Rana Ta 3: Masu Zanga Zanga Sun Toshe Titi Mai Muhimmanci a Abuja kan Matsalar Tsaro
- Masu zanga-zanga sun toshe gadar Karu-Nyanya, sun bukaci gwamnati ta dauki mataki kan yawaitar hare-haren yan ta'adda a kasar nan
- Hakan dai na zuwa ne yayin da zanga-zangar adawa da matsalar rashin tsaro ta shiga rana ta uku a babban birnin tarayya Abuja
- Sha'anin tsaro na ci gaba da kara kamari a Najeriya musamman bayan sace dalibai da malamai a makarantu a jihohin Oyo da Borno
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Matasa sun sake mamaye tituna a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja, yayin da zanga-zanga kan matsalar rashin tsaro ta shiga rana ta uku a jere.
Rahotanni sun nuna cewa masu zanga-zangar suka toshe wata gada da ke kan babban titin Karu-Nyanya, lamarin da ya haifar da cunkoson ababen hawa.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa masu zanga-zangar sun fito dauke da alluna masu dauke da sakonni daban-daban tare da rera wakokin suka ga gwamnati.
Sun bukaci hukumomi su tashi tsaye wajen cika nauyin da kundin tsarin mulki ya dora musu na kare rayuka da dukiyoyin al'ummar Najeriya.
An toshe muhimmiyar hanyar Abuja
Rahotanni sun nuna cewa masu zanga-zangar sun fara taruwa ne a kan wata gada da ke yankin Karu kafin daga bisani su fara tattaki zuwa Nyanya.
Toshe hanyar ya haifar da cunkoson ababen hawa mai tsanani a kan titin Abuja zuwa Keffi, lamarin da ya sa matafiya da dama suka makale na tsawon sa'o'i.
Masu zanga-zangar sun bayyana cewa yawaitar sace-sacen mutane, hare-haren yan ta'adda da sauran matsalolin tsaro sun sanya rayuwa ta zama mai wahala ga mazauna yankunan.
Sun bukaci gwamnati ta dauki mataki
Masu zanga-zangar sun yi kira ga gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro da su dauki tsauraran matakai domin dakile matsalolin tsaro da suka addabi sassan kasar nan.
Sun ce rashin tsaro ya jefa jama'a cikin fargaba tare da kawo cikas ga harkokin yau da kullum, kamar yadda Punch ta rahoto.
An tura dakarun tsaro zuwa wurin
Bayanai sun nuna cewa an jibge jami'an tsaro a yankin domin sa ido kan zanga-zangar tare da taimaka wa wajen daidaita zirga-zirgar ababen hawa.
Hukumomi sun kuma bukaci masu amfani da hanyar da su nemi wasu hanyoyi na daban saboda cunkoson da zanga-zangar ta haifar.

Source: Twitter
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a samu barkewar rikici ko asarar rai ba, sai dai har yanzu toshe hanyar na ci gaba da kawo tsaiko ga zirga-zirga a yankin Karu da Nyanya.
Wani matashi, Aminu Ahmad ya shaida wa Legit Hausa cewa ya kamata yan Arewa su dauki darasi kan gudanar da zanga-zangar lumana domin mika bukatunsu ga gwamnati.
Ya ce yan Arewa ba su iya zanga-zangar lumana da za a karelafiya ba, galibi sai an kwashi kayan mutane.
"ina fatan yan Arewa za su farka, su yi koyi da wannan zanga-zanga, sannan muna fatan hankalin gwamnati ya dawo jikinta, ta magance matsalar tsaron nan, domin abin ya wuce tunani," in ji shi.
Matawalle ya fadi hanyar dawo da tsaro
A wani labarin, kun ji cewa Karamin Ministan Tsaro na Ƙasa, Bello Matawalle, ya ce Allah SWT ne kaɗai zai iya kawo ƙarshen matsalar tsaron da ke addabar Najeriya.
Ya ce matsalar tsaro ta shafi kowa da kowa ba tare da la'akari da jam'iyya ko addini ba, don haka ya kamata 'yan Najeriya su haɗa kai da jami'an tsaro domin kawo ƙarshenta.
Ya ƙara da cewa babu wani ɗan Najeriya da ke farin ciki da abin da ke faruwa, amma wasu daga cikin 'yan adawa suna amfani da matsalar domin nuna gazawar gwamnati.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


