Dan Bindiga Ya kai Hari Amurka ana Gasar Kofin Duniya a Kasar

Dan Bindiga Ya kai Hari Amurka ana Gasar Kofin Duniya a Kasar

  • Rahotanni sun nuna cewa an kai hari ranar Juma’a a jihar Texas a Amurka, aka kashe mutum ɗaya tare da jikkata wasu da aka kai asibiti
  • An ce wanda ya yi harbin ya yi fito-na-fito da jami’an tsaro na kusan sa’o’i biyu, amma daga bisani ya mutu yammacin ranar Juma’a
  • Hakan na zuwa ne yayin da kasar Amurka ta karbi bakuncin gasar cin kofin duniya na 2026, inda kasashe da dama su taru a jihohinta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Aƙalla mutum ɗaya ya mutu yayin da wasu tara ke kwance a asibiti bayan wani harbe-harbe da ya faru a Texas, kamar yadda jami’ai suka bayyana a ranar Juma’a.

Da farko ‘yan sanda sun yi na fito-na-fito da wanda ake zargi da harbin, amma daga bisani suka ce ya mutu da yammacin ranar Juma’a a Midland, wani gari da ke yammacin Texas mai nisan kusan mil 330 (kilomita 530) daga Dallas.

Kara karanta wannan

Duniya za ta huta: Trump ya ce yaki da Iran ya zo karshe, babu sauran kai hari

Wajen da aka kai hari a Amurka
Jami'an tsaro sun ajiye mota a wajen da aka kai hari a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

'Dan bindiga ya yi barna a Amurka

BBC ta wallafa cewa Jami’an yankin da abin ya faru sun ce adadin waɗanda lamarin ya shafa ya kai 11, ciki har da wanda ya mutu.

Asibitin Midland Memorial ya ce ya karɓi mutum tara da suka jikkata, kuma huɗu daga cikinsu suna cikin dakin tiyata. Wani mutum kuma an kai shi Asibitin Odessa.

“Zuciyata ta yi rauni saboda waɗanda abin ya shafa da iyalansu,”

In ji Magajin Garin Midland, Lori Blong.

Ta kara da cewa:

“Muna addu’a ga kowane mutum da wannan lamari ya shafa a yau, da kuma jami’an tsaro da suka saka rayukansu cikin haɗari domin kare al’ummarmu,”

Blong ta ce jami’ai sun samu kiran farko game da harbe-harben da ƙarfe 8:03 na safe agogon yankin kuma nan take suka isa wurin.

Yadda aka bude wuta a Amurka

Rahotanni sun nuna cewa tsawon kusan sa’o’i biyu aka yi wanda ake zargi yana harbe-harbe yayin fito-na-fito da jami’an tsaro.

Kara karanta wannan

Yakin Iran: Amurka ta jefa makamai, an hallaka jami'an kasar Indiya

The Guardian ta ruwaito cewa ‘yan sanda sun ce lamarin ya fara ne a wani ɓangare na birnin kafin ya kai kusa da wani asibitin dabbobi a wani yanki daban.

Andrea Mendias, wadda ke aiki a wani wurin gyaran motoci kusa da asibitin dabbobin, ta shaida cewa ta ji kamar an harba bindiga fiye da sau 40.

Jim kaɗan bayan haka, rundunar ‘yan sandan Midland ta sanar da cewa an kawo ƙarshen harbe-harben, kuma an tabbatar da mutuwar wanda ake zargi.

Cikin wajen da aka kai hari a Amurka
Kowa ya watse a wajen da aka kai hari a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Trump ya cinma matsaya da Iran

A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Donald Trump ya ce an cimma yarjejeniya da kasar Iran bayan shafe watanni ana kai ruwa rana.

Bugu da kari, shugaban kasar ya bayyana cewa za a iya sanya hannu a kan yarjejeniyar a ƙarshen wannan makon, mai yiwuwa a Turai.

Hakan na zuwa ne bayan Trump ya dakatar da hare-haren soji kan Iran, sa’o’i kaɗan bayan ya yi barazanar ƙara tsananta yaƙin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng