An yi tiyatar dashen koda 60 a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano
An sanar da samun nasarar yin tiyatar dashen koda kashi sittin a asibitin koyar wa na Mallam Aminu Kano da ke jihar Kano kan marasa lafiya daban-daban daga dukkanin sassa a fadin Najeriya.
Sanarwar na kunshe ne cikin wasu jawabai na babban likitan asibitin, Aminu Zakari, a yayin bikin cikar asibitin wanda ya kasance na gwamnatin tarayya shekaru 31 da kafuwa kamar yadda jaridar Kano Focus ta ruwaito.
Dakta Zakari wanda ya kasance Farfesan nazarin cututtuka, ya ce tawagar kwararrun likitoci na asibitin wanda aka fi sani da asibitin Mallam, sun gudanar tiyatar dashen koda ta baya-bayanan ne a watan Agusta.
Sai dai babban likitan ya bayyana damuwa musamman dangane da kalubale da suke fuskanta na rashin samun wadataccen wurin tatance nagarta da lafiyar koda gabanin a yi dashenta a asibitin.
KARANTA KUMA: Akwai hukuncin da har yanzu kotu ba tabo ba kan laifukan da ake tuhumar Sowore, Dasuki da El-Zakzaky
Ana iya tuna cewa, a shekerar 2010 wanda ya kasance karo na farko a Najeriya, asibitin koyarwa na Jami'ar Maiduguri ya gudanar da aikin tiyatar dashen koda shekaru goma sha bakwai bayan da aka kafa cibiyar lura da masu cutar kodar na shiyyar arewa maso gabashin kasar.
Kamar yadda jaridar BBC Hausa ta ruwaito, kwararrun likitoci ne daga asibitocin koyarwa na Mallam Aminu Kano da na jami'ar Obafemi Awolowo suka halarci wannan aikin tiyata domin tallafa wa takwarorinsu na Jami'ar Maiduguri.
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng