An Sako Tinubu a Gaba Ya Yi Murabus kafin 2027 kan Rashin Tsaro

An Sako Tinubu a Gaba Ya Yi Murabus kafin 2027 kan Rashin Tsaro

  • Sanata Dino Melaye ya soki jawabin ranar dimokuraɗiyya da hugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar a ranar Juma’a, 12 ga Yunin 2026
  • Melaye ya yi magana yana mai bayyana jawabin shugaban kasar a matsayin wanda bai yi daidai da halin da ‘yan Najeriya ke ciki ba
  • Tsohon ɗan majalisar ya kuma yi kira ga shugaban ƙasar da ya yi murabus saboda tabarbarewar tsaro da ƙaruwar sace-sacen mutane

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon Sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya yi murabus.

Ya ce jawabin da Bola Tinubu ya gabatar a ranar dimokuraɗiyya bai nuna gaskiyar matsalolin tsaro da ƙuncin tattalin arziki da ‘yan Najeriya ke fuskanta ba.

Kara karanta wannan

Tinubu zai kashe Naira tiriliyan 5 kan tsaro, za a dauki sababbin ƴan sanda 50000

Shugaba Bola Tinubu da Sanata Dino Melaye
Shugaba Bola Tinubu a hagu, Sanata Dino Melaye a dama. Hoto: Bayo Onanuga|Dino Melaye
Source: Facebook

Vanguard ta wallafa cewa Melaye ya bayyana hakan ne a Abuja yayin taron tunawa da marigayi Raymond Dokpesi da kungiyar D-37 da ta ƙunshi abokan hulɗar siyasar Dokpesi ta shirya.

Dino Melaye ya soki jawabin Bola Tinubu

Tsohon ɗan majalisa, Dino Melaye ya ce jawabin Tinubu na ranar 12 ga Yuni bai bayyana ainihin ƙalubalen da talakawan Najeriya ke fuskanta ba.

“Ina da matsala da dukkan sassan jawabin Tinubu na ranar 12 ga Yuni saboda bai nuna gaskiya ba.
"Alƙaluman da aka gabatar ba daidai ba ne, manufar ba ta da sahihanci, kuma dukkan sassan jawabin sun saɓa da abin da ‘yan Najeriya ke fuskanta a zahiri.,”

In ji Melaye.

Ya kawo misalan wasu hare-haren rashin tsaro da aka ruwaito a jihar Kogi da kuma sace-sacen ɗalibai a matsayin hujjar cewa matsalolin tsaro suna ƙara ta’azzara a ƙasar.

A cewarsa, ya kamata gwamnatin tarayya ta ɗauki matsalar tsaro a matsayin dokar ta-baci ta ƙasa tare da nuna ƙwarewa da ƙarfi wajen magance ta.

Kara karanta wannan

June 12: Tinubu ya ce a caccake shi, amma ya fadi abin da ba ya so a yi

Melaye ya nemi Tinubu ya sauka

Jigon jam’iyyar ADC ya yi nuni da sashe na 14(2)(b) na kundin tsarin mulkin Najeriya, wanda ya tanadi cewa tsaro da walwalar jama’a ne ya kamata su zama manyan abin da gwamnati za ta yi.

Punch ta rahoto ya ce:

“Duk wani shugaba da ya gaza a fannin tsaro da walwala shugaban ƙasa ne da ya gaza. Najeriya ba Legas ba ce. Matsalolin sun fi ƙarfinsa kuma ba shi da ƙarfin jagorantar wannan ƙasa,”

Ya ƙara da cewa duk da cewa ba ya goyon bayan biyan kuɗin fansa ga masu garkuwa da mutane, dole ne gwamnati ta nuna cewa tana da ikon kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

“Idan ba za ka iya yin hakan ba, ya kamata ka yi murabus cikin mutunci ka bar kujerar,”

In ji shi.

Sanata Dino Melaye na jihar Kogi
Sanata Dino Melaye na hira da 'yan jarida a Abuja. Hoto: Dino Melaye
Source: Facebook

‘Yan Najeriya na iya suka ta,' Tinubu

A wani labarin, mun kawo muku cewa Shugaba Bola Tinubu ya ce a shirye yake ya karɓi suka kan manufofi da ayyukan gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

'Tinubu ya dawo da zaman lafiya a wasu yankuna': Matawalle ya hango nasara a 2027

Ya bayyana hakan ne a jawabin da ya yi wa ƙasa baki ɗaya a ranar Juma’a, 12 ga watan Yunin 2026 domin bikin ranar dimokuraɗiyya ta bana.

Yayin da yake jawabi, Tinubu ya yi waiwaye kan tafiyar dimokuraɗiyyar Najeriya tun bayan dawowar mulkin farar hula a shekarar 1999.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng