Portugal Ta Ƙaƙaba Dokar Haramta wa Mata Musulmi Saka Niƙabi, an Yi Mata Rubdugu

Portugal Ta Ƙaƙaba Dokar Haramta wa Mata Musulmi Saka Niƙabi, an Yi Mata Rubdugu

  • Kasar Portugal ta kafa dokar hana sanya nikabi da ke rufe fuska a wuraren jama’a, matakin da masu suka suka ce ya shafi Musulmai mata
  • Shugaba António José Seguro ya rattaba hannu kan dokar, wadda ta tanadi tarar Yuro 150 zuwa 3,000 ga masu karya dokar
  • Jam’iyyun adawa sun yi Allah-wadai da dokar, suna cewa za ta iya kara kyamar Musulunci da wariya ga al’ummar Musulmi a Portugal

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Portugal - Kasar Portugal ta kafa doka wacce ta shafi mata Musulmi kai tsaye da mutane da dama suke ta ce-ce-ku-ce.

An tabbatar da cewa dokar za ta haramta rufe fuska a wuraren jama’a, matakin da aka soke shi saboda zargin ya shafi matan Musulmi masu sanya nikabi.

An sanya dokar hana nikabi a Portugal
Wata mata sanye da nikabi tana hutawa. Hoto: Getty Images.
Source: UGC

Shugaba António José Seguro ya rattaba hannu kan dokar bayan majalisar dokokin kasar ta amince da ita a watan Yuli, dokar ta haramta tufafi ko wasu abubuwa.

Kara karanta wannan

FBI na fargabar sakin bayanan zargin Tinubu a Amurka ya jawo babban hadari

Waɗannan abubuwan na nufin ɓoye fuskar mutum ko hana a gane shi a wuraren jama’a, haka kuma, tilasta wa wani rufe fuskarsa ya zama laifi.

Dokar ta haramta tilasta wa mutum rufe fuska bisa dalilan da suka shafi jinsi, addini, shekaru ko asalinsa, kamar yadda sabon tsarin ya tanada.

Da yake kare dokar, Seguro ya ce fuska tana taka muhimmiyar rawa wajen hulɗar ɗan Adam da sadarwa tsakanin mutane a cikin al’umma.

“Ya kamata a ɗauki fuska a matsayin muhimmin ginshiƙi na ɗan Adam wajen bayyana ainihi da sadarwa."

- In ji Seguro

Kafofin yaɗa labaran Portugal sun kira dokar da sunan “dokar burka”.

Gamayyar jam’iyyun masu ra’ayin dama da na masu tsattsauran ra’ayi sun mara mata baya.

Sai dai wasu jam’iyyu sun yi adawa da dokar, suna bayyana damuwa kan tasirinta ga ’yancin addini da al’ummar Musulmi.

A ƙarƙashin sabuwar dokar, duk wanda ya karya ta na iya fuskantar tarar da ta kai daga Yuro 150 zuwa Yuro 3,000.

Sai dai dokar ta tanadi wasu keɓancewa ga dalilan lafiya, aikin yi, fasaha da yanayin sanyi ko zafi, inda za a iya rufe fuska.

Kara karanta wannan

Tsohuwar matar yaron El Rufai ta yi magana watanni shekaru 3 mutuwar aurensu

Haka kuma, dokar ba za ta shafi wuraren ibada, ofisoshin jakadanci da jiragen sama ba, kamar yadda tanadin dokar ya bayyana.

Jam’iyyun adawa da wasu kungiyoyin shari’a sun soki dokar, suna nuna damuwa kan yiwuwar ta tauye ’yancin addini da kuma ƙara nuna wariya.

Jam’iyyar Socialist ta Portugal (PS), Livre da Jam’iyyar Kwaminis ta Portugal (PCP) sun yi adawa da dokar, suna gargadin cewa za ta iya ƙara kyamar Musulunci.

PS ta bayyana dokar a matsayin wadda aka kafa da “manufar kyamar Musulunci”, yayin da PCP ta ce ba ta da alaƙa da haƙƙin mata.

PCP ta kuma ce dokar ba ta da alaƙa da matsalar tsaro, sai dai tana da nufin haifar da ƙiyayya da nuna wariya ga ƙananan al’ummomi.

Livre ma ta zargi jam’iyyun masu ra’ayin dama da haifar da abin da ta kira “tsoron ɗabi’a kan zargin mamayar Musulunci”.

Masu goyon bayan dokar sun kare ta da hujjar cewa tana taimakawa wajen gane mutum da sauƙaƙa sadarwa a wuraren jama’a.

Shugaba Seguro ya amince cewa batun na da matuƙar muhimmanci ga al’umma da al’adu, saboda yana da alaƙa da ’yancin mutum da addini.

Kara karanta wannan

Sojoji sun ɗana tarko, an daƙile harin garkuwa da mutane a Zamfara

Yanzu Portugal ta shiga cikin jerin ƙasashen Turai da suka kafa dokoki kan rufe fuska a wuraren jama’a, duk da cewa bambancin dokoki da keɓancewa ya kasance.

An kori dalibai kan saka hijabi a Faransa

A baya, an ji cewa wasu makarantu a kasar Faransa sun kori dalibai da dama da su ka ki bin dokar kasar wanda ya shafi dalibai Musulmi.

Faransa ta kafa dokar sanya hijabi ko abaya a makarantu da duk wani tufafin da ke nuna alamun addini wanda ya jawo magana.

Ministan ilimi a kasar, Gabriel Attal shi ya bayyana haka inda ya ce daliban sun bijirewa dokar kasar da ta kafa wanda hakan saba doka ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.