Matawalle Ya Tsage Gaskiya, Ya Ce Allah Kadai Zai Iya Magance Matsalar Tsaron Najeriya
- Karamin Ministan Tsaro na Ƙasa, Bello Matawalle, ya ce Allah ne kaɗai zai iya kawo ƙarshen matsalar tsaron da ke addabar Najeriya
- Ya buƙaci 'yan Najeriya su ci gaba da bai wa jami'an tsaro goyon baya tare da addu'o'in samun zaman lafiya mai dorewa
- Matawalle ya zargi wasu 'yan adawa da amfani da matsalar tsaro domin cimma manufofin siyasa yayin da ake tunkarar zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Ƙaramin Ministan Tsaro na Ƙasa, Bello Muhammad Matawalle, ya bayyana cewa Allah ne kaɗai ne zai iya kawo ƙarshen matsalolin rashin tsaro da ke addabar Najeriya.
Ministan ya ce matsalar tsaro ta shafi kowa da kowa ba tare da la'akari da jam'iyya ko addini ba, don haka ya kamata 'yan Najeriya su haɗa kai da jami'an tsaro domin kawo ƙarshenta.

Source: Facebook
Matawalle ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa, yayin da ake ci gaba da fuskantar hare-haren 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane a sassa daban-daban na ƙasar.
Bello Matawalle ya bukaci hadin kan jama'a
A cewarsa:
"Abin takaici ne matuƙa, kuma dole ne mu tashi tsaye domin tabbatar da cewa jami'an tsaro da 'yan Najeriya sun haɗa kai wajen kawo ƙarshen rashin tsaro a ƙasar nan.
"Rashin tsaro ba ya nuna bambanci tsakanin jam'iyya ko addini. Yana iya shafar kowa da kowa."
Ya ƙara da cewa babu wani ɗan Najeriya da ke farin ciki da abin da ke faruwa, amma wasu daga cikin 'yan adawa suna amfani da matsalar domin nuna gazawar gwamnati.
Ministan ya soki yan adawa a Najeriya
Matawalle ya ce wasu 'yan siyasa na yada bayanan da za su iya tayar da hankalin jama'a ta hanyar amfani da matsalar tsaro domin cimma muradun siyasa.

Kara karanta wannan
'Nigeria Air': EFCC ta tona yadda Ministan Buhari ya yaudari 'yan kasa da jirgin aro
"Mun roƙi 'yan adawa su daina amfani da matsalar tsaro wajen tunzura jama'a. Wasu daga cikinsu abin da ya fi damunsu shi ne su nuna gwamnati ta gaza domin cimma manufofinsu na siyasa."
"Allah kaɗai ne zai kawo ƙarshen wannan matsala ta tsaro, tare da addu'o'inmu da ƙoƙarin da muke yi gaba ɗaya. Bai kamata a yi amfani da shi wajen zargin juna ko neman maki na siyasa ba."
- In ji Bello Matawalle.

Source: Twitter
Matawalle yaba wa jami'an tsaro
Ministan ya tabbatar da cewa jami'an tsaro na ci gaba da aiki ba dare ba rana domin murƙushe 'yan ta'adda da masu tayar da ƙayar baya a sassan ƙasar.
A rahoton Daily Trust, Matawalle ya kara da cewa:
"Jami'an tsaronmu suna aiki tuƙuru a faɗin ƙasar nan. Mun ba su umarni su ɗauki matakan da suka dace kan masu ta'addanci. Amma wannan matsala ba abu ba ne da zai ƙare cikin dare ɗaya ba."
Janar Musa ya tona masu taimakon ta'addanci
A wani rahoton, kun ji cewa Ministan Tsaro, Christopher Musa, ya ce masu taimaka wa ‘yan ta’adda a cikin al’umma ne ke ƙarfafa ayyukan ta’addanci da garkuwa da mutane.
Ya ce masu bada bayanai da ake kira imfoma da masu ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga da masu tayar da ƙayar baya ne suka sa matsalar tsaro ta ci gaba da ƙamari a ƙasar.
Janar Musa Mai ritaya ya ce ba zai yiwu a kawo ƙarshen matsalolin tsaro ba idan har jama’a ba su ba jami’an tsaro cikakken haɗin kai da goyon baya ba.
Asali: Legit.ng

