Bukukuwan aure a ƙasar Hausa tare da yadda ake gudanar da su

Bukukuwan aure a ƙasar Hausa tare da yadda ake gudanar da su

Aure wani muhimmin abu ne a cikin rayuwar kowace al'umma, domin dashi ake kafa zuri'a mai ƙarfi kuma a tabbatar da kyakkyawan tushe.

Wani ango kenan da galleliyar amarya sa a kasar hausa
Wani ango kenan da galleliyar amarya sa a kasar hausa

A kowace irin al'umma ta duniya, alaƙar rayuwa ko ta zama tsakanin mace da namiji ba ta samun karbuwa sai ta zama harsashin ta an gina sa ne bisa aure. Kuma tun kafin bayyanar kowane addini kowace al'umma take gudanar da harkokin auratayya bisa manufa da kuma tsarin da ta ga ya dace da ita.

Al'ummar hausawa kamar sauran al'ummomi suna da nasu tsarin da manufa wajen gudanar da harkokin auratayya a tsakanin su. Wannan kuwa a cakude yake da hanyoyin su na gargajiya da kuma wanda suka samu a tafarkin addinin musulunci.

Ganin yadda matsayin aure yake a musulunci da al'adar hausawa, jaridar Legit.ng ta ga yana da kyau a sami wani abin karantawa game da sha'anin aure a ƙasar hausa.

Yadda ake aure a kasar hausa

Saboda muhimmancin da hausawa suka baiwa aure, akwai matakai daban-daban da ake bi kafin akai ga daurin aure. Wannan matakai sun hadar da; zance, toshi, na gani ina so, kayan jin kira, barka da shan ruwa, toshin sallah, gasa, nuna soyayya, fitowa, bincike, baiko, ada'a, sa rana, tsarince, kayan lefe, sadaki sai kuma daurin aure.

Idan ranar daurin aure ta rage sauran 'yan kwanaki, sai iyaye da dangin kowane bangare su shiga sanar da jama'a daurin 'ya'yan su ta hanyar raba alewa da goron gayyata, ko kuma yin shela. Da yake zamani ya kan kawo sauye-sauye, akan aika da kati ko kuma sanarwa ta hanyar kafofin watsa labarai na zamani.

KARANTA KUMA: Kayatattun kalar rawar gargajiya 4 a kasar Hausa

Daurin aure shine mataki na ƙarshe wanda za a dauki amarya zuwa gidan mijin ta tare da wata tsohuwa da zata zauna da ita zuwa wasu 'yan kwanaki ƙalilan.

Shagulgulan bikin aure sun hadar da; amarci, gudu, kamu, zaman lalle, ƙunshi, jere, zarewa, yini, budar kai, zaman daki, angonci, kamun ango, alibidi, hawan angonci, sayen baki, tasa-ni, sai kuma gara.

Da zarar an kammala wannan shagulgula, shikenan sai a bar amarya da ango a gidan su na aure domin ci gaba da rayuwa tare zaman hakuri da juna da kuma samun zuri'a wadda har sai dai rai yayi halin sa kamar yadda kowa ke muradi.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, akwai ƙayattatun kaloli na rawaye-rawaye a al'adun hausa, wanda a cikin su ake aiwatar a yayin shagulgulan bikin aure.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: