamnoni — inda ya taka rawa wajen sasanta rikicin addini da kabila a ƙasar.

Irin yadda ya haɗa kan mutane daga dukkanin sassa da tsararraki ya sa aka dauke shi a matsayin ginshiƙin haɗin kan Najeriya.

Aminu Dantata ya gina masallatai, makarantu tare da daukar nauyin mutane su je aikin Hajji
Alhaji Aminu Dantata ya rasu a Abu Dhabi yana da shekaru 94 a duniya. Hoto: @SasDantata
Asali: Twitter

7. Rayuwa cike da tawali’u da tunanin lahira

A shekarun ƙarshe na rayuwarsa, mun ruwaito cewa Aminu Dantata ya fara nuna shirin barin duniya da tawali’u.

A wata ganawa da Kashim Shettima a 2022, ya bayyana cewa:

"Ina jiran lokacina, ina fata na bar duniya cikin ƙoshin lafiya da imani."

Ya nemi gafara daga duk wanda ya taɓa yi wa kuskure kuma ya yafe wa waɗanda suka cutar da shi. Wannan hali ya dace da yadda ya ke rayuwa bisa ka’idar jin-kai da yafiya.

Rasuwar Aminu Dantata a Abu Dhabi a ranar 28 ga Yuni, 2025, ta kawo ƙarshen wani zamani amma ta bar gadon ayyukan alherinsa, da kuma sadaka mai gudana.

Shugaba Bola Tinubu, mataimakin shugaba Kashim Shettima da sauran manyan ‘yan Najeriya sun nuna alhini da girmamawa ga irin gudunmawar da ya bayar ga cigaban ƙasa.

Kammalawa

Alhaji Aminu Dantata ya shafe rayuwarsa wajen gina jama'a da ayyukan alheri wanda ya nuna sadaukarwarsa ga hidimar al’umma, addini da ci gaban kasa.

Daga gidauniyar jihar Kano zuwa cibiyar Haemodialysis, daga taimakon ambaliya a Borno zuwa daukar nauyin aikin Hajji da gina masallatai — irin wannan gudunmawa ta bar tarihi mai zurfi.

Abubuwan da za a tuna da shi sun hada da tawali’u, alheri da sadaukarwa — abubuwan da za su ci gaba wanzuwa da zamar wa al’umma haske har abada.

Yayin da Najeriya ke jimamin rasuwarsa, rayuwarsa ta tuna mana cewa dukiya ta gaskiya ba a cikin abin da mutum ya tara ba ce, sai a cikin abin da ya bayar.

An yi jana'izar Dantata a birnin Madina

Tun da fari, mun ruwaito cewa, bayan cika dukan sharuɗɗan Saudiyya, an yi jana'izar marigayi Alhaji Aminu Ɗantata a birnin Manzon Allah S.A.W.

Kamar yadda ya bar wasiyya, an yi wa fitaccen ɗan kasuwar sallah ta jana'iza a masallacin Annabi kuma an birne shi a maƙabartar Baqi'a.

Manyan jiga-jigai daga Najeriya da wakilan gwamnatin tarayya, ƴan uwa da iyalai sun halarci jana'izar yau Talata, 1 ga watan Yuli 2025.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.