Mahaifiyar Ministar Tinubu, Hannatu Musa Musawa Ta Riga Mu Gidan Gaskiya
- Iyalan Ministar Fasaha, Al’adu da Yawon Bude Ido sun sanar da rasuwar mahaifiyarta Hajiya Fatima Ladi Binta Musa Musawa bayan fama da jinya
- Sanarwar da ministar Hannatu Musawa ta bayyana ta ce za a gudanar da sallar jana’iza a Babban Masallacin Kasa Abuja
- Za a birne marigayiyar a makabartar Gudu bayan kammala jana’iza, inda aka gayyaci ’yan uwa, abokai da musulmi domin yi mata addu’o’i da rokon gafara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Iyalan minista, Hannatu Musa Musawa a Najeriya sun sanar da rasuwar mahaifyarta wacce ta bar duniya bayan fama da jinya.
Hajiya Fatima Ladi Binta Musa Musawa wadda ita ce mahaifiyar ministar Fasaha, Al’adu, Yawon Bude Ido ta Najeriya ta rasu a Abuja.

Source: Facebook
Hakan na cikin wani rubutu da Ministar ministar Fasaha, Al’adu, Yawon Bude Ido, Hannatu Musa Musawa ta yi a X.

Kara karanta wannan
Mutuwa ga girgiza sarakunan Najeriya, Osi Balogun ya riga mu gidan gaskiya a Ibadan
Yaushe ne sallar jana'izar marigayiyar
Hannatu Musa Musawa ta bayyana cewa za a gudanar da sallar jana’izarta a Babban Masallacin Kasa da ke Abuja bayan sallar Azahar da misalin karfe 1:30pm.
A cewar sanarwar, za a birne marigayiyar a makabartar Gudu bayan kammala jana’iza a birnin Abuja tare da addu’o’i da karramawa nan
An gayyaci ’yan uwa abokai da ’yan uwa musulmi domin halartar sallar jana’iza da yi mata addu’a ga marigayiya Allah da neman gafara Ameen
Ta kuma yi addu’ar Allah ya ji kan ta kuma ya gafarta mata tare da rokon Allah ya ba ta Aljannatul Firdaus Ameen Ameen.

Source: Facebook
Yadda al'umma ke yi wa marigayiya addu'a
Rasuwar Hajiya Fatima ta jawo ta’aziyya daga masu jaje da dama a fadin Najeriya inda suke ci gaba da addu’a ga iyalan Musawa kwarai
Sanarwar iyalan ta roki Allah Madaukaki ya gafarta mata ya kuma yi mata rahama tare da ba ta Aljannatul Firdaus.
Rasuwar ta kuma jawo sakonnin ta’aziyya daga mutane daban-daban da abokai da masoya a fadin kasar inda ake ci gaba da addu’a da jaje
Mutane da dama sun yi adduar Allah ya jikanta da rahama ya kuma sanya ta gidan aljanna firdausi madaukakiya.
Iyalan marigayiyar suna ci gaba da karbar ta’aziyya daga jama’a da dama tare da addu’o’i ga marigayiyar domin roka mata Allah ya saka mata da gidan aljanna.
Manjo Janar Rabe Abubakar ya mutu
Mun ba ku labarin cewa rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa tsohon Manjo Janar na rundunar sojojin Najeriya, Rabe Abubakar (mai ritaya) ya riga mu gidan gaskiya a hannun ƴan bindiga.
Gwamnatin Katsina ta tabbatar da rasuwar tsohon sojan wanda aka ce ya rasu ne yayin da yake tsare a hannun ‘yan bindiga sakamakon matsalolin ciwon sukari da hawan jini.
Gwamna Dikko Radda ya bayyana lamarin a matsayin babban rashi ga jihar Katsina da Najeriya baki daya yayin da ake ci gaba da fuskantar hare-hare a Arewacin kasar.
Asali: Legit.ng
