Dan Majalisar Amurka mai Sukar Najeriya Ya Jinjina a Tinubu kan Dokar Ƴan Sandan Jihohi
- Dan majalisar dokokin Amurka, Riley Moore Wanda ya saka Najeriya a gaba ya yaba da matakin Bola Ahmed Tinubu kan tsaro
- Ya kuma jinjina wa Majalisar Wakilai kan kudirin ‘yan sandan jihohi wanda aka amince da shi a ranar Alhamis, 11 ga watan Yuni, 2026
- Riley Moore ya bayyana yadda dokar za ta taimamlka wa Najeriya wajen tabbatar da an kawo karshen rashin tsaro a sassa daban-daban
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Ƙasar Amurka – Ɗan majalisar dokokin Amurka, Riley Moore, ya yaba da matakin da Majalisar Wakilan Najeriya ta dauka na amincewa da kudirin kafa rundunar ‘yan sandan jihohi.
Moore ya bayyana cewa wannan mataki ne mai muhimmanci da zai taimaka wajen magance matsalolin rashin tsaro da kuma karfafa ikon gwamnatocin jihohi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummarsu.

Source: Twitter
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa a zaman majalisar da aka gudanar ranar Alhamis, 11 ga watan Yuni, 2026, ‘yan majalisar wakilai 289 sun kada kuri’ar amincewa da kudirin.
Kudirin na neman ba wa jihohi 36 damar kafa da gudanar da rundunonin ‘yan sandansu tare da hadin gwiwa da rundunar ‘yan sandan tarayya.
More ya gani gwamnatin Najeriya
Jaridar Punch ta wallafa cewa Moore ya bayyana goyon bayansa ga wannan mataki, inda ya ce ya dade yana kira da a ba jihohi karin iko wajen tunkarar matsalolin tsaro.
Ya kuma bayyana cewa ya taba tattauna batun kai tsaye da Uwargidan Shugaban Kasa yayin wata ziyara da ta kai birnin Washington, tare da sake jaddada bukatar ga wakilan Najeriya da ya rika ganawa da su.
Dan majalisar ya ce ba wa jihohi damar kare jama’arsu zai taimaka wajen rage matsalolin tsaro da ke addabar sassan kasar nan.
Haka kuma, ya yabawa Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa goyon bayan da ya nuna wa kudirin da kuma kokarin da ya yi wajen ganin an amince da shi a majalisar dokoki.
Akwai sauran aiki a gaba – Moore
Sai dai Moore ya bayyana cewa har yanzu akwai sauran matakai kafin a fara aiwatar da dokar a kasa baki daya domin a ci gajiyarta.
A cewarsa, dole ne Majalisar Dattawa ta amince da kudirin, sannan a samu amincewar akalla majalisun dokokin jihohi 24 kafin a mika shi ga shugaban kasa domin sanya hannu.

Source: Facebook
Ya kara da cewa amincewar Majalisar Wakilai alama ce da ke nuna cewa kokarin da aka shafe lokaci ana yi domin ganin an samar da ‘yan sandan jihohi yana fara haifar da sakamako.
Majalisa ta amince da dokar ƴan sandan jihohi
A baya, mun kawo labarin cewa Majalisar wakilai ta amince da kudirin kafa rundunar ‘yan sandan jihohi bayan kuri’ar da ‘yan majalisa 288 suka kada a ranar Alhamis.
Kudirin zai ba wa gwamnoni damar nada kwamishinonin ‘yan sanda tare da ba su umarni kan harkokin tsaro a matakin jihohinsu,.wanda ake sa ran zai taimaka matuka.
Sai dai, dole ne Majalisar dattawa da majalisun jihohi su fara amince wa da wannan kuduri kafin rundunar ‘yan sandan jiha ta fara aiki a dukkanin jihohin Najeriya.
Asali: Legit.ng

