An Cafke Dan Amurka na Leken Asiri a China Kwanaki bayan Ziyarar Trump

An Cafke Dan Amurka na Leken Asiri a China Kwanaki bayan Ziyarar Trump

  • Rahoto ya nuna cewa jami’an tsaron ƙasar China sun kama wani ɗan ƙasar Amurka da ke nazarin harkokin siyasa a Myanmar da ke kusa da ita
  • Wasu mutane da ke da masaniya kan cafke mutumin sun bayyana cewa ana zargin dan Amurkan da barazana ga tsaron ƙasar China
  • An kama mutumin mai suna U Min Zin a farkon watan Yunin 2023, in ji majiyoyin da suka nemi a sakaya sunayensu saboda yanayin diflomasiyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

China - Rahotanni da suka fito daga China sun nuna cewa kasar ta kama wani masanin harkokin siyasa dan Amurka bisa zargin leƙen asiri.

Ma’aikatar harkokin wajen China ta tabbatar da kama mutumin mai suna U Min Zin a ranar Juma’a 12 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

Dan bindiga ya kai hari Amurka ana gasar kofin duniya a kasar

Shugaban kasar China a ofis
Shugaban kasar China, Xi Jinping. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

China ta cafke dan Amurka da leken asiri

Reuters ta wallafa cewa Zin na jagorantar wata cibiyar bincike da ta mayar da hankali kan Myanmar, inda aka ce ana zarginsa da leƙen asiri da kuma barazana ga tsaron ƙasar China.

“An fahimci cewa hukumomin da abin ya shafa sun tsare Min Zin bisa tanadin doka saboda zargin shiga harkokin leƙen asiri da kuma barazana ga tsaron ƙasar China,”

In ji mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen China, Lin Jian yayin wani taron manema labarai na yau da kullum.

Ya ƙara da cewa China ta sanar da ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Guangzhou da ke kudancin kasar game da cafke mutumin.

An tsare Min Zin ne bayan ya isa Kunming da ke Kudu maso Yammacin China, kamar yadda wasu mutane uku da ke da masaniya kan lamarin suka bayyana.

New York Times ta ce duk da tabbatar da labarin, dukkan mutanen sun nemi a sakaya sunayensu saboda muhimmancin lamarin.

Kara karanta wannan

Duniya za ta huta: Trump ya ce yaki da Iran ya zo karshe, babu sauran kai hari

Kasar Amurka ba ta ce komai ba

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka da kuma ISP-Myanmar ba su mayar da martani nan take ba kan buƙatar manema ta neman bayani.

Kamun ya zo ne a lokacin da Amurka da China ke ƙoƙarin daidaita dangantakarsu da ta yi tsami bayan ziyarar da Shugaba Donald Trump ya kai Beijing a watan da ya gabata.

Min Zin, wanda tsohon ɗan gwagwarmayar ɗalibai ne kuma ya shiga fafutukar dimokuraɗiyya ta Myanmar ta shekarar 1988, ya karanci kimiyyar siyasa a Jami’ar California da ke Berkeley.

Shugaba Donald Trump a China
Donald Trump da Shugaban China a lokacin da suka gana a kwanakin baya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ya kuma taimaka wajen kafa ISP, wadda tun farko tana aiki a cikin Myanmar amma daga baya ta koma ƙasashen waje bayan juyin mulkin shekarar 2021, lokacin da sojoji suka hambarar da gwamnatin farar hula.

Juyin mulkin ya jefa Myanmar a dogon yaƙin basasa, inda sojoji ke fafatawa da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da kuma rundunonin ƙabilu daban-daban, rikicin da cibiyar ISP ta Min Zin ke sa ido a kansa.

Kara karanta wannan

Yadda aka sulale da sinadarin hada nukiliya a asirce daga Venezuela zuwa Amurka

China ta yi kira ga Amurka/Iran

A wani labarin, kun ji cewa China ta yi kira ga Washington da Tehran da su daina ƙara tsananta rikici bayan Amurka ta kai sababbin hare-hare kan Iran.

China ta ce tana cikin damuwa game da sabon yanayin da ake ciki, kamar yadda kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar, Lin Jian ya fada a Beijing.

Rundunar sojin Amurka ta ce sun kai hare-haren sama kan wuraren sojin Iran a matsayin martani ga harbo wani jirgin yaƙin ta na Apache.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng