Zaɓen 2027: Peter Obi Ya Bayyana Abin da Zai Fara Yi game da Nnamdi Kanu

Zaɓen 2027: Peter Obi Ya Bayyana Abin da Zai Fara Yi game da Nnamdi Kanu

  • 'Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar adawa ta NDC, Peter Obi ya yi magana kan abubuwan da zai yi idan ya yi nasara a 2027
  • Ya bayyana haka ne a Washington yayin ganawa da ‘yan Najeriya, ya ce masu rike da mukami suna fuskantar zagi amma hakan bai kamata ya zama laifi ba
  • Obi ya kuma ce zai yi amfani da tattaunawa wajen magance masu fafutuka da sauran korafe-korafe a fadin kasar, yana ganin hakan ne mafita

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi ya bayyana muhimman abubuwan da zai yi idan ya ci zaben 2027 da ake tunkara.

Peter Obi ya ce zai saki Nnamdi Kanu idan aka zabe shi shugaban Najeriya a zaben shugaban kasa da za a yi a 2027.

Kara karanta wannan

Tinubu zai kashe Naira tiriliyan 5 kan tsaro, za a dauki sababbin ƴan sanda 50000

Obi ya magantu kan sakin Nnamdi Kanu bayan ya yi nasara
Dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi da mataimakinsa, Rabi'u Kwankwaso. Hoto: Mr. Peter Obi.
Source: Facebook

Peter Obi ya bayyana hakan ne yayin ganawa da ‘yan Najeriya da ke Washington, kamar yadda Punch ta tabbatar da a rahotonta.

Abin da Peter Obi zai tsunduma kansa

Ya kuma ce zai shiga tattaunawa da masu fafutukar ballewa da sauran masu korafe-korafe a fadin Najeriya domin fahimtar dalilansu da kuma warware matsaloli ta hanyar zaman lafiya.

Obi ya ce bai ga dalilin ci gaba da tsare Kanu ba saboda abin da ya aikata ba laifi ba ne a siyasance.

A cewarsa, Kanu ana zarginsa ne da kalamai da yake yi a gidan rediyon Radio Biafra, amma yana ganin cewa sukar shugabanni ko kiran sunaye bai kamata a dauka a matsayin laifi ba.

Ya ce:

“Babu wani dalili na ci gaba da tsare Nnamdi Kanu. Zan sake shi idan na zama shugaban kasa. Bai yi wani laifi ba.”
Peter Obi zai tattauna da masu shirin ballewa
Tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi a taro. Hoto: Mr. Peter Obi.
Source: Twitter

Yadda Obi zai tattauna da masu korafe-korafe

Obi ya kara da cewa ‘yan siyasa suna fuskantar zagi da kalamai iri-iri daga jama’a, amma hakan bai kamata ya zama abin hukunci ba a tsarin dimokuradiyya.

Kara karanta wannan

June 12: Tinubu ya ce a caccake shi, amma ya fadi abin da ba ya so a yi

Ya kuma jaddada cewa tattaunawa da fahimtar juna ne kadai hanyar warware matsalolin masu fafutuka da rikice-rikicen cikin gida a Najeriya.

A cewarsa:

"Duk wanda ke da korafi ya kamata a zauna da shi domin fahimtar abin da yake so da kuma nemo mafita ta lumana”.

Ya kuma jaddada cewa tattaunawa da fahimtar juna ne kadai hanyar warware matsalolin masu fafutuka da rikice-rikicen cikin gida a Najeriya, Daily Post.

Peter Obi wanda ya fito takarar shugaban ƙasa a NDC ya kasance daga yankin Kudu maso Gabashin Najeriya da Nnamdi Kanu wanda aka tura shi gidan kaso saboda ta'addanci.

Takarar Obi da Kwankwaso ta ƙara ƙarfi

Mun ba ku labarin cewa wata kungiyar Dattawan Igbo ta bayyana wanda za ta goyi baya a zaben shugaban kasa na shekarar 2027 da ake tunkara.

Dattawan sun yaba da tsarin tikitin takarar Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso na jam'iyyar NDC gabanin zaben 2027 da ke tafe nan da watanni kadan.

Rabi'u Kwankwaso ya yaba da kyakkyawar alakarsa da Obi, yana mai jaddada kudirin NDC na samun nasara a zabe mai zuwa wanda ake ganin zai yi zafi sosai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.