Tuna Baya: Dantata Ya Fadi yadda Ya ke Fata Ya Cika da Imani kafin Rasuwarsa

Tuna Baya: Dantata Ya Fadi yadda Ya ke Fata Ya Cika da Imani kafin Rasuwarsa

  • Kafin rasuwar shi, Aminu Alhassan Dantata ya taba bayyana cewa ba ya jin daɗin rayuwa kuma yana fatan barin duniya cikin salama
  • Aminu Alhassan Dantata ya bayyana haka ne yana da shekaru 91, lokacin da Kashim Shettima ya kai masa ziyara a jihar Kano
  • A lokacin hirar da ya yi, fitaccen dan kasuwar ya ce da wuya ya tuna mutane 10 da ya saba da su a rayuwarsa da ke raye a yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja Tsohon ɗan kasuwa kuma dattijon ƙasa, Aminu Alhassan Dantata, wanda aka sanar da rasuwarsa ranar Asabar yana da shekaru 94, ya taɓa bayyana cewa ya gaji da rayuwa.

A lokacin rayuwar shi, Dantata ya bayyana cewa a lokacin yana jiran tafiyarsa zuwa ga Mahaliccinsa ne cikin salama.

Alhaji Aminu Dantata da ya rasu yana da shekara 91
Alhaji Aminu Dantata da ya rasu yana da shekara 94. Hoto: Hassan Mohammed
Asali: Twitter

Daily Trust ta wallafa cewa ya fadi haka ne a wata zantawa da ya yi da mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, kimanin shekaru biyu da rabi da suka wuce.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ina jiran lokaci, na gaji da rayuwa,” Dantata

A lokacin, Dantata ya bayyana cewa rayuwa ta fara gundurar sa, yana kuma fatan barin duniya cikin yarda da Allah.

Dantata ya ce:

“Gaskiya, yadda nake a yanzu, ina jiran lokacina. Ba na wani jin jin daɗin rayuwa. Ina fatan zan tafi lahira cikin yarda da Allah.”

Ya ƙara da cewa:

“Ina fatan ban cutar da kowa ba a rayuwa ta. Idan na bata wa wani rai, ina roƙon yafiyar shi. Idan wani ya bata mani rai, na yafe masa.”

A wancan lokacin, Dantata ya bayyana cewa shi kaɗai ya rage daga cikin abokansa, yana rayuwa da jikokinsa ne kawai.

Yaushe Aminu Dantata ya yi jawabin?

Marigayi Dantata ya yi maganar ne a lokacin ziyarar da Kashim Shettima ya kai masa a gidansa da ke Kano.

Dantata ya nuna farin ciki da godiya bisa wannan ziyara, yana mai roƙon zaman lafiya da daidaituwar lamura a Najeriya.

Ya ce:

“Allah kada ya bar mu da ƙoƙarinmu kadai. Muna roƙon shiriyarsa da kariyarsa a garemu da ƙasarmu baki ɗaya.”

Ziyarar ta kasance wani bangare na shirin tuntubar manyan dattawan Arewa da Shettima ya yi gabanin zaɓen 2023.

Gwamnan Kano na wancan lokacin, Abdullahi Umar Ganduje, da wasu fitattun mutane irinsu Musa Gwadabe, Janar Lawal Jafaru Isa da Tanko Yakasai ne suka raka Shettima gidan Dantata.

Gwamnatin Kano ta yi ta'aziyyar Dantata

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi ta'aziyyar rasuwar, Dantata jim kadan bayar sanar da mutuwar shi.

Abba Kabiir ya yi ta'aziyyar rasuwar Dantata
Abba Kabiir ya yi ta'aziyyar rasuwar Dantata. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

Legit ta gano cewa mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya fitar da sakon a shafinsa na Facebook.

Malami ya koka kan rashin girmama Dantata

A wani rahoton, kun ji cewa malamin addini a Kano, Sheikh Lawan Abubakar Shu'aib Triumph ya koka kan abin da ya kira rashin girmama Alhaji Aminu Dantata.

Sheikh Lawan Abubakar Shu'aib Triumph ya ce wasu da suka yi bikin sallah a cikin tawagar wani sarki ne suka nuna rashin dattaku wa Dantata.

Malamin ya yi kira ga al'umma da su rika girmama manyan mutane, musamman wadanda suka bayar da gudumwa ga jama'a sosai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng