Matashi Ya Yi wa Mahaifinsa Kisan Wulakanci da Sanda a Bauchi
- Wani matashi mai suna Limam Muhammad Baba ya kashe mahaifinsa Malam Baba Siti a kauyen Uzum, Bauchi
- Rahotanni sun bayyana cewa ya doke mahaifinsa da sanda a kai bayan wata gardama da suka yi a cikin gida
- Rundunar ’yan sandan jihar ta tabbatar da kama wanda ake zargin, kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - Wani mummunan lamari ya faru a kauyen Uzum da ke ƙaramar hukumar Giade a jihar Bauchi, inda wani matashi ya kashe mahaifinsa yayin wata gardama da suka yi.
Wanda ake zargi da aikata wannan ta’asa an bayyana shi da suna Limam Muhammad Baba, yayin da wanda aka kashe shi ne Malam Baba Siti, mahaifinsa matashin.

Asali: Facebook
Legit ta tattaro bayanai kan kisan ne a cikin wani sako da Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:15 na dare a ranar Alhamis, 3 ga watan Yuli 2025, inda gardamar da suka yi ta rikide zuwa tashin hankali, wanda ya kai ga dukan da ya zama ajalinsa.
Yadda matashi ya kashe mahaifinsa
Majiyoyi daga yankin sun cewa bayan gardamar da suka yi, Limam ya ɗauki sanda ya bugi mahaifinsa a kai, wanda hakan ya sa ya faɗi ƙasa ya suma nan take.
Bayan faruwar lamarin, aka kai rahoto ga ofishin ’yan sanda na Giade da misalin ƙarfe 10:30 na dare, inda aka ce an tabbatar da cewa Limam ya yi amfani da sanda wajen dukan mahaifinsa.
Wata majiya daga rundunar ’yan sanda ta ce ana samun rahoton, aka tura tawagar jami’an tsaro zuwa wurin da lamarin ya faru, inda aka kama wanda ake zargin.
Mahaifin ya rasu kafin a kai shi asibiti
Bayan kama Liman, aka garzaya da mahaifinsa zuwa Asibitin Gwamnati na Giade, amma likita ya tabbatar da cewa ya riga ya mutu kafin isarsu asibitin.
An ajjiye gawar mamacin a dakin ajiye gawa na asibitin yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da bincike kan dalilan da suka haifar da rikicin.
Wata majiya daga rundunar ’yan sanda ta bayyana cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.
Rundunar ’yan sanda ta yi martani kan kisan
Rundunar ’yan sanda ta jihar Bauchi ta bayyana cewa tana ɗaukar wannan lamari da matuƙar muhimmanci, kuma za a tabbatar da cewa an yi adalci.
Ta kuma shawarci al’umma da su guji rikicin cikin gida da kuma rungumar hanyoyin warware matsaloli cikin lumana da sanin ya kamata.

Asali: Twitter
An kama 'yan ta'adda 14 a jihar Benue
A wani rahoton, kun ji cewa jami'an tsaro sun yi nasarar dakile wasu miyagu a lokacin da su ke shirin kai hari a jihar Benue.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an kama mutum 14 cikin 'yan kungiyar wani dan ta'adda da ya dade yana addabar jihar.
Legit Hausa ta tabbatar da cewa jami'an tsaro na cigaba da bincike a yankin domin kama sauran bata gari da ke neman tada zaune tsaye.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng