Sojoji Sun Bi Sawun Yan Bindiga da aka Raunta, An Kama Mutum 2 da ke Jinya a Adamawa

Sojoji Sun Bi Sawun Yan Bindiga da aka Raunta, An Kama Mutum 2 da ke Jinya a Adamawa

  • Sojojin 'Operation' Hadin Kai sun kama wasu mutane biyu da ake zargin ’yan ta’adda ne a karamar hukumar Hong ta jihar Adamawa
  • An kwato wayar hannu, katin SIM, baka da kibau, takobi da bindigogi guda hudu da aka kera a gida da wasu kayan da ake aikata laifi da su
  • Daya daga cikin wadanda aka kama ya ce ’yan ta’adda sun yi garkuwa da shi tare da tilasta masa shiga cikinsu domin ci gaba da aikin ta'addanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Adamawa – Dakarun Operation Hadin Kai tare da hadin gwiwar mafarauta na sun kama wasu mutane biyu da ake zargin ’yan ta’adda.

An kuma samun nasara sosai tare da kwato makamai yayin wani samame da aka gudanar bisa bayanan sirri a karamar hukumar Hong ta jihar Adamawa.

Kara karanta wannan

An birne ƴan uwa 11 da wasu mutum 41 bayan kifewar kwale kwale a Sokoto

Sojoji sun tarfa yan bindiga
Wasu sojojin Najeriya wajen aikin tabbatar da tsaro Hoto: Joris Bolomey/Getty
Source: Getty Images

Zagozala Makama ya wallafa a shafin X ta wallafa cewa an gudanar da samamen da10.15 na safe a ranar 16 ga watan Agusta, 2026 inda sojojin rundunar da ke Garaha suka yi aiki tare da mafarautan.

Yan ta'addan da aka kamawa a Adamawa

An bayyana wadanda aka kama da sunayen Hyema Luka mai shekaru 20 da Hyellaki Manasse mai shekaru 47. Majiyoyin tsaro sun ce samamen ya biyo bayan samun sahihan bayanan sirri.

Binciken farko ya nuna cewa Luka ya samu raunin harbin bindiga a kafarsa ta dama yayin wani hari da aka kai a kauyen Yau da ke kusa da Garaha a karamar hukumar Hong a ranar 24 ga Disamba, 2025.

Bincike na gaba ya kai ga kama Manasse, wanda ake zargin yana kula da Luka tare da yi masa magani a kauyen Bilamari da ke karamar hukumar Hong.

An kwato bindigu a Adamawa

A yayin tambayoyin farko, Luka ya ce ’yan ta’adda ne suka yi garkuwa da shi da karfi a lokacin da yake aiki a gonarsa da ke kauyen Lamba a karamar hukumar Hong a wani lokaci cikin shekarar 2025.

Kara karanta wannan

Yadda sojoji suka ceto bayin Allah a Kebbi da wasu jihohi 2 daga yan bindiga

Majiyoyin tsaro sun ce Luka ya tsere daga sansanin ’yan ta’addan da daddare a ranar 14 ga Agusta, 2026, kafin daga bisani jami’an tsaro su kama shi.

An kama yan bindiga 2 a jihar Adamawa
Taswirar jihar Adamawa a Arewa maso Gabas Hoto: Legit.ng
Source: Original

Kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da wayar hannu guda daya, katin SIM guda daya, baka da kibau guda biyu, takobi guda daya da aka kera a gida da kuma bindigogi guda hudu da aka kera a gida.

A halin yanzu, ana tsare da wadanda ake zargin a sansanin 232 Battalion domin ci gaba da gudanar da bincike. Samamen na baya-bayan nan na cikin kokarin da dakarun na wanzar da zaman lafiya.

An kama yan ISWAP da taimakon jami'an Adamawa

A baya, kun ji cewa sojojin Najeriya sun kama wani jami’in ISWAP da ake zargi yana aiki tare da shugaban ’yan ta’adda Dogo Gide da suka addabi jama'a.

An kuma kama wasu mutane 60 da ake zargi da haɗin gwiwa da ’yan ta’adda a jihar Adamawa yayin aikin da sojoji suka gudanar domin kakkabe masu aikata laifuka.

Sojoji sun cafke wasu ’yan ta’adda biyar tare da lalata sansanoninsu a Benue da ke yankin Arewa ta Tsakiya na Najeriya a kokarin da ake na rge ayyukan bata gari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng