ADC Ta Fito da Bayani, An Ji Dalilin Atiku na Kin Sa Hannu a Yarjejeniyar Zaman Lafiya Ta Zaben 2027

ADC Ta Fito da Bayani, An Ji Dalilin Atiku na Kin Sa Hannu a Yarjejeniyar Zaman Lafiya Ta Zaben 2027

  • Jam'iyyar ADC ta yi karin haske kan rashin ganin Atiku Abubakar a taron rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben 2027
  • Jam’iyyar ta ce Kwamitin Zaman Lafiya na Kasa bai ɗauki matakin da ya dace kan tashe-tashen hankulan siyasa da ke faruwa ba
  • Bolaji Abdullahi ya ce ya kamata a riƙa ɗaukar ’yan siyasa da alhaki kan kalaman da za su iya haddasa tashin hankali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Jam’iyyar ADC ta kare rashin halartar ɗan takararta na shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, wajen rattaba hannu kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya ta Ƙasa.

Ta bayyana cewa matakin ya kasance wata hanya ce ta nuna rashin amincewa da abin da ta bayyana a matsayin gazawar tsarin zaman lafiyar wajen magance tashin hankalin zaɓe.

Atiku.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar lokacin da yake jawabi a taron matasan ADC a Abuja Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ne ya bayyana hakan ne ranar Juma’a yayin wata hira a shirin Sunrise Daily na Channels Television.

Kara karanta wannan

Yadda Atiku ya rikita Najeriya da maganar maido tallafin man fetur

Ya ce ADC ta yanke shawarar kin halartar bikin rattaba hannun ne da gangan, yana mai cewa ’yan siyasa sun sha rattaba hannu kan irin waɗannan yarjejeniyoyi a lokutan zaɓe da suka gabata ba tare da ganin an ɗauki mataki idan an saba ba.

Jam'iyyar ADC ta yi tir da tsarin

“Mun kasance muna rattaba hannu kan wannan abu shekara bayan shekara, a kowane lokacin zaɓe; muna rattaba hannu don nuna goyon bayan wannan alƙawari.
"Amma abubuwa har yanzu suna faruwa; ana kashe mutane, ana gallaza musu, kamar yadda ya faru a Osun, amma ba mu ji Kwamitin Zaman Lafiya ya ce komai ba. Ba sa yin Allah wadai da kisan.”

- Bolaji Abdullahi.

Abdullahi ya kuma yi tsokaci kan kalaman da aka danganta ga Sanatan Osun, Francis Fadahunsi, gabanin zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar kwanan nan, yana mai cewa kwamitin bai dauki matakin da ya kamata ba.

Kara karanta wannan

INEC ta yi maganar goyon bayan wani dan takara ko jam'iyya a zaben 2027

“Lokacin da Sanata Fadahunsi ya ce su fita su kashe mutane, ba mu ji Kwamitin Zaman Lafiya ya ce komai ba. To, mene ne amfanin hakan? Saboda haka, wannan ita ce hanyar da mu (ADC) muka ce a’a,” in ji kakakin ADC.
Bolaji Abdullahi.
Mai magana fa yawun jam'iyyar adawa ta ADC, Mallam Bolaji Abdullahi Hoto: @BolajiADC
Source: Twitter

ADC ta bukaci a dauki mataki

Ya ce matsayin jam’iyyar na da nufin matsa wa Kwamitin Zaman Lafiya na Ƙasa, wanda ya shirya yarjejeniyar, lamba domin ya wuce shirya bukukuwan rattaba hannu kawai, cewar rahoton Leadership.

A cewarsa, ya kamata a ɗauki shugabannin siyasa da alhaki kan kalaman da za su iya ƙarfafa tashin hankali, ba tare da la’akari da matsayinsu na siyasa ba.

NDC ta nemi Atiku ya janye takara

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar adawa ta NDC ta bukaci dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar ya hakura da takara a babban zaben 2027.

NDC ta bukaci tsohon mataimakin shugaban kasar ya marawa dan takararta, Peter Obi baya domin hada karfi da karfe wajen kayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zabe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262