Mariya Sunusi Dantata: Matar da ta zama baya goya marayu a kaf fadin Afirka wajen ciyar da mabukata

Mariya Sunusi Dantata: Matar da ta zama baya goya marayu a kaf fadin Afirka wajen ciyar da mabukata

- Mutane da yawan gaske basu san wacece Hajiya Mariya Sunusi Dantata ba, kawai dai sunan suke ji

- Hajiya Mariya ita ce dai mahaifiya ga hamshakin mai kudin nan na daya a nahiyar Afirka, Alhaji Aliko Dangote

- An bayyana cewa Hajiya Mariya ba ta da aiki da ya wuce taimakon marayu da marasa karfi a fadin jihar Kano da kewaye

Mutane da yawa basu san ko wacece Mariya Sunusi Dantata ba, suna kawai kallon ta ne a matsayin mahafiya ga hamshakin mai kudin Afirka Alhaji Aliko Dangote.

Sunan da ake yi mata lakabi da shine, Uwar Marayu da marasa gata, idan kaje kofar gidanta kaga yadda ake ciyar da marayu da marasa karfi abin kamar wasan kwaikwayo.

Gidan Hajiya Mariya ya zama wata inuwa wacce talakawa ke zuwa su huta, sannan ta zama tamkar katanga ga al'umma wacce suke jingina a jikinta su samu saukin rayuwa.

KU KARANTA: Tirkashi: A wannan karon Zahra Buhari ta zo da wata zazzafar magana

Anyi hasashen cewa talakawa sama da dubu hamsin suna cin abinci daga safe zuwa dare a kullum a gidan Hajiya Mariya, saboda da yawa daga cikinsu basu da wata hanyar samun abinci sai a gidanta.

Kullum dafa abinci ake yi a gidan Hajiya Mariya kala daban-daban, na asibiti daban, na gidan nakasassu daban, na sauran al'ummar gari daban.

An bayyana cewa Hajiya Mariya tana da ma'aikata wadanda take biya albashi sama da dubu a karkashinta, wadanda ta dauke su aikine kawai saboda ta dinga ciyar da al'ummar Annabi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel