Ranar Dimokuraɗiyya: Tinubu Ya ba BUK da Jami'o'i 2 Kyautar Motocin CNG a Kano

Ranar Dimokuraɗiyya: Tinubu Ya ba BUK da Jami'o'i 2 Kyautar Motocin CNG a Kano

  • Daliban jami’o’i uku da ke Kano sun karɓi motocin bas masu amfani da CNG daga Gwamnatin Tarayya a bikin Ranar Dimokuraɗiyya
  • Gwamnatin Bola Tinubu ta ce shirin zai rage wa ɗalibai wahalar sufuri tare da ƙarfafa amfani da makamashi mai tsafta a Najeriya.
  • Hukumar NELFUND da shirin PI-CNG sun jagoranci rabon motocin ga ƙungiyoyin ɗaliban jami’o’in BUK, NWU da YUMSFUE a Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kano - Daliban jami’o’i uku da ke jihar Kano sun karɓi kyautar sabbin motocin bas masu amfani da iskar gas ta CNG daga Gwamnatin Tarayya domin rage musu matsalolin sufuri.

Jami’o’in da suka amfana sun haɗa da Jami’ar Bayero Kano, Northwest University Kano da Yusuf Maitama Sule Federal University of Education.

Gwamnatin tarayya ta raba wa daliban jami'o'i uku a Kano motocin CNG.
Motoci masu amfani da CNG da gwamnatin tarayya ta raba wa daliban jami'o'i uku a Kano. Hoto: Abdulaziz Abdulaziz
Source: UGC

An raba motocin CNG ga jami'o'i 3 a Kano

Kara karanta wannan

Rai ya baci: Gwamna zai kori hadiman shi da suka ki shiga APC cikin sa'o'i 48

An gudanar da rabon motocin ne a harabar Jami’ar Bayero Kano yayin bukukuwan Ranar Dimokuraɗiyya, kamar yadda Premier Radio ta ruwaito.

Ofishin kula da ayyukan gwamnatin tarayya a Arewacin Najeriya tare da Hukumar Bayar da Lamunin Karatu ta NELFUND da shirin shugaban ƙasa na PI-CNG ne suka jagoranci rabon motocin.

An bayyana cewa shirin na daga cikin matakan da gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke ɗauka domin tallafa wa ɗalibai da rage musu nauyin kuɗaɗen sufuri.

Haka kuma gwamnati ta ce shirin zai taimaka wajen ƙarfafa amfani da makamashi mai tsafta a harkokin zirga-zirga.

Abdulaziz ya yaba da shirin gwamnatin Tinubu

Mai ba Tinubu shawara kan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Abdulaziz Abdulaziz, ya yaba da shirin yayin bikin.

A zantawarsa da 'yan jarida, Abdulaziz ya bayyana cewa rabon motocin wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatin Tinubu na tallafa wa ilimi da kuma inganta rayuwar ɗalibai a Najeriya.

Abdulaziz Abdulaziz ya kuma buƙaci ɗaliban da suka amfana da motocin su tabbatar sun yi amfani da su yadda ya kamata domin cimma manufar da aka samar da su.

Kara karanta wannan

Rikicin NDC: Abin da Kwankwaso da Seriake Dickson suka tattauna a zaman Abuja

An bukaci daliban da suka samu tallafin da su yi amfani da motocin yadda ya kamata.
Dalibai rike da fosta ta nuna godiya ga Shugaba Bola Tinubu bayan ba su kyautar motocin CNG. Hoto: Abdulaziz Abdulaziz
Source: UGC

An fara shirin tun kafin 12 ga Yuni

Tun makonni biyu da suka gabata, gwamnatin tarayya ta bayyana shirin rabon motocin CNG ga wasu jami’o’in Arewa domin rage matsalolin sufuri a cibiyoyin ilimi, in ji rahoton NTA News.

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsare-tsare, Hadiza Bala Usman, ta bayyana hakan a wani taron yini guda da aka shirya wa shugabannin ƙungiyoyin ɗalibai daga jami’o’i 19 na Arewa.

Gwamnatin Tinubu ta ce manufofinta a bangarorin ilimi, noma, lafiya da ababen more rayuwa sun fara kawo sauƙi ga ɗalibai musamman ta hanyar asusun lamunin karatu na NELFUND.

A cewar gwamnati, sama da ɗalibai miliyan ɗaya ne suka ci gajiyar shirin lamunin karatu, kuma adadin na ci gaba da ƙaruwa.

Gwamnati ta kaddamar da motocin CNG

A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamnati ta fara aiwatar da shirin motocin CNG da na lantarki a Kano domin rage kuɗin sufuri da bunƙasa amfani da makamashi mai tsafta.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya fusata kan rashin tsaro, ya ragargaji Tinubu

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce shirin zai taimaka wajen sauƙaƙa zirga-zirga, rage wahalar man fetur da kare muhalli a jihar Kano.

Hukumar PI-CNG & EV ta bayyana cewa an horar da sama da ‘yan Najeriya 7,000 tare da kafa cibiyoyin gyaran CNG 41 a sassan jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com