Akwai Alheri: An Bude Shirin da Ake Bukatar Matasa Masu Shekaru 15 zuwa 35 Su Cike a Najeriya
- Gwamnatin Tarayya ta bukaci ’yan Najeriya matasa dmasu shekaru tsakaninn15 zuwa 35 su yi rajista da shirin NYDB
- Bayanai sun nuna cewa wannan tsarin rijistar zai taimaka wajen gano kwarewa, bukatu da wuraren da matasa suke a Najeriya
- Gwamnati za ta yi amfani da bayanan wajen hada matasa da damarmakin samun aiki domin dogaro da kansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta kaddamar da shirin rijista da tattara bayanan matasa na NYDB a fadin Najeriya
Gwamnatin ta bukaci ’yan Najeriya masu shekaru 15 zuwa 35 su yi rajista da shirin NYDB, inda ta ce hakan zai taimaka wajen gano kwarewarsu, bukatunsu da wuraren da suke.

Source: Twitter
A rahoton Daily Trust, gwamnatin tarayya ta kara da cewa hakan zai taimaka eajen tare hada matasa su da damarmakin samun aikina bangaren gwamnati da masu zaman kansu.
Ministan Harkokin Matasa, Kwamared Ayodele Olawande, ya yi wannan kiran ranar Talata a Abuja, yayin kaddamar da shirin tattara bayanan matasa na kasa (NYDB).
Matasan da ake bukatar su cike NYDB
Olawande ya ce rijistar za ta shafi matasa da ke bangaren aiki na hukuma da wadanda ke gudanar da sana’o’in kansu, ciki har da masu aikin gona, wasanni, masana’antun kirkire-kirkire da fasaha.
Ya ce samun ingantattun bayanai kan matasan Najeriya zai taimaka wa gwamnati wajen rage tazarar da ke tsakaninta da matasa, da kuma inganta tsarawa da aiwatar da shirye-shiryen da suka shafi matasa.
A cewarsa, tattara bayanan zai taimaka wajen amsa muhimman tambayoyi kamar “su waye matasanmu?”, “ina suke?”, “me za su iya yi?” da “wace irin dama suke bukata?”
Ya ce shirin wani tsari ne na gwamnati da zai ci gaba, kuma ba a kirkiro shi ne domin dalilan zabe ba.
“Muna kuma son matasan da ke aiki da masu sana’o’in kansu su kasance cikin wannan shiri.

Kara karanta wannan
Shirin Bola Tinubu na tsaka mai wuya da APM ta aika saƙo na musamman Bankin Duniya
"Muna son samun bayanan kowa, har ma muna son sanin matasan da ke aikin gona, wasanni da duk wadanda ke cikin kirkire-kirkire da fasaha, domin idan muka ce wasu na bukatar aiki, mu san cewa wadannan mutane suna bukatar kwarewa,” in ji shi.

Source: Twitter
Cibiyoyin da matasa za su yi rijista
Da yake magana, shugaban kamfanin POGMA Nigeria Limited, Otunba Oluyinka Akerele, wanda aka ba aikin, ya ce an samar da wuraren yin rijista a cibiyoyin ilimi, kuma za a fadada su zuwa kananan hukumomi da unguwanni a fadin kasar.
Ya ce shirin zai shafi matasa a makarantun sakandare, kwalejojin kimiyya da fasaha, jami’o’i da kwalejojin ilimi, da kuma wadanda ke bangaren sana’o’in kansu da yankunan karkara.
Akerele ya ce za a tura jami’an tattara bayanai zuwa kananan hukumomi 774 domin yin rijistar matasa, ciki har da wadanda ke yankunan da ke da wahalar isa.
Akerele ya ce rijistar a bude take ga ’yan Najeriya masu shekaru 15 zuwa 35, bisa tsarin Manufar Matasa ta Najeriya, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Za a samar da ayyukan yi miliyan 1
Kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da shirin samar da ayyukan yi miliyan daya da ke da alaƙa da fitar da kayayyaki zuwa ketare nan da shekarar 2030.
Gwamnatin ta dauki aniyar haka ne yayin da Najeriya ke neman samun kaso mafi girma daga kasuwar ayyukan kasashen waje da ke ci gaba da bunƙasa a duniya.
Asali: Legit.ng
