Latest
’Yan bindiga dauke da makamai sun kashe wani jami’in JTF tare da sace wata mata mai suna Asma’u da ɗanta Umar a Kyauta New Millennium City da ke Kaduna.
Dan takarar ADC, Atiku Abubakar ya yi alƙawarin dawo da tallafin man fetur idan ya ci zaben 2027, yayin da fadar shugaban ƙasa da masana suka soki shirin.
Gwamnatin Tarayya a Najeriya ta ayyana Talata, 25 ga Agusta 2026, a matsayin ranar hutu domin bikin Eid ul Mawlid, ranar haihuwar Annabi Muhammad.
Dr Ibrahim Jalo Jalingo ya yi magana kan muhawarar tallafin man fetur, inda ya ce 'yan Najeriya za su so tallafi idan tattalin arzikin ƙasa zai iya ɗaukar nauyinsa.
A labarin nan za a ji cewa wasu daga cikin mazauna jihar Sokoto sun bayyana takaici game da halin da suka shiga bayan mummunan harin yan bindiga.
Nigerian Democratic Congress ta bukaci Atiku Abubakar ya janye daga takarar shugaban ƙasa ta 2027 tare da mara wa Peter Obi baya domin ƙarfafa ’yan adawa.
FBI ta nemi kotun Amurka ta ba ta damar bayyana a ɓoye dalilin riƙe bayanan binciken Tinubu, tana cewa sakin su na iya tona dabarun tsaro da jefa rayuka a haɗari.
Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Imole ta musanta rade-radin cewa Ademola Adeleke na shirin ficewa daga Accord Party zuwa APC bayan ganawarsa da Shugaba Bola Tinubu.
Domin inganta harkar tsaro da ababen more rayuwa, gwamnoni sun karbi biliyoyi tsakanin Janairu da Yuni 2026. Gwamnatocin jihohin Najeriya sun samu tsabar kudi N435bn
Masu zafi
Samu kari