Malamin Addini da ke Goyon Bayan Tinubu Ya Magantu kan Tallafin Mai
- Dr Ibrahim Jalo Jalingo, ya ce batun cire ko dawo da tallafin man fetur zai ci gaba da kasancewa abin tattaunawa saboda muhimmancinsa ga tattalin arzikin Najeriya
- Malamin ya ce dukkan 'yan Najeriya za su so gwamnati ta taimaka masu da tallafin man fetur idan tattalin arzikin ƙasa zai iya ɗaukar nauyin hakan
- Ya kuma tunatar da cewa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya taɓa bayyana cewa cire tallafin man fetur abu ne da ba makawa a yi shi a shekarun baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Shugaban malaman Izala, Dr Ibrahim Jalo Jalingo, ya yi magana kan muhawarar da ake yi a Najeriya game da cire tallafin man fetur ko kuma dawo da shi.
Dr Jalo, wanda ya nuna goyon bayansa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027, ya bayyana ra'ayinsa ne bayan maganar da Atiku Abubakar ya yi.

Source: Facebook
A sakon da ya wallafa a Facebook, Dr Jalo ya ce duk da cewa 'yan ƙasa za su so gwamnati ta taimaka masu ta hanyar ci gaba da tallafa wa man fetur, hakan ya dogara ne da ƙarfin tattalin arzikin ƙasa.
Me Dr Jalo ya ce kan tallafin?
Dr Jalo ya ce gaskiyar al'amari ita ce, dukkan 'yan ƙasa za su so a ce gwamnati ta taimaka masu wajen samun man fetur mai sauƙin farashi.
Sai dai ya ce idan ƙarfin tattalin arzikin ƙasa bai iya ɗaukar nauyin tallafin ba, to ba za a iya tilasta yin hakan ba.
Ya yi amfani da wata karin magana ta Larabci wajen bayyana matsalar, inda ya ce wanda bai mallaki abu ba ba zai iya bayar da shi ba.
Ya ce:
“Gaskiyan al'amari shi ne dukkan 'yan ƙasa za su so in da da hali a ce gwamnati ta taimaki jama'ar kasa, ta yi masu, ko ta bar masu tallafin man fetur, sai dai in ƙarfin tattalin arzikin Ƙasar ne ba zai iya ɗaukan ɗawainiyar yin hakan ba.”

Kara karanta wannan
Abin boye ya fito: An gano bashi ya yi wa Amurka katutu yayin da ta ke yaki da Iran
Tinubu ya cire tallafin a 2023
Dr Jalo ya tunatar da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cire tallafin man fetur a farkon hawansa mulki a shekarar 2023.
A bayanin da ya yi, ya ce shugaban ya bayyana dalilan da suka sa gwamnati ba za ta iya ci gaba da ɗaukar nauyin tallafin ba.
Cire tallafin ya kasance ɗaya daga cikin manyan sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Tinubu ta aiwatar, inda farashin man fetur ya tashi tare da ƙara tasirin tsadar sufuri da sauran kayayyaki ga 'yan ƙasa.

Source: Facebook
Atiku ya taɓa cewa zai cire tallafi
Dr Jalo ya kawo misalan kalaman manyan 'yan siyasa kan batun tallafin man fetur, musamman tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar.
Ya ce a ranar 22 ga Yuli, 2022, yayin wata hira da Arise Television, Atiku ya bayyana cewa cire tallafin man fetur abu ne da ba makawa, amma ya kamata a yi hakan ta hanyar tattaunawa da ƙungiyoyin ƙwadago da sauran ɓangarorin tattalin arziki.
Ya kuma ce a ranar 1 ga Nuwamba, 2022, a wani taro a Lagos, Atiku ya bayyana cewa zai ci gaba daga inda aka tsaya tare da cire tallafin man fetur gaba ɗaya.
Haka kuma, Dr Jalo ya ce Atiku ya bayyana a jaridar The Guardian a ranar 1 ga Disamba, 2022, cewa idan ya zama shugaban ƙasa, zai magance batun cire tallafin cikin kwanaki 100 na farko na mulkinsa.
Muhawarar dawo da tallafin mai
A wani labarin, kun ji cewa batun tallafin man fetur ya sake daukar sabon salo bayan Atiku Abubakar ya yi alƙawarin dawo da tallafin idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a 2027.
Shugaba Tinubu ya mayar da martani kan wannan alƙawari, inda ya bayyana cewa Atiku yana nuna “rashin fahimta” kan mulki da tattalin arziki.
Tinubu ya yi wannan magana ne a ranar Alhamis yayin da yake karɓar Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, bayan nasarar da gwamnan ya samu a zaben da aka gudanar a jihar.
Asali: Legit.ng

