Yaƴan Jagororin ADC da ke cikin Jam'iyyun APC da PDP a Yau

Yaƴan Jagororin ADC da ke cikin Jam'iyyun APC da PDP a Yau

Lere Olayinka, mai bai wa Ministan Abuja, Nyesom Wike, shawara kan harkokin sadarwa da kafafen sada zumunta, ya bayyana rashin amincewarsa da sahihancin ADC.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – A makon da ya gabata ne jagororin adawa suka amince da hadewa waje guda, ayi amfani da jam'iyyar ADC wajen abin da suka kira ceto Najeriya daga APC.

Jagororin ADC, Atiku, David Mark, Nasir El-Rufa'i
Wasu daga cikin jagororin ADC na ci gaba da zamansu a jam'iyyun adawa Hoto: Atiku Abubakar/ADC Coalition 2027/Nasir El-Rufa'i
Asali: Facebook

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, Olayinka ya caccaki jagororin, yana zargin cewa wasu daga cikin shugabannin ADC na da ‘ya’ya masu cin moriyar APC da PDP.

Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin yaran jiga-jigan da ke kawancen adawa da Bola Tinubu, da ke more gwamnatocin adawa da iyayensu ke kokarin kawar da su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Adamu: Dan Atiku a gwamnatin Fintiri

Gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya nada Adamu Atiku, babban yaron tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, a matsayin kwamishina.

A shekarar 2019, gwamnan ya tura jerin sunayen mutane 23 da ya ke so a tantance a matsayin kwamishinoni zuwa majalisar dokokin jihar.

Atiku Abubakar da dansa, Adamu Atiku
Adamu Atiku jigo ne a gwamnatin Adamawa Hoto: @Atiku, @AdamuAtikuA
Asali: Twitter

Shugaban majalisar, Aminu Iya-Abbas, ne ya karanta jerin sunayen, wanda daga bisani majalisar ta amince da nada karin masu ba gwamna shawara guda 40.

Adamu Atiku na rike da mukamin Kwamishinan Ayyuka da Ci gaban Harkokin Makamashi a jihar Adamawa.

Duk da rikicin siyasa tsakanin Atiku Abubakar da Gwamna Fintiri, ɗan gidan Waziri na Adamawa bai sauya sheka ko ajiye mukaminsa ba.

2. 'Dan tsohon gwamnan Kaduna yana APC

Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa Mohammed Bello El-Rufai, ɗan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana goyon bayansa ga APC.

Haka kuma zuwa yanzu ba a ga alamun yana adawa da Bola Tinubu wajen neman wa’adi na biyu ba, duk da cewa mahaifinsa ya bar jam’iyyar APC zuwa SDP a watan Maris 2025.

Bello El-Rufa'i, yaron Nasir El-Rufa'i
Bello El-Rufa'i ya goyi bayan Tinubu Hoto; Bello El-Rufa'i
Asali: Twitter

Bello El-Rufa'i dan majalisar wakilai ne da ke wakiltar mazabar Kaduna ta Arewa a majalisar tarayya.

An gan shi a babban taron jam’iyyar APC a Abuja, inda aka amince da Tinubu a matsayin dan takara daya tilo na jam’iyyar a zaben 2027.

Wannan lamari ya faru ne bayan mahaifinsa ya fice daga APC, yana mai cewa jam’iyyar ta kauce da daga abin da aka tsara na ceto al'umma.

3. Blessing Onuh: Diyar shugaban ADC tana APC

Blessing Onuh, ‘yar shugaban riko na sabuwar kawancen jam’iyyun adawa da aka kafa karkashin ADC, David Mark ta ki bin mahaifinta zuwa sabuwar jam’iyyarsa.

Onuh ‘yar majalisar wakilai ce da ke wakiltar mazabar Otukpo/Ohimini a jihar Binuwai. Ta sauya sheka daga jam’iyyar APGA zuwa APC a shekarar 2021.

Diyar David Mark ba ta bar APC ba
Diyar David Mark na ci gaba da zamanta a APC Hot: Warri People
Asali: Facebook

Ta lashe zaben a karkashin APGA, inda ta doke dan kawunta, Egli Johnson Ahubi, wanda ya tsaya takara karkashin PDP, daga baya sai ta koma APC.

Yadda masana ke kallon ADC

Yayin da wasu 'yan siyasa ke rububin ADC, amma manyan jagororinta da yaransu sun ci gaba da zama a jam’iyyunsu, masu sharhi sun fara tofa albarkacin baki kan tasirin kawancen adawa.

Farfesa Kamilu Sani Fagge, masanin siyasa daga Jami’ar Bayero da ke Kano, ya shaida wa majiyar Legiit a Kano cewa lokaci bai yi ba da za a iya yanke hukunci kan tasirin ADC ba.

Ya ce:

"A yanzu dai ba za a iya yanke hukunci a ce haɗakar ADC za ta yi ƙarfi ko ba za ta yi ba. Wannan zai dogara da yadda suka haɗu, da manufofin da suka fito da su, da kuma irin ’yan takarar da za su tsayar a matakai daban-daban."

Ya kara da cewa:

"Idan suka yi haka, za su iya samun nasara, kuma za su iya yin tasiri a siyasar Najeriya."

Ya ce ko da yake, har yanzu lokaci bai yi ba na hasashe a kan zabe mai zuwa ba, amma idan 'yan haɗakar suka dauki matakan da suka dace, za su iya girgiza siyasar Najeriya.

Sule Lamido ya magantu kan ADC

A baya, mun wallafa cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma jigo a PDP, Sule Lamido, ya yi maraba da duk wani yunkuri na haɗin gwiwa da zai kifar da APC.

Wannan bayani na Lamido na zuwa ne bayan an hango hotonsa tare da wasu fitattun ’yan siyasa da ke goyon bayan haɗakar jam’iyyar ADC gabanin zaben 2027.

Sule Lamido ya ce yana tare da sabuwar tafiyar ADC domin samar da wata sabuwar gwamnati da za ta ceto Najeriya daga halin da gwamnatin APC ta jefa ta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.