'Babbar Masifar da Arewa Za Ta Fuskanta idan Atiku ko Obi Suka Lashe Zaɓen 2027'

'Babbar Masifar da Arewa Za Ta Fuskanta idan Atiku ko Obi Suka Lashe Zaɓen 2027'

  • Shugaban APC Nentawe Yilwatda ya ce nasarar Atiku Abubakar ko Peter Obi a 2027 ka iya lalata Arewacin Najeriya baki daya
  • Yilwatda ya kare cire tallafin man fetur, yana mai cewa kudaden da aka samu na taimakawa ayyukan hanyoyi, noma da ilimi a Arewa
  • A Ondo da Imo, shugabannin APC sun nemi goyon bayan jama'a da sarakunan gargajiya domin sake zaben Tinubu da nasarar jam'iyyar a 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya gargadi masu kada kuri’a cewa nasarar Atiku Abubakar ko Peter Obi na iya kara talauci.

Ya ce shawarwarin ‘yan adawa na mayar da wasu sauye-sauyen Tinubu, musamman cire tallafin man fetur, za su rage kudaden ci gaban Arewa.

An gargadi yan Arewa kan zaben Atiku ko Peter Obi
Atiku Abubakar, Shugaba Bola Tinubu da Peter Obi. Hoto: Atiku Abubakar, Bayo Onanuga, Mr Peter Obi.
Source: Facebook

Shugaban APC ya bayyana hakan jiya a Abuja, yayin da yake jawabi ga ‘yan takarar majalisun jihohi da suka sauya sheka zuwa APC, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

2027: Rarara ya sake fitowa da maganganu masu zafi kan 'yan Arewa da Tinubu

Zargin da APC me yi wa yan adawa

Yilwatda ya zargi ‘yan adawa da amfani da kafafen yada labarai na yankin, musamman gidajen rediyon Hausa, wajen karkatar da fahimtar manufofin gwamnati.

‘Yan takarar sun sauya sheka ne daga African Democratic Congress, ADC, zuwa APC, daga jihohin Jigawa, Plateau, Taraba da Zamfara.

Yilwatda ya ce:

“Musamman ADC, ‘yan adawa suna yada labaran abubuwan da babu su."

Shugaban APC ya ce ayyukan hanyoyin gwamnatin tarayya da ake gudanarwa a yankin sun nuna kokarin gwamnati wajen bunkasa Arewacin Najeriya.

Ya ambaci hanyoyin Abuja zuwa Kano da Kano zuwa Maiduguri, da kuma Abuja-Lokoja-Benue, Akwanga-Jos da Kwara-Mokwa a matsayin misalai.

Sauran ayyukan da ya lissafa sun hada da hanyoyin Sokoto-Kebbi, Kano-Daura da Zaria-Danja, wadanda ya ce suna nuna ci gaban yankin.

APC ta gargadi yan Arewa game da zaɓen 2027
Shugaban jam'iyyar APC a Najeriya, Nentawe Yilwatda. Hoto: Prof. Nentawe Yilwatda.
Source: Twitter

Kalubalen APC ga yan adawa

Yilwatda ya tambayi yadda ‘yan adawa za su samar da kudin sake dawo da tallafin man fetur tare da ci gaba da ayyukan hanyoyin.

Kara karanta wannan

Shugaban APC ya dawo daga kasar waje, ya fadi abin da za su yi wa Nyesom Wike

Ya ce:

“Abin da suke ci gaba da fada a rediyo shi ne za su dawo da tallafin man fetur, amma ina tambayar yadda za su yi hakan?
“Shin za su dakatar da duk wadannan ayyukan hanyoyi ne saboda suna son dawo da tallafin man fetur?."

Ya kuma danganta karin rabon kudaden tarayya da inganta yanayin kudaden jihohin Arewa, yana tunawa da matsalolin biyan albashi da alawus.

Yilwatda ya ce kafin Tinubu ya hau mulki, jihohin Arewa na daga cikin jihohin da suka kasa biyan albashi da wasu hakkokin ma’aikata, cewar Punch.

Ya ce:

“Zan iya tabbatar muku cewa daga cikin kusan jihohi 30 da suka kasa biyan albashi a Najeriya, duk jihohin Arewa ba su iya ba.”

Ya ce hakan ya faru ne a shekarar 2023, lokacin da Shugaba Tinubu ya karbi ragamar mulkin Najeriya daga gwamnatin da ta gabata.

Yilwatda ya bukaci wadanda suka sauya sheka da sauran mambobin APC su kara kaimi wajen wayar da kan jama’a domin sake zaben Tinubu.

Kara karanta wannan

Babachir ya kawo shawarar da za ta ba Peter Obi da Kwankwaso nasara a zaben 2027

APC ta magantu kan rigima da Wike

A wani labarin, an ji cewa Nentawe Yilwatda ya waiwayi rikicin kungiyar PGF da Nyesom Wike bayan dawowarsa daga gajeren hutu.

Shugaban APC na kasa yana kasar waje aka samu sabani tsakanin gwamnonin APC da Ministan Abuja.

Farfesa Yilwatda bai ga abin rigima ba, ya ce salin-alin za a shawo kan duk wani sabani a jam’iyyarsu ba kamar yadda ake tunani ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.