'Menene Laifinmu': Mazauna Sokoto Sun Zargi Gwamnati Ta Bar Su da 'Yan Bindiga
- ’Yan bindiga sun kashe mutane 32 tare da sojoji huɗu a hare-haren da suka kai yankunan Kebbe da Ungushi a jihar Sokoto da ke Arewacin Najeriya
- Sama da mutum 5,000 daga ƙauyukan Ungushi da kewaye sun tsere zuwa Jega a Jihar Kebbi domin neman mafaka tare da neman tsira
- Rundunar Sojoji da Gwamnatin Sakkwato sun ce sun ɗauki matakan ƙara matsa wa ’yan bindiga tare da taimaka wa waɗanda abin ya shafa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Sokoto – Matsalar tsaro na ƙara ta’azzara a Jihar Sakkwato, inda wasu wuraren da a baya ake ganin suna cikin kwanciyar hankali yanzu suke fuskantar hare-haren ’yan bindiga.
A makon da ya gabata, wasu ’yan bindiga sun shiga ƙaramar hukumar Kebbe, inda suka aikata ta’asar da ba a saba gani ba a yankin.

Source: Facebook
Kafar Channels da ta ruwaito harin ta ce mazauna yankun sun kuma fita daga yankunan domin neman mafaka a wasu wurare da ke makotaka da su.
Yadda aka kai hari Sokoto
Jaridar Aminiya da ta hira da wasu mazauna yankin ta ruwaito cewa lamarin da ya jawo Allah wadai daga mazauna garin tare da kira ga gwamnati ta ƙara ɗaukar matakan kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Al’ummar yankin sun zargi hukumomi da gazawa wajen dakile hare-haren, suna cewa ’yan bindigar sun samu damar kashe mutane, sace dabbobi da kona gidaje da kadarori ba tare da fuskantar isasshen martani ba.
Wani mazaunin Kebbe, Ashiru Muhammad Sani Kebbe, ya ce a lokacin da mazauna yankin sun fita gonaki, sai suka dawo da gudu bayan sun ga ’yan bindiga dauke da babura, inda kusan kowane babur ke ɗauke da mutum uku.
A cewarsa, sojojin da ke aikin samar da tsaro a yankin sun tunkari ’yan bindigar, lamarin da ya haifar da musayar wuta. amma daga cikin ’yan bindigar sun yi wa sojojin kawanya daga baya, inda suka kashe sojoji huɗu tare da tilasta wa sauran su ja da baya.
Mazauna Sokoto sun yi tir da gwamnati
Ashiru ya kuma zargi hukumomi da rashin ɗaukar matakan da suka dace, yana cewa jirgin sama ya yi shawagi a lokacin harin amma bai hana ’yan bindigar ci gaba da kai hare-haren ba

Source: Facebook
Ya yi kira ga gwamnati ta tuna da alkawarin da ta ɗauka na kare rayuka da dukiyoyin jama’a, yana cewa mutane sun talauce, an kashe su, sannan noma ya tsaya saboda rashin tsaro.
Ya ce mutanen Ungushi sun tsere zuwa ƙaramar hukumar Jega a Jihar Kebbi, inda suke samun mafaka a Makarantar Firamare ta Nizamiyya.
Alhaji Sa’idu Atta Ungushi, tsohon kansila a mazabar Ungushi, ya ce sun koma Jega ne saboda tana kusa da yankinsu domin neman agaji.
“Muna koke shin wane laifi ne muka yi wa gwamnati da za ta kyale mu ana kashe mu? Da idona na ga jirgi ya zo kuma ya gan su, amma babu abin da ya yi musu, ya wuce abin sa."
DSS ta gano shirin ta'addanci a Sokoto
A wani labarin, kun ji cewa hukumar DSS ta gargadi gwamnatin Sokoto kan shirin ’yan ta’adda da ’yan bindiga na kai hari cibiyoyin ilimi na gaba da sakandare a jihar.
Hukumar ta ce sabbin bayanan sirri sun nuna cewa masu laifin na sauya salon ayyukansu daga makarantun firamare da sakandare zuwa jami’o’i da wasu manyan makarantu.
Hukumar tsaro ta farin kaya ta DSS ta bukaci a gaggauta karfafa tsaro a cibiyoyin ilimi domin kare dalibai, malamai, ma’aikata da sauran muhimman ababen more rayuwa.
Asali: Legit.ng


