Alhaji Dantata zai dauki nauyin karatun dalibai 100 a sabuwar jami'ar Al-Istiqama

Alhaji Dantata zai dauki nauyin karatun dalibai 100 a sabuwar jami'ar Al-Istiqama

- Tsohon dan majalisar wakilai ya kafa sabuwar jami'a a garin Sumaila, jihar Kano

- An nada Farfesa Salisu Shehu a matsayin shugaban jami'ar

- Alhaji Dantata ya yi alkawarin biyan dukkan kudin wadanda zai dauki nauyi lokaci guda

Shugaban Kamfanin Dantata kuma dattijo, Alhaji Aminu Dantata, zai dauki nauyin karatun 'yayan talakawa 100 a sabuwar jami'ar Al-Istiqama dake Sumaila, Arewacin jihar Kano.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa Alhaji Dantata ya ce zai bada wannan gudunmuwa ne domin taimakawa wajen magance matsalar ilimi a kasar kuma yayi alkawarin biyan dukkan kudin lokaci guda.

Yayin ziyarar da shugabannin jami'ar suka kai masa a jihar Kano, Dantata ya bayyana farin cikinsa kan kafa jami'ar inda yace hakan zai taimaka wajen samar da aiki da kuma guraben karatu ga dalibai.

Yayin jinjinawa wanda ya kafa jami'ar, Suleiman Abdulrahman Kawu-Sumaila, Alhaji Dantata, ya yi kira ga sauran attajirai su kwaikwayeshi.

Hakazalika ya yi kira ga gwamnatoci da masu hannu da shuni su koyi halin daukan nauyin karatun dalibai marasa galihu.

KU KARANTA: Kasaitattun fadar sarakuna 6 a Najeriya da kyawawan hotunansu

Alhaji Dantata ya dauki nauyin karatun dalibai 100 a sabuwar jami'ar Al-Istiqama
Alhaji Dantata ya dauki nauyin karatun dalibai 100 a sabuwar jami'ar Al-Istiqama Hoto: dailynigerian.com/dantata-awards-scholarships
Source: UGC

DUBA NAN: Kasashe 7 sun dakatar da amfani da rigakafin Astrazeneca bayan wasu sun mutu, irinta Najeriya ta kawo

Kawu-Sumaila, wanda tsohon dan majalisa ne ya godewa Dantata bisa wannan gudunmuwa.

Ya ce jami'ar na shirin bada rahusa musamman a sabon diban da za'ayi ba da dadewa ba.

A cewarsa, wasu kwasa-kwasan da jami'ar za ta fara sun hada da ilmin addinin Musulunci, ilmin tattalin arziki, ilmin Akawu, ilmin Haraji, dss.

A bangare guda, wata budurwa yar Najeriya mai suna Maryam Muhammed wacce ta kammala karatun zama lauya a Birtaniya ta samu lambar yabon shugaban makarantar.

A cewar APC United Kingdom, budurwar ta kammala karatu a jami'ar Queen Mary University of London.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel