2027: Yadda Atiku Ya Rikita Najeriya da Maganar Maido Tallafin Man Fetur

2027: Yadda Atiku Ya Rikita Najeriya da Maganar Maido Tallafin Man Fetur

  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya sake tayar da batun tallafin man fetur
  • Atiku ya ce za a dawo da tallafin ne ta hanyar da za ta tabbatar da cewa an yi amfani da kuɗin cikin gaskiya, tare da binciken yadda aka sarrafa su
  • Sai dai fadar shugaban ƙasa ta soki matakin, yayin da masana suka ce samar da ingantattun matatun mai a cikin gida shi ne mafita mai ɗorewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ce zai dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a 2027.

Atiku ya bayyana hakan ne a wata hira a ranar Laraba, inda ya soki illolin cire tallafin man fetur tare da tambayar inda kuɗin da gwamnati ta ce ta tara suka tafi.

Kara karanta wannan

Malamin addini da ke goyon bayan Tinubu ya magantu kan tallafin mai

Atiku Abubakar a Abuja
Dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar. Hoto: Paul Ibe
Source: Facebook

Daily Trust ta rahoto cewa matakin na Atiku ya sake haifar da muhawara kan makomar tallafin man fetur, musamman ganin yadda farashin mai a yanzu yake dogaro da sauye-sauyen kasuwar duniya.

Atiku zai dawo da tallafin mai

Atiku ya ce bai yi adawa da cire tallafin man fetur a farko ba, amma ya nuna rashin gamsuwa da yadda gwamnati ta yi amfani da kuɗin da ta ce ta samu bayan cire tallafin.

Punch ta wallafa cewa ya ce idan ya zama shugaban ƙasa, zai dawo da tallafin tare da binciken yadda aka kashe kuɗin tallafin da suka gabata.

Ya ce:

“Da farko ban yi adawa da cire tallafin man fetur ba. Amma yanzu da aka cire shi, ina kuɗin?
“Idan na lashe zaɓen shugaban ƙasa, zan dawo da tallafin. Kuma duk wanda ya saci kuɗin tallafin Najeriya zai mayar da su.”

Atiku ya fadi sabon tsarin tallafi

Sai dai daga baya Atiku ya yi karin bayani kan tsarin tallafin da yake son aiwatarwa, yana mai cewa ba zai dawo da tsohon tsarin tallafin shigo da man fetur ba.

Kara karanta wannan

Tinubu ya firgita da Atiku ya ce zai maido tallafin mai, ya yi martani mai zafi

A cewar sa, shirin da yake gabatarwa zai mayar da tallafin daga shigo da mai zuwa samar da shi a cikin gida, musamman ta matatun mai na Najeriya.

Ya ce za a sanya iyaka kan tallafin, a tanade shi cikin kasafin kuɗi a fili sannan a gudanar da bincike mai zaman kansa domin tabbatar da gaskiyar adadin man da aka samar.

Martanin fadar shugaban kasa

Fadar shugaban ƙasa ta soki alkawarin Atiku, inda mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya zarge shi da neman mulki ko ta halin kaka.

Onanuga ya ce Atiku ya koma ga wani tsohon tsari da ya kamata a yi watsi da shi, yana mai cewa tsarin tallafin man fetur ya kasance cikin ɓarna da almundahana.

Ya kuma ce Atiku a baya ya yi imanin cewa ya kamata a kawar da tallafin, amma yanzu ya sauya matsayinsa saboda kusantar zaɓen 2027.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu na magana a taro. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Meye mafita ga 'yan Najeriya?

Wani masanin tattalin arziki kuma masani kan harkar mai da gas, Dr Marcel Okeke, ya ce mafita mai ɗorewa ga tsadar man fetur ita ce gina masana'antar tace mai mai ƙarfi a cikin Najeriya.

Kara karanta wannan

Atiku ta tayar wa Tinubu hankali kan kudirin dawo da tallafi idan ya yi nasara

Ya bayyana cewa tallafin mai na nufin gwamnati tana ɗaukar wani bangare ko dukkan bambancin da ke tsakanin kuɗin shigo da mai da kuma farashin da jama'a suke biya.

Okeke ya ce idan aka samar da man fetur a cikin gida, farashinsa zai rage dogaro da wasu abubuwa kamar kuɗin shigo da mai, farashin danyen mai a kasuwar duniya, canjin kuɗi da kuɗin jigilar kaya.

Dangote ya kara kudin mai

A wani labarin, mun rahoto muku cewa matatar Dangote da ke Legas ta kara farashin dizil da man fetur ga manyan 'yan kasuwar Najeriya.

Farashin dizil ya tashi daga N1,570 zuwa N1,670 kan kowace lita, wanda ke nufin an samu ƙarin N100 inda aka kara N20 a man fetur.

Rahoto ya nuna cewa karin farashin ya zo ne yayin da farashin danyen mai a kasuwar duniya ya haura dala 94.13 kan kowace ganga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng