Jihohi 29 Sun Samu Biliyoyin Kudi na Musamman da Sunan Tsaro da Ayyuka a wata 6

Jihohi 29 Sun Samu Biliyoyin Kudi na Musamman da Sunan Tsaro da Ayyuka a wata 6

  • Gwamnatocin jihohin Najeriya sun samu tsabar kudi N435bn a cikin watanni shida daga asusun FAAC na tarayya
  • Enugu, Legas da Ondo ne kan gaba a kudin da aka ba jihohi wajen inganta ayyukan tsaro da ababen more rayuwa
  • Jihohin Adamawa da Anambra ba su samu komai ba daga wannan tsarin tallafin tsakanin Janairu da Yuni 2026

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Gwamnatocin jihohi suna samun biliyoyin kudi ta wani sabon tsari da aka kawo a karkashin kwamitin FAAC.

Ana bada kudin ne da nufin a yaki matsalar rashin tsaro kuma a samar da ayyukan more rayuwa a wasu jihohin Najeriya.

Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu a taron ECOWAS a Abuja Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Wani rahoto na musamman da aka gani a jaridar Punch ya nuna an fitar da akalla N435bn ga jihohi 29 a cikin tsawon watanni shida.

Bayanin da aka samu daga shafin BudgIT ya nuna an raba kudin daga watan Junairu zuwa Yunin 2026, abin da ba a yi ba a bara.

Kara karanta wannan

Tinubu ya dauki sabon mataki kan tsaro, ya ba da wa'adin kwanaki 90

An raba wa jihohi karin kudi daga asusun tarayya

An yi rabon ne lokacin da ake fama da matsalar garkuwa da mutane, satar ‘yan makaranta da karancin abubuwan more rayuwa.

Da aka yi nazarin bayanan da aka samu, an fahimci jihohi 16 sun tashi da N265bn domin gwamnatoci su yaki matsalar tsaro.

Wasu jihohi 13 sun ce sun samu N169.75bn daga lissafin FAAC, sai dai ba a nuna ko kudin tsaro ko na ayyukan more rayuwa ba ne.

Yadda jihohi suka samu N435bn a 2026

Adadin kudin da aka ba jihohin nan ya tashi kan N435.25bn. A gefe akwai jihohin Adamawa, Anambra da Oyo ba su samu sisin kobo ba.

Akwa Ibom ba ta cikin jihohi da aka duba, amma ba a san nawa aka ba ta ba. Babu Bayelsa, Edo, Osun da Rivers a wannan sahu.

Bauchi, Borno, Cross River, Ebonyi, Enugu, Gombe, Imo, Jigawa da kuma Kano sun tabbatar da cewa sun amfana da kudin.

Kara karanta wannan

Dalilai 15 da suka sa APC ta sha kasa a zaben jihar Osun

Rahoton ya ce haka zalika gwamnatocin Katsina, Kogi, Kwara, Ogun, Sokoto, Taraba da Yobe.

Biliyoyin kudin da jihohin suka samu

Da N27.0bn, Enugu ta fi kowa samun wannan kudi sai Gombe ta ke biye da N24.50bn. Sai Jigawa, Katsina da Ogun masu N19.5bn.

Cross River da Yobe sun tashi da N17.50bn a cikin watannin shida. Jihar Borno da Bauchi kuwa sun samu N16.41bn da N14.58bn.

A jihohin da suka bambanta lissafin abin da suka samu, Sokoto da Kogi ne a kashin baya.

Shugaban Najeriya
Bola Tinubu ranar ya zama sabon Shugaban Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Idan aka zo kan jihohin da suka hada kudin da suka samu a cikin kason FAAC, za a ga Ondo da Legas sun samu N31bn da N30bn.

Sai Abia N24.50bn, Nasarawa N21.24bn, Niger N15.50bn. Akwai Benue da Plateau masu N14bn sai jihar Delta kuma ta samu N5.50bn.

Ekiti ta tashi N5.38bn, Kaduna ta samu N3.83bn, an biya Kebbi da Zamfara N1.95bn da N1.71bn.

Kudin da kwastam suke samo wa gwamnati

Kuna da labarin cewa an samu ranar da kwastam ta rika samun fiye da N1bn a duk awa 1 a Legas sakamakon gyare-gyare da aka yi.

Kara karanta wannan

Ana korafi a kan zargin lakadawa Musa Mai Sana'a duka kan tallan Tinubu a Katsina

Jami'an Kwastam na reshen Apapa sun tattaro wa gwamnati N28.1bn a rana guda, abin da ba a taba gani ba tun da aka kafa hukumar a tarihi.

Shugaban reshen, Emmanuel Oshoba, ya bayyana cewa kudin za su taimaka wajen bunkasa tattalin arziki da ababen more rayuwa a jihohi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng