Trump Ya Kawo Babbar Matsala bayan Iran Ta Mika Tayin Bude Hormuz ga Amurka

Trump Ya Kawo Babbar Matsala bayan Iran Ta Mika Tayin Bude Hormuz ga Amurka

  • Kasar Musulunci ta Iran ta gabatar wa Amurka da shirin kwanaki bakwai na sake buɗe Mashigar ruwa ta Hormuz
  • Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi ya ce za a dawo da zirga-zirgar jiragen ruwa idan Amurka ta cika sharuddan
  • Rahotanni sun ce shugaban kasat Amurka, Donald Trump ya yi watsi da shirin, yayin da ya nuna yiwuwar sabon harin bama-bamai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Amurka - Iran ta ce ta gabatar da wani tsari ga Amurka na sake buɗe mashigar Hormuz mai matuƙar muhimmanci, amma cikin sa’o’i kaɗan rahotanni suka bayyana cewa Shugaba Donald Trump ya yi watsi da shirin.

Mashigar ruwan, wadda ke da muhimmiyar rawa wajen samar da man fetur ga duniya, ita ce cibiyar rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran, wanda ya shiga halin ɗaure kai bayan shafe kusan watanni bakwai.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 7 da Najeriya ta nema a taron UNGA karo na 81

Trump.
Shugaban Amurka, Donald Trump yana jawabi ga manema labarai a fadar White House
Source: Getty Images

Tashar Channels tv ta ce ƙoƙarin sasanci da aka yi a taron Majalisar Ɗinkin Duniya na shugabannin ƙasashe a New York a wannan mako sun haifar da fata cewa za a samu ci gaba wajen cimma yarjejeniya.

Iran ta yi wa Amurka tayin bude Hormuz

Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya gana da wakilin Trump, Steve Witkoff, ranar Talata, inda suka tattauna batun rikicin. Tun da farko, Iran ta bayyana sharuddan kawo ƙarshen yaƙin da sake buɗe mashigar ruwan.

“Ta hannun Qatar, Iran ta isar wa Amurka da wani shiri na kwanaki bakwai. Idan aka cika sharuddan da ake buƙata, za a iya sake buɗe mashigar, sannan a dawo da zirga-zirgar jiragen ruwa yadda aka saba cikin kwanaki bakwai,” in ji Araghchi a Majalisar Ɗinkin Duniya.
“Yanzu zaɓin yana hannun Amurka. Iran ba ta amince da tilastawa, barazana ko tsoratarwa ba, kuma ba za ta mika haƙƙoƙinta na mallakar ƙasarta ba saboda matsin lamba.”

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa 7 sun shilla ƙasar Amurka, sun nemo abin da zai amfani 'yan Najeriya

Trump ya yi fatali da tayin Iran

Sai dai sa’o’i kaɗan bayan kalaman nasa, jaridar The Wall Street Journal ta ruwaito cewa Trump ya yi watsi da shirin, tana ambaton wasu jami’an Amurka da ke da masaniya kan batun.

Rahoton ya ce shugaban mai shekaru 80 na shakkar cewa Tehran za ta cika buƙatunsa, sannan ya ƙara da cewa Trump na ganin yiwuwar sake kai hare-haren bama-bamai.

Hormuz.
Wasu jirage a hanyar wuce wa ta mashigar ruwa ta Hormuz Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Trump ya kuma wallafa wani hoto, wanda ke nuna taswirar Mashigar Hormuz da aka yi wa alama da rubutun “Trump Strait”.

Rahotannin kafafen yaɗa labarai na baya sun nuna cewa sabon shirin ya ƙunshi dakatar da duk wani yaƙi a Gabas ta Tsakiya na tsawon kwanaki bakwai, ciki har da Lebanon.

Trump ya sauya sunan fasahar AI

Kun ji cewa shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce daga yanzu za a riƙa kiran fsahar AI da “Super Intelligence” watau SI a gwamnatinsa.

Trump ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin jawabin buɗe taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 da aka gudanar a brinin New York na kasar Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262