Kisan Danbokolo: Abin da Al'umma Suka Shirya saboda Tsoron Abin da Kai Iya Biyo Baya
- Mutane a Arewa maso Yamma na shirin ramuwar gayya bayan kashe shugaban ’yan bindiga Yellow Danbokolo da dakarun DSS suka jagoranta
- Matasa da mazauna garuruwa irinsu Shinkafi da Jibia sun ce sun ji daɗin mutuwar Bokolo, kuma sun fara ɗaukar matakan kare kansu
- Jami’an tsaro sun ƙarfafa farmaki a Zamfara, yayin da wasu ke zargin Turji yana neman hanyar mika wuya sakamakon rasa manyan mayaƙansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - Biyo bayan kashe shugaban ’yan bindiga Yellow Danbokolo, wasu yan gari suna shirye-shiryen jiran ko ta kwana.
Matasa da mazauna yankin Arewa maso Yamma sun fara shirin kare kansu daga ramuwar gayya daga mabiyansa.

Asali: Facebook
Yadda aka hallaka Kachallah Danbokolo
Punch ta gano cewa kisan Bokolo, wanda babban kwamanda ne a cikin cibiyar ta’addanci ta Bello Turji, ya ƙarfafa mutane su kafa kungiyoyin tsaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bokolo wanda aka ce ya jagoranci hare-hare da dama kuma yana da iko a dazuka, an kashe shi a ranar 29 ga Yuni tare da mayaƙa 200.
Kisan nasa da wasu hare-hare da aka kai kan ’yan bindiga sun girgiza cibiyar Turji, tare da rage haɗin gwiwa tsakaninsu a yankin.
Wani mazaunin Shinkafi, Sani Ibrahim, ya ce suna shirye su yaƙi Bello Turji da mutanensa idan sun zo ɗaukar fansa saboda mutuwar Bokolo.
Ya ce:
“Mun shirya mu yaƙi Turji da mayakansa da za su iya shigowa domin ɗaukar fansar ɗan’uwansu, Bokolo."
Ibrahim ya ce mazauna yankin suna murna da kisan Bokolo, yana mai cewa “Bokolo ya fi Turji muni. Shi ne uban Turji ba mabiyinsa ba.
Matsayar wasu yan Katsina kan kisan Danbokolo
Mazauna Jibia da Batsari a Katsina sun ce ba su cikin damuwa da yiwuwar harin ramuwar gayya, duk da kusancinsu da sansanin Turji, cewar Premium Times.
Shugaban matasa, Umar Labaran, ya ce mutanen yankin sun karɓi labarin mutuwar Bokolo da farin ciki saboda munin laifinsa da kuma hare-harensa.
Ya danganta zaman lafiya da haɗin gwiwar jami’an tsaro da Audu Lankai, wani tsohon shugaban ’yan bindiga da ke yawan sintiri da mutanensa.

Asali: Facebook
Hukumomi sun kara shiri a Zamfara
A Zamfara kuwa, hukumomi sun ƙara kaimi wajen ragargazar ragowar mayaƙan Turji a ƙaramar hukumar Shinkafi, bayan kisan Danbokolo.
Mai taimakawa Gwamna Dauda Lawal a kan hulɗa da jama’a, Mustafa Kaura, ya ce sun katse sadarwar wayar hannu a Shinkafi don datse hanyar sadarwar ’yan bindiga.
“Tun bayan mutuwar Bokolo, an tura karin jami’an tsaro. An yanke hanyoyin sadarwa don hana samun bayanai daga leƙan asiri."
- In ji Kaura
Ya ce ana ci gaba da binciken gida-gida don kama masu ba da mafaka ga ’yan ta’adda da masu haɗin gwiwa da su a yankin Shinkafi.
Ya ce:
“Wannan yaƙi ne na gaskiya da Turji da sauran ’yan ta’adda. Har yanzu ana ganin sakamako mai kyau."
Ya ce babu tattaunawa da masu ta’addanci, Gwamna Lawal ya bayyana cewa ba za a sake yin sulhu da ’yan ta’adda ba har abada.
Turji na neman sulhu bayan kisan Danbokolo
Kun ji cewa majiyoyi sun bayyana cewa Bello Turji yana neman a yi sulhu bayan mutuwar dan uwansa kuma kwamandansa.
An ce Turji na shirin ganawa da wasu kungiyoyin 'yan bindiga domin duba yuwuwar mika wuya ga gwamnatocin jihohin Arewa maso Yamma.
Wata majiya ta ce, Turji ba ya da karfi yanzu, Kachalla Danbokolo ne ke tafiyar da ayyukan fada da kayayyaki a daji.
Asali: Legit.ng