Kalli hotunan wasu kayatattun Masallatai 5 da suka fu kyau a Duniya
Sanannen abu ne ga Musulmai da ba wadanda ba Musulmai ba cewa Masallaci wani kebabben wuri ne de da mabiya addinin Musulunci ke zuwa don ganawa da Ubangijinsu, watau ta hanyar Sallah, karatu da kuma wa’azantarwa.
Saboda wannan muhimmanci dake tattare da Masallaci ne yasa Musulmai a duk fadin duniya suke kyautata Masallatai da kwalloua irin wanda ta dace, da wannan ne majiyar Legit.ng ta kawo muku hotunan masallatai biyar da suka di kawa a Duniya.
KU KARANTA: Yadda Sanata Wammako ya azurta wani mai sana’ar sayar da Kwakwa a ranar Sallah
Masallacin Harami
Wannan shine Masallaci na farko a Duniya da aka yi shi don bautan Allah, kuma yafi kowanne Masallaci daraja a wajen Allah, kamar yadda Al-Qur’ani ya tabbatar, kuma an gina shi ne a garin Makkah, wanda a yanzu haka yana cin sama da mutum miliyan 4 a ciki da wajensa.
Masallacin Annabi
Wannan shine Masallacin da Annabi ya gina a lokacin daya koma garin Yathriba, watau Madina, sa’annan shine Masallaci mafi daraja wanda a jikinsa aka binne Manon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, da manyan sahabbansa.
Masallacin Qudus
Shidai wannan Masallaci na uku a cikin jerin Masallatan duniya yana nan ne a kasar Isra’ila, cikin garin Jerusalem, wanda a baya ma shi Musulmai suke fuskanta a matsayin Al’kiblah don gudanar da Sallah, ta cikin wannan Masallaci Annabi yayi mi’iraji.
Masallacin Hassan
Wannan Masallaci an gina shi ne a shekarar 1993 a kasar Morocco a birnin Casablanca, kuma yana nan a gab da tekun Atalakantik, tsayin hasumiyarsa ta kera mita 210.
Masallacin Sultan Brunei
Wannan shine Masallacin Sultan Omar Ali Saifuddin an gina shi a shekarar 1958 a babban birnin kasar Brunei, Bandar Seri Begawan, wanda domin tsananin kyawunsa, jama’a daga kasashen wajen na zuwa yawon bude ido a Masallacin.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng