Gwamnatin Tinubu Ta Ware Gwamnonin Arewa 3, Za Ta Karrama Su saboda Kokarinsu

Gwamnatin Tinubu Ta Ware Gwamnonin Arewa 3, Za Ta Karrama Su saboda Kokarinsu

  • Gwamnatin Tarayya za ta karrama wasu daga cikin gwamnonin Arewacin Najeriya saboda nasarorin fasahar zamani
  • Za a gudanar da bikin bayar da lambar yabo a Abuja ranar 13 da 14 ga Oktoba, yayin taron Nigeria GovTech na karo na huɗu
  • Bikin zai mayar da hankali kan amfani da fasahar zamani wajen inganta ayyukan gwamnati da bunƙasa tattalin arziki na zamani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Gwamnatin Tarayya ta shirya karrama wasu daga cikin gwamnonin Najeriya saboda nasarorin da suka samu a bangaren fasahar zamani.

Daga cikinsu akwai na Katsina Dikko Umaru Radda, da na Zamfara Dauda Lawal da Cross River Bassey Otu sai kuma Enugu Peter Mbah.

Gwamnatin tarayya za ta karrama wasu gwamnoni
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Jaridar The Nation ta ce sauran sun hada da na Anambra Charles Soludo da jihar Benue Hyacinth Alia a bikin 'Nigeria GovTech Public Service Awards' da aka shirya na shekarar 2026.

Kara karanta wannan

'Babbar masifar da Arewa za ta fuskanta idan Atiku ko Obi suka lashe zaɓen 2027'

Musabbabin shirin karrama gwamnonin a Najeriya

Za a karrama gwamnonin ne saboda gudunmawarsu wajen inganta harkokin gwamnati ta hanyar fasahar zamani, kirkire-kirkire da samar da ayyukan gwamnati ta bangaren zamani.

Hukumar Bureau of Public Service Reforms (BPSR) ce ta shirya taron tare da haɗin gwiwar Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tattalin Arziki da Haɗa Kowa cikin Tsarin Kuɗi.

Taken taron shi ne: 'Ƙarfafa Gwamnati a bangaren zamani: Faɗaɗa Ababen More Rayuwa na zamani don Ingantacciyar Gudanarwa da Samar da Ayyuka.'

Za a karrama wasu gwamnonin Najeriya
Gwamna Dikko Umaru Radda, Dauda Lawal da Ali Hyacinth na Benue. Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda, Dauda Lawal, Alia Iormen Hyacinth.
Source: Facebook

A cikin wata sanarwa da ta bayyana taron, Darakta-Janar na BPSR, Dasuki Arabi, ya ce taron zai tattauna yadda ababen more rayuwa na dijital da fasahohin zamani za su ƙarfafa hukumomin gwamnati.

Bangaren da taron zai mayar da hankali

Ya ce taron zai kuma mayar da hankali kan haɗa tsarin hukumomi, amfani da sabbin fasahohi da kirkire-kirkire wajen inganta ayyukan gwamnati da samar da kyakkyawar hidima ga jama'a.

Kara karanta wannan

Da sauran rayuwa: Tsohon sanata mai shekaru 70 ya auri budurwa ƴar shekara 18

Arabi ya ce taron zai nuna muhimmiyar rawar da sauya tsarin gwamnati zuwa na zamani ke takawa wajen cika burin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na samar da Najeriya mai inganci, haɗa kowa da kuma dogaro da fasahar zamani.

Ya ƙara da cewa hakan zai taimaka wajen inganta haɗa jama'a cikin tsarin hada-hadar kuɗi, bunƙasa tattalin arziki na zamani da kuma sauƙaƙa wa 'yan Najeriya samun ayyukan gwamnati, cewar Punch.

Ya ce an ƙirƙiri lambar yabon ne domin karrama ma'aikatan gwamnati da ƙungiyoyin da suka nuna jajircewa wajen amfani da fasaha wajen sauya tsarin hukumomi da inganta ayyukan da ake yi wa jama'a.

Gwamnonin shida za su samu karramawar ne bayan wani kwatancen tantance ayyukan gwamnati na zamani a jihohin Najeriya, inda aka duba ci gaban ayyukan dijital, shirye-shiryen hukumomi da ababen more rayuwa.

An karram Dauda Lawal a ketare

An ji cewa an karrama Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara da lambar yabo ta zaman lafiya da kyayyawan shugabanci a kasar Ghana.

An yabawa gwamnatinsa kan sauye-sauyen tattalin arziki da shugabanci nagari a Zamfara da ke Arewa maso Yamma.

Gwamnan ya ce lambar yabon za ta kara masa kwarin gwiwar yin aiki domin ceto jihar daga dukkan wani kalubale.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.