'Ku Kai Zuciya Nesa': Kashim Shettima Ya Shawarci Iyalan Dantata kan Rabon Gado

'Ku Kai Zuciya Nesa': Kashim Shettima Ya Shawarci Iyalan Dantata kan Rabon Gado

  • Sanata Kashim Shettima ya kai gaisuwar ta’aziyya ga dangin marigayi Aminu Dantata a madadin Shugaba Bola Tinubu
  • Mataimakin Shugaban Ƙasa ya ja hankalin dangin Dantata da su ci gaba da zama ɗaya, ka da dukiya ta jefa su cikin rigima da rikici
  • Ya ce mai dukiyar ya tafi, yake cewa wannan ya isa ya tuna mana cewa babu wani abu da ke dawwama a duniya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya kai ziyara domin ta'aziyya ga iyalan marigayi Alhaji Aminu Alhassan Dantata.

Sanata Shettima roƙi dangin marigayi dattijo kuma hamshaƙin ɗan kasuwa, Aminu Dantata, da su zauna lafiya cikin haɗin kai.

Kashim Shettima ya gargadi iyalan marigayi Dantata
Kashim Shettima ya shawarci iyalan Dantata kan rigima a gado. Hoto: Kashim Shettima.
Asali: Twitter

Kashim Shettima ya yi ta'azziyar rasuwar Dantata

Daily Trust ta ruwaito cewa Shettima ya fadi haka yayin gaisuwar ta’aziyya ga dangin Dantata a Kano, a madadin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ziyarar da Shettima ya kai na daga cikin jerin gaisuwar ta’aziyya da manyan mutane ke kaiwa dangin marigayin Dantata, wanda ya rasu yana da shekaru 94 a Abu Dhabi, kuma aka binne shi a birnin Madina da ke Saudiyya.

Mataimakin shugaban kasar ya bukaci iyalan su ci gaba da rike halaye na gaskiya, tawali’u da taimakon jama’a da suka bayyana rayuwar mahaifinsu.

Ya bayyana marigayin a matsayin “ginshiƙin ƙasa” wanda mutuwarsa babban rashi ce ba kawai ga danginsa ba, har ma ga ƙasar baki ɗaya.

Kashim Shettima ya kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan Dnatata
Kashim Shettima ya shawarci iyalan Dantata kan rabon gado. Hoto: Kashim Shettima.
Asali: UGC

Shawarar da Shettima ya ba iyalan Dantata

Kashim Shettima ya ja hankalin dangin da su ci gaba da zaman lafiya tare da kauce wa duk wata fitina da dukiyar da aka bari za ta iya haifarwa, cewar Punch.

Ya ce:

“Ina mai cewa mutuwar Alhaji Aminu Dantata ba ta tsaya a danginsa kaɗai ba, asara ce ga ƙasa gaba ɗaya.
Shi wata taska ce ta ƙasa, mutum ne da rayuwarsa ta kasance alheri ga ɗan’adam.

“Ina mai cewa mai dukiyar ya riga mu gidan gaskiya, wannan kaɗai ya isa ya tunatar da mu cewa babu wani abu da ke dawwama a duniya."

Ya kuma roƙi dangin Dantata da su ci gaba da kiyaye suna da dabi’un da suka shahara da su, yana mai jaddada cewa Dantata ya shahara wajen gaskiya, karamci da jajircewa wajen cigaban al’umma.

“Ku kiyaye sunan Dantata da mutuncin da yake ɗauke da shi. Ku ci gaba da rike haka domin a ci gaba da tunawa da shi ba kawai a danginku ba, har a faɗin ƙasa da ƙetare."

- Cewar Kashim Shettima

Tinubu ya kadu da rasuwar Dantata

Kun ji cewa shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayyana rasuwar Alhaji Aminu Dantata a matsayin babban rashi ga ƙasa, yana mai yabon gudummawarsa.

Dantata ya rasu yana da shekara 94, kuma ya kasance ɗaya daga cikin manyan ’yan kasuwa masu taimakon al'umma a Najeriya.

Tinubu bayyana Dantata a matsayin mutum mai kokarin kawo cigaba tare da mika ta’aziyya ga iyalansa da al’ummar Kano.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.