Allahu Akbar: Yadda Aka Yi Jana'izar Aminu Ɗantata a Masallacin Annabi SAW a Madina
- Bayan cika dukan sharuɗɗan Saudiyya, an yi jana'izar marigayi Alhaji Aminu Ɗantata a birnin Manzon Allah S.A.W
- Kamar yadda ya bar wasiyya, an yi wa fitaccen ɗan kasuwar sallah ta jana'iza a masallacin Annabi kuma an birne shi a maƙabartar Baqi'a
- Manyan jiga-jigai daga Najeriya da wakilan gwamnatin tarayya, ƴan uwa da iyalai sun halarci jana'izar yau Talata, 1 ga watan Yuli 2025
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Madina - Daga ƙarshe, an yi jana'izar fitaccen ɗan kasuwa na Najeriya, Alhaji Aminu Dantata, wanda ya rasu ranar Asabar a Abu Dhabi, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).
An birne shi ne ranar Talata a maƙabartar Al-Baqi'a da ke Madina, ƙasar Saudiyya bayan an gudanar da sallar jana’iza da Magariba a Masallacin fiyayyen halitta, Annabi SAW.

Asali: Twitter
Vanguard ta rahoto cewa an kawo gawar marigayin Madina da safiyar ranar Talata, 1 ga watan Yuli, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ɗansa, Alhaji Tajudeen Dantata, ɗan uwansa kuma fitaccen ɗan kasuwa, Alhaji Aliko Dangote, da sauran ’yan uwa da danginsa ne suka ɗauko gawar daga Abu Dhabi zuwa Madina.
Tawagar gwamnatin Tinubu ta halarci jana'iza
Wakilan Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin ministan tsaro, Abubakar Badaru sun halarci jana’izar a birni mai tsarki na Musulunci.
Tawagar ta bar Najeriya ne a daren ranar Lahadi, inda suka isa Madina da safiyar ranar Litinin da ta gabata.
Sauran ƴan tawagar sun haɗa da Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Ƙasa, Lateef Fagbemi, SAN da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Alhaji Mohammed Idris.
Sai kuma ƙaramin ministan harkokin gidaje da raya birane, Yusuf Abdullahi Ata; da kuma Daraktan Tsaron Cikin Gida na Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (ONSA), Hassan Abdullahi, wanda ya wakilci NSA.
Malaman da suka je jana'izar Aminu Ɗantata
Manyan malamai Musulmi na cikin tawagar sune Dr. Bashir Aliyu Umar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, da Khalifa Abdullahi Muhammad, limamin Masallacin Dantata da ke Abuja.
Jami’an ofishin jakadancin Najeriya da ke Jeddah, ƙarƙashin jagorancin Ambasada Ibrahim Moddibbo, sun halarci jana’izar, tare da Ambasada Muazzam Ibrahim Nayaya.
Sauran manyan suka halarta sun haɗa da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin da tsohon Shugaban jam’iyyar APC, Dr. Abdullahi Ganduje.

Asali: Twitter
Tawagar gwamnatin Kano ta halarci jana'izar Dantata
Haka nan kuma Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi tare da tawagarsu sun halarci jana'izar a Madinah.
Alhaji Aliko Dangote ne ya jagoranci sauran ’yan uwa da iyalan mamacin zuwa wurin jana'izar wadda ita ce gata na ƙarshe ga marigayin.
Sarkin Kano na 16, Muhammad Sanusi II, da Sarki na 15, Aminu Ado Bayero suma sun halarci jana’izar, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.
Tinubu da Atiku sun yi alhinin rasuwar Ɗantata
A wani labarin, kun ji cewa shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya bayyana rasuwar Alhaji Aminu Dantata a matsayin babban rashi ga ƙasa, yana mai miƙa ta'aziyya ga iyalansa.
Shugaba Tinubu ya ce Dantata ba wai kawai babban ɗan kasuwa ba ne, har ma dattijo ne da ya kasance ginshikin zaman lafiya da cigaba a Najeriya.
Haka zalika, Atiku Abubakar ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan Dantata, fadar masarautar Kano da kuma daukacin al’ummar Najeriya, yana mai roƙon Allah ya jikansa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng