Duk da Alkawarin da Ya Yi, NDC Ta Nemi Atiku Ya Janye daga Takarar Shugaban Kasa a 2027

Duk da Alkawarin da Ya Yi, NDC Ta Nemi Atiku Ya Janye daga Takarar Shugaban Kasa a 2027

  • Jam'iyyar adawa ta NDC ta bukaci dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar ya hakura da takara a babban zaben 2027
  • NDC ta bukaci tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya mara wa dan takararta, Peter Obi baya domin kayar da Bola Ahmef Tinubu
  • Tun farko dai Atiku ya bayyana cewa zaben shugaban kasa na 2027 ne na karshe da zai nemi takara ko da kuwa ya yi nasara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Jam'iyyar NDC ta yi kira ga ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, da ya janye daga takarar shugaban ƙasa ta 2027.

NDC ta bukaci tsohon mataimakin shugaban kasar ya marawa dan takararta, Peter Obi baya domin hada karfi da karfe wajen kayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Abin da Atiku zai yi don magance rashin tsaro cikin kwana 100 idan ya zama shugaban kasa

Atiku.
Dan takarar shugaban kasa karkashin inuwar jam'iyyar ADC a zaben 2027, Alhaji Atiku Abubakar Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Daraktan Kafofin Yaɗa Labarai da Sadarwa na jam'iyyar NDC ta kasa, Theo Abu Agada, ne ya yi wannan kiran a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Alhamis da ta gabata.

Agada ya ce janyewar Atiku daga takarar da kuma mara wa Obi baya zai ƙara ƙarfafa damar ’yan adawa na kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.

2027: NDC ta nemi Atiku ya janye

Mai magana da yawun NDC ya ce janyewar Atiku ba za ta rage darajar tarihin siyasarsa ba, sai dai za ta iya taimakawa wajen samar da haɗakar ’yan adawa mai ƙarfi.

Yayin da ya amince da tarihin Atiku a siyasa da hangen nesansa ga Najeriya, Agada ya ce tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kamata ya yi la’akari da janyewa daga takarar shugaban ƙasa domin amfanin ’yan adawa baki ɗaya.

Ya rubuta:

“A kowane lokacin zaɓe, Atiku Abubakar mutum ne nagari kuma jajirtacce, amma a wannan matakin ya kamata ya hakura.

Kara karanta wannan

Atiku ta tayar wa Tinubu hankali kan kudirin dawo da tallafi idan ya yi nasara

“Ra’ayinsa na gina Najeriya mai aiki yana da kyau, amma a wannan lokaci ya kamata ya hakura da burinsa.
“Idan ya janye, babu abin da zai rage kyakkyawan tarihin da ya bari. Ya kamata AA ya mara wa Obi baya domin korar APC daga mulki.”
Obi da Atiku.
Dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi da tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar Hoto: Peter Obi, Stiku Abubakar
Source: Facebook

Atiku ya kusa hakura da neman mulki

Wannan kira ya zo ne jim kaɗan bayan Atiku ya bayyana cewa zaɓen shugaban ƙasa na 2027 zai kasance na ƙarshe da zai shiga takara, ko da kuwa sakamakon zaɓen ya kasance mai kyau ko akasin haka.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi kai tsyae a dandalin sada zumunta na Facebook.

Atiku ya yi alkawarin dawo da tallafin fetur

A wani labarin, kun ji cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ce zai dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a 2027.

Ya ce gwamnati ta kasa fadin inda kuɗin da aka samu sakamakon cire tallafin man fetur suka tafi, yana mai cewa ya kamata a yi amfani da su wajen rage talauci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262