Gwamnatin Tarayya Ta ba da Hutu domin Maulidin Annabi Muhammad SAW

Gwamnatin Tarayya Ta ba da Hutu domin Maulidin Annabi Muhammad SAW

  • Gwamnatin Tarayya ta ayyana Talata, 25 ga Agusta 2026, a matsayin ranar hutu domin bikin Maulidi na bana
  • Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya taya Musulmai murna, tare da kira da su yi koyi da kyawawan halayen Annabi Muhammad
  • Ministan ya bukaci ‘yan Najeriya su yi amfani da bikin wajen addu’ar samun zaman lafiya, hadin kai da fahimtar juna a tsakanin al’umma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar ranar hutu domin bikin Maulidin Annabi Muhammad SAW.

Sanarwar ta ce an ba da hutun ne domin ba al'ummar Musulmi damar gudanar da bukukuwan cikin kwanciyar hankali.

Gwamnatin tarayya ta ba da hutun Maulidi
Shugaban kasar Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Hoto: Dada Olusegun.
Source: Facebook

Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan a madadin Gwamnatin Tarayya, cikin wata sanarwa da ma'aikatar ta wallafa a shafin X.

Kara karanta wannan

"Ku daina jira": Ministan Tinubu ya ba matasan Najeriya shawara kan gwamnati

Gwamnatin tarayya ta taya Musulmi murnar Maulidi

Ministan ya taya Musulman Najeriya da wadanda ke kasashen waje murnar wannan rana, tare da kira gare su su yi tunani kan koyarwar Annabi.

Tunji-Ojo ya ce bikin wata dama ce ga ‘yan Najeriya su koyi darussa daga rayuwar Annabi Muhammad, musamman tausayi, tawali’u da hidima ga bil’adama.

Ya ce:

“Kowane bikin Maulidi yana ba mu dalilin tsayawa mu koyi darussa daga rayuwar da ta kasance cike da tausayi, tawali’u da hidima ga wasu.
“Waɗannan halaye su ne al’ummarmu ke matukar bukata a yanzu, don haka ina kira ga kowane ɗan Najeriya ya yi tunani a kansu.”
An ba da hutun bikin Maulidi a Najeriya
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III. Hoto: The Sultanate Council Media Team.
Source: Facebook

Shawarwari da gwamnatin tarayya ta ba Musulmi

Ministan ya bukaci ‘yan Najeriya su yi amfani da bikin wajen yin addu’ar samun zaman lafiya, hadin kan kasa da kuma kyakkyawar fahimtar juna.

Ya jaddada cewa gina kasa mai zaman lafiya da kuma tabbatar da dorewarta nauyi ne da ya rataya a kan kowa, ba gwamnati kadai ba.

Kara karanta wannan

Zargin safarar kwayoyi: Tinubu ya roki kotun Amurka kan shirin sake bayanansa

Tunji-Ojo ya kuma bukaci ‘yan Najeriya su gudanar da bikin cikin natsuwa, mutunta juna da kuma kula da bukatun sauran mutane yayin bukukuwan.

Ya yi wa al’ummar Musulmi fatan samun bikin Maulidi mai cike da zaman lafiya da farin ciki, tare da kyakkyawar makoma ga kasa baki daya.

Haka kuma, ministan ya sake tabbatar da kudirin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya da kuma inganta zaman lafiya.

Ya bukaci ‘yan Najeriya su ci gaba da mara wa kokarin karfafa hadin kan kasa baya, tare da samar da zaman lafiya tsakanin mutane masu addinai da al’adu daban-daban.

Sarkin Musulmi ya umarci fara duban wata

A kwanan nan, mu ka kawo muku cewa Majalisar Sarkin Musulmi ta jihar Sokoto ta fitar da sanarwa game da duban watan Maulidi a Najeriya.

Majalisar ta bukaci Musulmi su lura da sararin sama, sannan su kai rahoton ganin wata ga shugaban gunduma ko ƙauye mafi kusa.

Rahotannin ganin watan za a isar da su ga Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, ta tsarin shugabancin gargajiya na ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.