An Yi Rashi: Ɗan Majalisar Tarayya Mai Ci daga Jihar Gombe Ya Rasu Ranar Juma'a

An Yi Rashi: Ɗan Majalisar Tarayya Mai Ci daga Jihar Gombe Ya Rasu Ranar Juma'a

  • 'Dan majalisar wakilai mai wakiltar Gombe, Kwami da Funakaye, Hon. Yaya Bauchi Tongo ya rasu a wani asibiti da ke Abuja
  • Farfesa Isa Ali Pantami ya ce ya ziyarci marigayin a asibitin Nizamiye kafin daga bisani ya samu labarin rasuwarsa yau
  • 'Dan takarar gwamnan ya yi addu’ar Allah ya gafarta wa marigayin tare da bai wa iyalansa hakurin jure babban rashi da suka yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Mun samu rahoton cewa 'dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabun Gombe, Kwami da Funakaye, Yaya Bauchi Tongo ya rasu.

An bayyana cewa marigayin ya rasu ne ranar Juma’a, 12 ga watan Yunin 2026 a asibitin Nizamiye da ke Abuja bayan fama da rashin lafiya.

Dan majalisar wakilai daga Gombe, Yaya Bauchi Tongo ya rasu a Abuja.
Dan majalisar wakilai daga Gombe, Yaya Bauchi Tongo da ya rasu a Abuja. Hoto: @TrackaNG
Source: Twitter

Hon. Yaya Bauchi Tongo ya rasu

Isa Ali Ibrahim Pantami ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya nuna alhini kan rasuwar dan majalisar.

Kara karanta wannan

Janar Abdulsalam ya faɗi abin da ba a sani ba kan mutuwa fuju'a da Abiola ya yi

Ya ce:

"Mun rasa dan majalisar mu, wanda ke wakiltar Gombe, Kwami, da Funakaye, Hon. Yaya Bauchi Tongo. ya rasu ne a yau Juma'a, 12 ga Yuni, 2026."

Pantami ya ce ya kai ziyara ga marigayin tare da Alhaji Bappa Ahmad Abdullahi da wasu abokai a asibitin Nizamiye da ke Abuja kafin rasuwarsa.

Halin da Pantami ya ga dan majalisar

Ya ce a ranar ya kasance tare da marigayin daga karfe 3:30 zuwa 3:50 na yamma, inda ya yi masa addu’o'i, sannan ya gana da abokin marigayin da ‘ya’yansa biyu da sauran ‘yan uwansa a asibitin.

A cewarsa, yanayin da ya ga dan majalisar a ciki ya tayar masa da hankali matuka saboda rashin lafiyar ta yi matukar tsanani.

“Tun bayan da na bar asibitin, na shiga damuwa saboda yanayin rashin lafiyar da na gani. Amma duk da haka mun dogara ga Allah Madaukakin Sarki,” in ji Pantami.

Pantami ya yi addu’a ga marigayin

Kara karanta wannan

'Dan takarar gwamnan Bauchi zai gamu da cikas da PDP ta taso shi a gaba

Tsohon ministan ya ce bayan wasu sa’o’i kadan da barinsa asibitin ne ya samu labarin rasuwar Hon. Yaya Bauchi Tongo.

Pantami ya ce:

"Bayan wasu 'yan awanni, na samu labarin rasuwarsa a asibitin Nizamiye, Abuja, a yau Juma'a. Mun rasa dan uwanmu. Sai dai, muna da yakinin cewa zai samu rahamar Allah saboda ya rasu ranar Juma'a."
Pantami ya yi ta'aziyyar rasuwar Yaya Bauchi, Dan majalisar Gombe da ya rasu a Abuja.
Farfesa Isa Ali Pantami zaune a ofishinsa lokacin yana ministan tattalin arziki na zamani. Hoto: @ProfIsaPantami
Source: Twitter

Pantami ya kawo wani hadisi na Annabi Muhammad (SAW) da ke nuna falalar mutuwa a ranar Juma’a, yana mai cewa:

"Annabi Muhammad (S.A.W) ya ce: 'Babu wani mai imani da zai rasu ranar Juma'a, ko darenta, fashe Allah ya kare shi daga tambayoyin kabari," Hadisin Tirmizi mai lamba ta 1074."

Daga karshe, ya yi addu’ar Allah ya jikansa da rahama tare da sanya shi a Aljannatul Firdaus, sannan ya bai wa iyalansa da makusantansa hakurin jure rashin.

Yaya Bauchi ya shiga ADC

A baya, Legit Hausa ta rahoto cewa Hon. Yaya Bauchi Tongo na daya daga cikin manyan 'yan siyasar da suka sauya sheka zuwa jam'iyyar ADC don tunkarar zabukan 2027.

Kara karanta wannan

"Suna tare cikin daki"; Tsohon jami'in DSS ya fadi abin da ya kashe Janar Sani Abacha

A ranar 31 ga watan Maris, 2026, dan majalisar mai wakiltar Gombe, Kwami da Funakaye a majalisar wakilai, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP.

Yaya Bauchi ya kasance daya daga cikin 'yan amutun tsohon shugaban kasa, marigayi Muhammadu Buhari, don ya taba shan alwashin kare mutuncinsa har karshen numfashinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com