Bayan Ganin Tinubu, Kwamitin Kamfen Adeleke Ya Magantu kan 'Shirin' Koma wa APC

Bayan Ganin Tinubu, Kwamitin Kamfen Adeleke Ya Magantu kan 'Shirin' Koma wa APC

  • Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Imole ta yi magana kan rahotannin cewa Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, na shirin koma wa APC
  • Ta ce ziyarar Adeleke ga Tinubu al’ada ce bayan zaɓen gwamna na musamman, kuma ba ta da alaƙa da shirin sauya jam’iyya
  • Majalisar ta tabbatar wa magoya bayan Adeleke cewa gwamnan zai ci gaba da mulkin Osun da kuma yi wa al’ummar jihar hidima

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Osogbo, Osun - Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Imole ta yi martani game da rahotannin da ke cewa Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, na shirin ficewa daga jam'iyyar Accord zuwa APC.

Rahotannin sun biyo bayan ziyarar da Adeleke ya kai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban ƙasa bayan nasarar da ya samu.

An musanta rahoton cewaAdeleke zai koma APC
Gwamna Ademola Adeleke da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Majalisar da ta jagoranci ayyukan yaƙin neman zaɓen Adeleke a zaɓen gwamnan Osun na ranar 15 ga Agusta, ta bayyana haka a shafinta na Facebook.

Kara karanta wannan

Minista ya fasa kwai, an ji yadda ake shirin ƙarawa Atiku 'hawan jini' kafin zaben 2027

Musabbabin ziyarar Adeleke ga Tinubu

Ta bayyana cewa ziyarar wani ɓangare ce ta al’adun siyasa da ake yi bayan kammala zaɓen gwamna da ake gudanarwa ba tare da haɗa shi da sauran zaɓuka ba.

A cikin sanarwa da Bamidele Salam, shugaban kwamitin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na majalisar, ya fitar ranar Juma’a, an ce ziyarar ba ta da alaƙa da sauya jam’iyya.

Majalisar ta ce ziyarar Gwamna Ademola Jackson Nurudeen Adeleke ga Shugaba Tinubu ta kasance cikin al’ada da tsarin siyasa bayan kammala irin waɗannan zaɓuka.

Ta ce Adeleke, bayan samun nasara a zaɓen gwamnan Osun da aka kammala, yana da nauyin nuna girmamawa da godiya ga ofishin shugaban ƙasa.

Adeleke ya gana da Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Ademola Adeleke na Osun. Hoto: Ademola Adeleke.
Source: Twitter

Kokarin Tinubu kafin zaben Osun

Majalisar ta kuma ce kafin zaɓen, Tinubu ya sha jaddada buƙatar INEC da hukumomin tsaro su tabbatar da gudanar da zaɓe cikin ’yanci da adalci.

Ta ce ziyarar ta kuma ba Tinubu da Adeleke damar tattauna batutuwan zaman lafiya, tsaro da ci gaban Osun bayan zaɓen da ya kasance mai zafi.

Kara karanta wannan

Abin da zaɓaɓben gwamnan Osun ya fadawa Tinubu gaba da gaba a fadar shugaban kasa

Wannan bayani ya biyo bayan hasashen da wasu suka yi cewa ziyarar Adeleke ga Tinubu na nufin yana tunanin barin Accord Party zuwa APC.

Sai dai Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Imole ta bayyana wannan hasashe a matsayin wanda ba shi da tushe, tana mai cewa batun sauya jam’iyya bai taso ba.

Majalisar ta ce:

“Domin kauce wa shakku, ziyarar Gwamna da manyan jami’an tawagarsa ba ta da alaƙa da shirin komawa APC kamar yadda ake hasashe.”

Davido ya fadi yadda Tinubu zai yi nasara

An ji cewa mawaki a Najeriya, David Adeleke ya ce zai iya yin caca da kuɗinsa kan sake zaɓen Bola Tinubu a 2027, saboda rarrabuwar kawunan ‘yan adawa.

Mawaƙin da aka fi sani da Davido ya ce kusan mutane takwas daga Kudu na son zama shugaban ƙasa, abin da ke hana ‘yan adawa haɗa kai.

Davido ya ce nasarar Adeleke a Osun ta nuna akwai dama, amma ya bayyana siyasar Najeriya a matsayin fage na mugunta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.